ZAYD ARMAAN

THE UNSEEN WOUNDS!

by @jiddaahbarkum

ZAYD ARMAAN

CHAPTER 114

THE UNSEEN WOUNDS

JIDDAAH BARKUM

————

A gidan Malam Musa kuwa, lokacin da Maryam da Bintu suka dawo, Baffa da matan gidan suna zaune a tsakar gida, Baffa ya bi su da kallo tun daga lokacin da ya hango su suna shigowa, ɗauke da ledoji maƙil da kaya, a hankali suka ƙaraso gabansa, suka risina suka gaishe shi, Baffa ya amsa musu, amma idanunsa na kan ledojin da suke riƙe da su, “Wnn ledoji fa? Daga ina ku ka samo waɗannan kayan?” Maryam ta ɗan sosa kanta, tana neman abin da za ta ce, “Umm… Baffa, dama Raihana ce ta ba mu,” ya kure ta da ido, yana kallonta cikin mamaki, “Me ta ba ku? Ba dai kayan mijinta ba ne?” Da sauri Maryam ta girgiza kai, “A’a, Baffa,” Bintu ta yi caraf, kamar wadda ta daɗe tana jiran a ba ta damar yin magana, “Baffa, a cikin kayan lefen ta ne fa! Ita ce ta ce mu zaɓi abin da muke so,” Baffa ya yi shiru, yana kallon yawan kayan da ke hannun Bintu, ya sake kallon Maryam, sannan ya mayar da idanunsa kan ledojin, “Duk waɗannan kayan kuka ɗebo mata? Saboda rashin hankali?” Maryam dai ba ta ce komai ba, ta sunkuyar da kanta, tana jin nauyin kallon Baffanta, Bintu kuwa ta sake yin magana, kamar ba ta fahimci abin da Baffa yake nufi ba, “Baffa, wallahi kayan da yawa fa ɗaki guda ne fa, kuma suna da yawa sosai, itace ma ta ce mu ɗauki duk abin da muke so,” Baffa ya ja dogon numfashi, ya girgiza kansa a hankali, “Bintu, ke kina ganin wannan abin da kuka yi yayı dai dai kenan? Saboda ta ce ku ɗauki abin da kuke so, sai ku tattara kaya kamar za ku kwashe mata gaba ɗaya?” Bintu ta ɗan turo baki, “Baffa, Ita da kanta ta ba mu,” “Na ji,” ya amsa a taƙaice, “Amma akwai abin da ake yi saboda mutum ya ba ka dama, akwai kuma abin da ya kamata ka san iyakarsa, Raihana ’yar gidan nan ce, kuma duk abin da ta mallaka, tana da ’yancin yin abin da ta ga dama da shi, amma hakan ba yana nufin ku za ku ɗauki komai ba tare da kun yi tunani ba,” ya sake kallon ledojin, “Ku faɗa min, duk waɗannan kayan da kuka ɗauka, ita ce ta zaɓa muku ɗaya bayan ɗaya, ko kuwa ku kuka je kuna ɗiba?” Bintu ta yi shiru na ɗan lokaci, kafin ta amsa, “Mu muka zaɓa, Baffa, amma ita ce ta ce mu ɗauki abin da muke so,” Baffa ya gyada kai a hankali, sannan ya kalli Maryam, “Ke kuma, Maryam, me ya sa ba ki ce komai ba?” Maryam ta ɗago kai a hankali, “Baffa, da ba zan dauka ba ni dai, amma da ta dage, sai na ga babu abin da zan ce mata, ban so ta ji kamar ba mu karɓi abin da ta ba mu ba ne,” Baffa ya yi shiru, yana nazarin kalamanta, daga nan sai ya sauke ajiyar zuciya, “Allah Ya kyauta, ni dai abin da nake so shi ne kada wannan kyautar ta zama sanadin wata matsala, Raihana tana gidan aure yanzu, kuma ina son ta riƙe mutuncinta da mutuncin gidanmu, ba na so a samu wani abu da zai sa a fara yi mata magana saboda kayan da ta ba ’yan uwanta,” Bintu ta sunkuyar da kanta, wannan karon ba ta sake cewa komai ba, Maryam kuwa ta kalli kayan da ke hannunsu, tana tunanin yadda Raihana ta ba su damar zaɓar duk abin da suke so cikin farin ciki, ta san halin yar uwarta, idan ta ba mutum abu daga zuciyarta, ba ta son a hana ta, amma a yanzu ta fara fahimtar abin da Baffa yake tsoro, ba wai ya hana su karɓar kyautar Raihana ba ne, yana tsoron kada wata rana a yi amfani da wannan kyautar wajen ɓata wa ’yarsa rai, Baffa ya sake kallonsu sai ya sauke ajiyar zuciya, “Ku wuce ciki,” “Toh, Baffa,” Maryam ta amsa a hankali, Bintu ma ta gyada kai, sannan suka juya suka nufi cikin gida da ledojin nasu, Baffa ya bi su da kallo har suka shige, kafin ya mayar da kansa ga matanshi da suke zaune a tsakar gidan, amma duk da haka, tunaninsa bai bar batun Raihana ba.

