INUWAR GASKIYA

Page 3

by @marhama2002

INUWAR GASKIYA


Na Marhama

Washegari da sassafe, Afnaan ta farka tun kafin a kira sallar asuba.

Ta zauna a gefen gadonta, ta zaro ƙaramin hoton da take ɓoyewa a cikin jakarta. Ta daɗe tana kallonsa ba tare da ta ce komai ba.

Hawayen da suka taru a idanunta sun fara zuba.

“Ki yi haƙuri…” ta furta cikin raɗaɗi.

Ta share hawayenta da bayan hannunta, ta mayar da hoton cikin jakarta, sannan ta tashi ta shirya.

A yau ne za ta fara aikin da ya kawo ta wannan gida.

Ba ta san abin da ke jiranta ba, amma ta san abu ɗaya: ba za ta bari abin da ya faru a baya ya hana ta cimma manufarta ba.


“Afnaan!”

Muryar Hajiya Rabi ta katse tunaninta.

“Ga ni, Hajiya.”

“Zo nan. Zan nuna miki aikin da za ki riƙa yi kullum. Ba na son a maimaita abu sau biyu. Idan na nuna miki abu, ki fahimta.”

“Na'am, Hajiya.”

Hajiya Rabi ta zagaya da ita cikin gidan, tana nuna mata inda za ta riƙa sharewa, inda za ta goge, da kuma wuraren da ba ta da izinin shiga.

“Wannan ɓangaren na sama, ke ba ki da hurumin zuwa can sai an kira ki.”

Ta nuna wani corridor mai nisa.

“Wannan kuma ɗakin Mai Gidan ne. Ba wanda yake shiga cikinsa sai da izininsa. Ki guji kusantarsa idan ba a kira ki ba.”

Afnaan ta gyada kai.

“Na gane.”

Suka ci gaba da tafiya har suka isa wani wuri da ƙofa mai launin baƙi ta mamaye. Ƙofar tana da makullai biyu, kuma babu wani abu a kanta sai ƙaramin abin riƙewa na ƙarfe.

Afnaan ta tsaya na ɗan lokaci tana kallonta.

Hajiya Rabi ta lura.

“Me kika tsaya kina kallo?”

Afnaan ta janye idanunta da sauri.

“Babu komai, Hajiya.”

“Wannan ƙofar ba ta shafe ki ba. Kada ki kusance ta, kada ki taɓa ta, kuma kada ki yi ƙoƙarin sanin abin da ke cikinta.”

Ta yi magana cikin tsauri, sannan ta ƙara da cewa:

“Ko da kin ji wani abu a bayanta, ba ki ji komai ba. Kin gane?”

Afnaan ta haɗiye yawu.

“Na gane, Hajiya.”

“Madalla. Ki tuna da abin da na gaya miki.”

Hajiya Rabi ta wuce, Afnaan kuma ta bi ta.

Amma a cikin zuciyarta, ta riga ta san cewa ƙofar nan ba ƙofa ce ta yau da kullum ba.

Akwai wani abu a bayanta.

Wani abu da kowa yake tsoron magana a kansa.


Da misalin ƙarfe goma na safe, Afnaan tana goge wani babban falo lokacin da motar Abdulmalik ta shigo harabar gidan.

Ma'aikatan da ke wajen suka fara motsi da sauri. Wata ta gyara labulen taga, wani ya ɗauki wasu takardu, yayin da Hajiya Rabi ta fito daga kitchen tana share hannunta.

Afnaan ta kalli yadda kowa ya canza a cikin 'yan daƙiƙu.

Ashe zuwansa kaɗai yake sa mutane su shiga wannan yanayin? ta yi tunani.

Ƙofar gidan ta buɗe.

Abdulmalik ya shigo tare da Bashir, hannunsa riƙe da wayarsa. Yana magana cikin murya mai sanyi, amma duk wanda ya ji maganarsa zai gane cewa ba ya son a saɓa masa.

