011
A yau ne kuma aka karb'i kudin auren falmata da auwal inda iyaye suka tsayar da watanni biyu masu zuwa kasancewar auwal ya gama komai a gidan sa, sai fenti wanda sai an kusa bikin zaiyi.
Dik wannan dramern da akeyi falmata batasan anayi ba, domin ita tinda ta karb'i wannan wayar ta shige d'aki bata fitowa.
Baba ne ya shigo ya d'ankawa umma kud'in.
"Ki ajiyesu kafin naje na dawo anjima sai a san yadda za'ai da su.
Karba tayi ta huce da su zuwa d'akinta.
Falmata na kwance a akan katifarta ta kunna littafin RAYUWAR WASU audio tana saurara, ni ko nace ko ina ta samo sa.
Haka wunin ranar ya kasance, falmata bata fito ba sai can goshin magariba, tayi alwala tazo tmzata shige.
Sadeeq be ya k'arasi ya rike ta yace"haba aunty falmata yanzu dama akan wani bare zaki iya fishi da iyayenmu, karki manta fa su suka shayar dake, suka tufatar da ke, har kika kai wannan matsayin amma akan wani d'an iska zaki iya kwana da kwanaki baki musu magana ba.
D'aga hannu tayi ta wanka masa mari ta juyo ta kallesa yayin da shi kuma ya rik'e kuncinsa.
"Sadeeq yaushe nayi lalacewar da zaka na mini wannan titsiyen, dik iskancinka da rashin mutuncinka ya tsaya a kaina, karka kuskura ta ka tab'a khalil, domin khalil jininsa ne ke gudana a jikina, kuma ko da wasa na k'ara jin ka zagesa sai na ci maka mutunci, shashasha kawai.
Hucewarta tayi fuuu ta barsa a tsaye rike da kunci yana share hawayen da ya zubo masa.
Dik wannan abin da akeyi a gaban umma, sadeeq na kallon ta tana share hawaye hakan yayi masa ciwo sosai.
Sadeeq da usman ne a d'akin, yayin da sadeeq ya kalli usman yace"Ban tab'a tunanin aunty falmata bata da hankali ba sai yau.
" a gaban mama ta mareni saboda nacewa wani katon banza dan iska.
" Ai kaine kaima da shegen shishigi ba sai ka kyaleta ba, duniya ce yadda ta b'ata ran kowa a gidan nan ita ma akwai lokaci da za'a b'ata ranta, ka kyaleta kawai ina gaya maka, akwai ranar k'in dillanci.
Daga haka usman bai sake magana ba, shima sadeeq ya bar zancen anan.
Umma ce ta linke kud'in da baba ya bata ta adana su da niyyar gibe zataje kasuwa, dama dayake tana siyan kayan kitchen tana ajiyewa,yanzu siyayyar ta zama saura kad'an.
Falmata dik wannan abun babu abinda ta sani, ita dai gata nan kawai, khalil kullin na kiranta domin k'ara debe mata kewa, ko nace ya k'ara zugata.
Washe gari ummi ce ta shigo gidan nasu da sallamarta.
Umma ta gani tana gyara masara, har k'asa ta gaisheta tana murmushi.
"ummi jiki yayi sauki kenan.
" Eh umma da sauki ta fad'a tana murmushi.Ina falmata kuwa umma.
"Tana d'akinta umma ta bata amsa.
Hucewa tayi ta tsaya bakin kofar tata tana knocking falmata na kwance taji ana bugawa, ko kallon kofar batayi ba, can kuma taji muryar ummi tana magana.
Tsaki taja a fili ta furta sai kiyi tayi ai munafuka kawai.
Ummi gajiya tayi da bugun kofar hmta juya ta koma tsakar gidan, anan ta zauna ta taya umma aikace aikace dik da tace ta barshi, amma sam taki bari.
Kwance yake da wayarsa a hannu, gefe kuma amira ce tana masa tausa, nace to kai kam ka cika ka tumbatsa.
Hayaniyar da suka jiyo daga waje ne yasa kallon amira yace"maza ki b'uya yanzun nan.
Tashi yayi ya bude kofar, mahaifinsa ne tsaye a bakin kofar sa, yayin da mutane ke hayaniya.
"Wallahi ba wanda ya isa ya budewa d'ana kofarsa, da zakuje yana kawo mata kuna da sheda ne, idan kuna da sheda sai ku fad'a, ba rana d'aya kawai ku tashi kuce yana kawo mata ba, mahaifin ya fad'a yana tada jijiyoyin wuya.
" wace sheda kuma alhaji, sanin kanka ne yana kawowa, tinda naga ai kofar gidanka ne nan d'in, kuma dik wainar da ake toyawa ka sani.
" Ka dallah malam rufe mana a gidan uwarwa nake kawo mata shagona, indai kaga wani ai abokina ne ba mata ba, idan kuma kuna ganin karya ne baba zo ka duba, khalil ya fad'a yana kallon mutanen.
Alhajin ne ya shiga bai ga kowa ba hakan ya saka shi juyowa yace musu ai gashi nan na fad'a muku d'ana bashi da wannan halayyar kunki yadda, sai na ga yadda za'ayi ai, gashi nan ba kowa, haka alhajin ya koresu ba dan sun so ba suka tafi.
Kallon khalil yayi yace"ka kiyaye fa mutane akwai sa ido, murmushi khaliil yayi ya juya ya koma.
Ameera wadda ke tsaye tace"wai khalil meyasa mutane akwai su da sa ido, aikin banza kawai, haka ta tattara ita ta huce ta barsa shi kadai.