Bayan Maryam da Bintu sun tafi cikin gidan da ledojin nasu, Mama Sabuwa ta tabe baki, ta gyara zamanta a kan tabarmar da suke kai, “Toh wai, Malam, meye a ciki?” ta faɗa, tana kallon Baffa, “Idan ’yar uwarsu ta ba su abu, ai ba wani laifi suka yi ba, idan ɗan uwanka bai maka abu ba, waye zai maka? Kai dai ka duba ka gani!” Ta yi wata ’yar dariya ta gefe, sannan ta ɗan karkata kai, “Wallahi, yanzu idan Raihana ta sake ba su wani abu, sai su yi daarrrr wajen karɓa! Sabida wnn abun da kayi, ai dama idan Allah Ya ba mutum gidan hutu, ba wai shi kaɗai zai zauna yana morewa ba, na kusa dashi ma ya mora mana! Ko ba haka ba?” Ta sake kallon Baffa, tana jiran ya goyi bayanta, “Ka ga ni dai, ban ga laifinsu ba sam, ai ba sata suka yi ba, kuma ba su je sun ƙwace mata kayan da ƙarfi ba, ita da kanta ta ce su zaɓi abin da suke so, to, idan mutum ya ba ka dama, me zai sa ka ƙi amfani da ita?” Baffa ya ɗaga idanunsa ya kalleta kawai, sannan ya girgiza kai a hankali ba tare da ya ce uffan ba, Mama Sabuwa ta lura da shirunsa, amma maimakon ta tsaya, sai ta ƙara da cewa, “Ni fa abin da na sani, idan mutum yana da hali, ya kamata ya taimaki danginsa, yanzu Raihana tana gidan arziki, Masha Allah, me zai hana ’yan uwanta su amfana da abin da Allah Ya ba ta? Ko sai ta tara komai a ɗakinta tana kallonsa?” Umma dai ba ta ce komai ba, ta zauna ne kawai tana sauraron maganganun Mama Sabuwa, fuskarta babu alamar cewa tana son shiga cikin maganar, Mama Indo kuwa, da ke zaune a gefe, ta juya ta watsawa Mama Sabuwa wata uwar harara, “Hm!” ta yi wani irin ƙwafa, tana girgiza kai, “Ke kam, Sabuwa, kinada ƙarfin hali” Mama Sabuwa ta juyo da sauri, “Ni kuma? Me na faɗa kuma?” Mama Indo ta yi mata wani kallo na sama da ƙasa, “Ke dai idan aka zo maganar abin da za a samu, sai ki zama kamar ba a taɓa ba ki wani abun arziki ba a rayuwarki ba, kin san abin da malam ke nufi amma saboda kin ji an ambaci kaya, sai kika manta da komai,” “Wai ni ne na manta da komai?” Mama Sabuwa ta tambaya, tana ɗaga murya kaɗan, “To, ku faɗa min abin da na faɗa ba gaskiya ba ne! Raihana ta ba su kayan ne ko ba ta ba su ba?” Mama Indo ta sake yin ƙwafa, ta kawar da kai, “Allah Ya kyauta!” Mama Sabuwa ta tabe baki, ta koma gyara waken gabanta tana ta faman mita a ƙasa-ƙasa, “Mutum ya faɗi gaskiya, sai a ce ya na da son abun duniya, yo yan uwanta tayi wa ba wani ba ko ta dauro wani abu tace gashi a kai wa sabuwa ne? Ai ni dai na san abin da nake faɗa tunda da hankalina,” Baffa kuwa bai ce komai ba, ya ci gaba da zama cikin shirunsa, yana kallon su lokaci-lokaci, kafin ya sauke ajiyar zuciya, ba wai bai ji maganganun Mama Sabuwa ba ne, amma ya san irin halinta, idan ta ga abin da za a amfana da shi, ba ta cika duba abin da zai biyo baya ba, shi kuma, abin da yake tsoro ba kyautar Raihana ba ce, abin da yake tsoro shi ne kada wata rana alherin da ’yarsa take yi wa danginta ya zama abin da za a yi amfani da shi wajen cutar da ita, a can kuwa, wajen ƙarfe sha biyu da rabi na rana, sai ga Hajiya Hauwa tare da Rabi da wata budurwa yarinya wadda shekarunta ba za su wuce sha shida