“Na gaya maka ba na son kuskure. Idan wannan al'amari ya sake tasowa, kai ne za ka ɗauki alhakin abin da zai biyo baya.”

Ya katse wayar.

A daidai lokacin ne ya hango Afnaan tana goge falon.

Ta sunkuyar da kanta cikin ladabi.

“Barka da zuwa, ranka ya daɗe.”

Bai amsa ba.

Ya wuce ta, amma bayan ya yi wasu 'yan matakai sai ya tsaya.

“Ke.”

Afnaan ta ɗago kai.

“Na'am, ranka ya daɗe?”

“Wacece ta ba ki izinin yin aiki a wannan ɓangaren?”

“Hajiya Rabi ce, ranka ya daɗe.”

Ya juya ya kalli Hajiya Rabi wadda ke tsaye nesa kaɗan.

“Na gaya miki ina son a kiyaye dokokin gidan nan.”

Hajiya Rabi ta sunkuyar da kanta.

“Yi haƙuri, ranka ya daɗe. Ni na ce ta yi aikin.”

Abdulmalik ya sake kallon Afnaan.

“Ki ci gaba da aikinki. Amma ki koyi abu ɗaya: a wannan gidan, babu wanda yake yin abin da ya ga dama.”

“Na'am, ranka ya daɗe.”

Ya wuce zuwa bene na sama.

Afnaan ta ci gaba da goge falon, amma tunaninta ya tsaya kan yadda ya kalle ta.

Ba kamar mutumin da yake magana da ma'aikaciyarsa kawai ba.

Kamar yana ƙoƙarin gano wani abu ne a kanta.


Da yamma, yayin da ma'aikatan suke shirin kammala ayyukansu, Afnaan ta dawo ɗakinta.

Ta zauna a gefen gado, ta fito da hoton daga jakarta. Ta kalle shi na ɗan lokaci kafin ta matsa shi a kirjinta.

A wajen ɗakinta, ana jin hayaniyar ma'aikatan da suke tattara kayan aiki.

Sai kwatsam, aka ji wani ƙara daga ɓangaren ƙofar baƙin.

Dum!

Afnaan ta zabura.

Ta ɗago kai, tana sauraro.

Sai aka ji wani sauti kamar ana jan wani abu a ƙasa.

Daga nan komai ya yi shiru.

Ta miƙe a hankali ta buɗe ƙofar ɗakinta kaɗan.

Corridor ɗin babu kowa.

Ta kalli ɓangaren da ƙofar baƙin take, zuciyarta tana bugawa da sauri.

Ta tuna gargaɗin Hajiya Rabi.

Ko da kin ji wani abu a bayanta, ba ki ji komai ba.

Ta fara mayar da ƙofar ɗakinta, amma kafin ta rufe, ta ga wani mutum yana tsaye a ƙarshen corridor.

Bashir ne.

Yana kallonta.

Ba ta san tsawon lokacin da ya yi a wurin ba, ko abin da ya ji.

Sai ya fara takowa zuwa gare ta.

“Me kike yi a nan?”

Afnaan ta yi saurin amsawa.

“Zan shiga ɗakina ne.”

Bashir ya kalli ƙofar ɗakin, sannan ya mayar da idanunsa gare ta.

“Kin ji wani abu?”

Ta ji jikinta ya yi sanyi.

“Wane abu?”

Ya zuba mata ido na wasu daƙiƙu.

Sai ya yi murmushi marar daɗi.

“Babu komai. Ki shiga ɗakinki.”

Afnaan ta shiga ta rufe ƙofar.

Ta jingina da ita, tana ƙoƙarin daidaita numfashinta.

Amma abin da ya fi tayar mata da hankali ba ƙarar da ta ji ba ce.

Abin da ya fi tayar mata da hankali shi ne yadda Bashir ya tambaye ta ko ta ji wani abu.

Kamar dai ya san cewa akwai wani abu da bai kamata ta ji ba.

Kuma a wannan daren, Afnaan ta fara fahimtar cewa sirrin wannan gida ya fi ƙarfin abin da ta yi zato.