ba, ba tare da ɓata lokaci ba, Hajiya Hauwa ta nufi ɓangaren Seeyama kai tsaye, tana shiga, ta dire mata Rabi, sannan ta juyo ta kalli Seeyama da wani irin kallo mai nuna tsanani, “Seeyama, ina so ki saurare ni da kyau, wallahi, duk abin da kika yi wa Rabi har ya sa ranta ya ɓaci, to, sai kin ga wani gefen halina da ba ki taɓa sani ba, na kawo miki ita ne domin ta taimaka miki da ayyukan gida, ba wai domin ki mayar da ita baiwarki ba, kin ji ni?” Ta ɗan dakata, tana kallon ’yarta sosai, “Ki kiyaye harshenki da yadda kike mu’amala da ita, ba zan yarda ki wulaƙanta ta ba saboda kawai tana aiki a gidanki ba, yanzu amintacciya ta ce nasan kinsan hakaa, ina fatan na isar da saƙona,” Seeyama dai ba ta ce komai ba, ta tsaya ne kawai tana kallon mahaifiyarta, amma cikin ranta bala’in jin haushin mommy take, ta zabga wa Rabi wata shegiyar harara, kamar ita ce ta jawo mata duk matsalar, Hajiya Hauwa ta sake kallonta a taƙaice, sannan ta juya ta fita, da zarar ta fita, Seeyama ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, tana girgiza kai, “Mtchewww!” Ta ja tsaki, Hajiya hauwa na fita ta mayar da kallonta ga yarinyar da ta kawo wa Raihana Sadiya wacce ke tsaye a wajen part din seeyama dan ko shigowa ma bata yi ba muje kawai tace yarinyar kuwa ta bi bayanta, Mommy na fita, Seeyama ta juyo ta kalli Rabi daga sama har ƙasa, ta ƙura mata ido, kai kace yau ta fara saninta ta yi wani murmushin gefen baki marar daɗi, “Wato, ɗan uwarki, sai da kika biyo Mommy ta kawo ki nan, ko?” Rabi ta tsaya cak, ba ta san abin da za ta ce ba, Seeyama ta matso kusa da ita, tana nuna ta da yatsa, “To, wallahi, kurkuku ma sai ya fi miki gidan nan daɗin zama! Tunda ke kin zama kamar jaka wajen aiki, ai za ki ga kuwa uban aikin da za ki yi,” ta ɗaga gira, sannan ta ci gaba da magana cikin fushi, “Daga yau, ayyukanki a gidan nan har da wanke min bango! Na rantse da Allah, ƙarfe huɗun asuba ta wuce baki tashi kin fara kintsa min gida ba, za ki ga abin da zan tashe ki da shi!” Ta haɗe hannayenta a ƙirji, tana kallon Rabi da wani irin kallo na raini, “Sannan duk lokacin da mijina yake gidan nan, kika kuskura ki fito ko ki yi wani yawo a gabansa, wallahi sai na zuba miki acid a wnn shegiyar kodaddiyar farar fuskar taki!” Rabi ta haɗiye yawu, tana kallon Seeyama cikin tsoro, Seeyama kuwa kamar ba ta gama faɗin abin da ke ranta ba, sai ta ƙara da cewa, ta matsa kusa da Rabi, ta runtse idanuwanta kaɗan, “Kuma kada ki dinga wani abu kamar kin san ni, ki ɗauka baki taɓa sanina ba, yau ne ki ka fara ganina a rayuwarki!” Ta juya ta kalli kayan da Rabi ta zo da su, sannan ta nuna mata hanyar store, “Yanzu ki tashi ki matsar da kayan nan cikin store, ki ɗauki ɗaya daga cikin zaninki ki shimfiɗa a ciki, ki dinga kwana a kai, na rantse, ba za ki zauna min a ɗaya daga cikin ɗakuna na ba, tunda ba ni na gayyato ki ba!” Ta ƙarasa maganar tana nuna kanta da yatsa, “Ni fa ba irin wacce kike zato ba ce, kuma idan kina son zaman lafiya a gidan nan, ki koyi yadda za ki zauna da ni, kin gane?” Rabi ta sunkuyar da kanta, ta matse hannayenta wuri guda, “To, Anty,” ta amsa a hankali, “Me kika ce?” “Na gane, Antyyy,” “Good!” Seeyama ta juya, ta zauna a kan kujera, tana ɗaukar wayarta kamar ba itace ta gama yi wa yarinyar barazana ba, Rabi tana tsaye tana ƙoƙarin tattara kayanta domin ta kai su store, sai ga Zayd ya fito daga ɗakinsa bayan ya yi wanka zaije masjid, sanye yake da wani simple home outfit na blue-black, wanda aka ɗinka da yadi mai kyau, rigarsa mai gajeren hannu ce, tsawonta ya kai daidai cinyoyinsa, ta zauna a jikinsa cikin sauƙi, fuskarsa kuwa a haɗe take, babu alamar murmushi ko walwala, amma duk da irin yanayin da yake ciki, ciwon da ya sha a daren da ya gabata kamar ma ya ƙara fito da wani irin kyau na daban a tare da shi, ya yi fresh tasss, fatarsa tana sheƙi kamar a wanke hannu a taɓa, ga wani azababben ƙamshi mai daɗi da ke tashi daga jikinsa, wanda ya gauraya da iska yake bada wani atmosphere mai dadi, tafe ya ke yana gyara agogon da ke hannunsa, sannan ya nufi hanyar fita daga ɓangaren ba tare da ya kalli inda suke ba, kusan rabin maganganun Seeyama da take yi wa Rabi tsaff ya ji su, amma bai nuna cewa ya ji komai ba, fuskarsa dai a haɗe take, yana tafiya cikin nutsuwarsa kamar babu wani mahalukie wanda yake wurin, Seeyama kuwa, tana zaune a kan kujera, ta bishi da kallo tun daga lokacin da ya fito, duk da irin bala’in da ya faru a daren jiya, duk da tsoron da ya kamata ta ji idan ta tuna abin da ta aikata, hakan bai hana zuciyarta motsawa da zarar ta ga Zayd ba, da zarar idanunta suka sauka a kansa, sai ta ji wani irin abu ya ratsa jikinta, Ya Allah! Wannan mutumin fa… Kallonshi kawai take, kamar tsohuwar mayya da ta manta da komai a duniya, zuciyarta ta fara bugawa da sauri, tana jin kamar ruwa na bin ƙafafunta, ta tuna da irin kusancin da suka yi a daren jiya sai ta haɗiye yawu, ganin shi a gabanta ya sa ta manta da duk wani tunanin da take yi, tana son ta kira shi, ta gaishe shi, ta tambaye shi ko jikinsa ya ji sauƙi, amma a lokaci guda, tana tsoron ya yarfa ta ga maid dinta a wajen kuma Seeyama ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, yanzu ita kanta ta san cewa idan ta kira Zayd, akwai yiwuwar ma ya ƙi amsawa, tun da ya dawo daga asibiti bai ba ta ko kallon kirki ba, balle ya nuna mata wata alamar cewa ya manta da abin da ya faru, sai dai duk da haka, zuciyarta ta kasa barin kallonsa, Seeyama ta bi shi da idanu har ya kusa ɓacewa daga ganinta, tana son ta buɗe baki ta kira shi, amma ta kasa, ta ji kamar wani abu ya toshe mata makogwaro, a ƙarshe, sai ta haƙura, ta kasa kunne tana sauraron takun sawunsa har sai da sautin ya fara nisa, sannan ya ɓace gaba ɗaya, sai a lokacin ta sauke ajiyar zuciya, tana jin wani irin baƙin ciki da takaici a ranta, ba zato ba tsammani, ta tuna da Rabi da take tsaye a gabanta, Seeyama ta ɗago kai da sauri, ta mayar da kallonta kanta, “Ke!” Rabi ta firgita, ta ɗago kai, “Na’am,?” Seeyama ta zuba mata uwar harara, “Uban me kike jira ne? Ko ba zan tashi ba ne? Na ce ki ɗauki kayan ki kai store, ko sai na maimaita miki?” Rabi ta yi saurin sunkuyar da kai, “Yi haƙuri, anty, zan je yanzu,” Rabi ta yi saurin ɗaukar kayanta, ta nufi store ɗin, yayin da Seeyama ta koma jingina da kujerarta, amma ko bayan Rabi ta tafi, tunaninta bai bar Zayd ba, fuskarsa, ƙamshinsa, da yadda ya wuce ta ba tare da ya kalleta ba duk sun tsaya mata a rai ga kuma yanda jikinta ke reacting da zarar ya fado mata a rai, tun lokacin da suka dawo daga asibiti, Raihana ba ta tashi daga falon da take ba, tana kwance ne a kan kujera, jikinta a sanyaye, ko tunanin breakfast bai faɗo mata ba, kwance kawai take a nan, sanye da hijabin da ta saka tun lokacin da suka fita asibiti, ba ta cire shi ba, ba ta canza kaya ba, kuma ba ta ma san adadin sa’o’in da ta ɗauka a wajen ba, idonta biyu amma tunaninta yana wani wuri daban, Zayd, abin da ya fi damunta shi ne yadda ya ƙi ko kallon fuskarta, da ace ya yi mata magana, ko ya yi mata faɗa, da wataƙila da ta ji sauƙi, amma wannan shirun nasa ya fi komai ciwo a gare ta, ta sake juyawa a hankali a kan kujerar, tana kallon ƙofar falon da idanunta suka kasa barin ta, ba ta san abin da take jira ba, ko dai tana fatan zai dawo? Ko kuma tana son ta sake ganin fuskarsa ne kawai? Ita kanta ba ta san amsar ba, sai kawai ta ji karar buɗe ƙofa, da sauri ta ɗago kanta, zuciyarta ta yi wani irin tsalle, tun daga lokacin da suka dawo daga asibiti, duk wani motsi da ta ji a gidan yana sa ta yi tunanin ko Zayd ne, amma da idanunta suka sauka kan waɗanda suka shigo, sai ta yi turus, Hajiya Hauwa ce tare da wata yarinya, a hankali Raihana ta gyara zamanta, ta jingina da kujerar tana ƙoƙarin kakalo murmushi duk da yanayin da take ciki, Hajiya Hauwa kuwa ta washe baki, ta ƙaraso kusa da kujerar da Raihana take zaune, ta tsaya na ɗan lokaci tana kallonta daga sama har ƙasa, kamar tana nazarin wata sabuwar halitta da ba ta taɓa gani ba, kafin ta zauna a hankali, Raihana ta sauke idanunta ƙasa, “Ina kwana,” Hajiya Hauwa ta ɗan shafa kanta, fuskarta cike da murmushi, “Ina yini dai, daughter, this is 12:45, ana kiran sallar Zuhr yanzu, ko kuma yanzu kika tashi daga bacci ne?” Raihana ta ɗan yi murmushi na jin kunya, ta sake sunkuyar da kanta, “Eh,” yarinyar da Hajiya Hauwa ta zo da ita ta ƙaraso kaɗan, sannan ta gaishe da Raihana cikin ladabi, “Ina yini, Hajiya?” Raihana ta ɗago kai kaɗan, “Lafiya lau, ya gida?” “Lafiya lau,” yarinyar ta amsa, bayan haka, Raihana ta sake mayar da kanta ƙasa, tana wasa da gefen hijab ɗinta, Hajiya Hauwa kuwa ta sauke ajiyar zuciya, har yanzu tana kallonta kamar zata cinyeta, “Raihana?” A hankali ta ɗago kanta, “Na’am, ?” Ta amsa a hankali, Hajiya Hauwa ta ɗage gira, “Baki da lafiya ne? You look dull,” da sauri Raihana ta girgiza kai, “A’a, lafiyata kalau, daga bacci na tashi ne kawai,” ta faɗi hakan cikin sanyin murya, tana ƙoƙarin ganin murmushin da zai sa Hajiya Hauwa ta daina tambayarta, amma Hajiya Hauwa ba ta gamsu ba, ta sake haɗe rai, tana ci gaba da kallonta, “Wato dai baki karya ba? Irin na ranar nan kuma? Raihana, na faɗa miki ki daina zama da yunwa haka, me ya sa kike son wahalar da kanki ne? Kina ganin wannan jikin naki lukui lukui kamar madara zai iya ɗaukar wahalar komai ne?” Raihana ta yi shiru, gaskiya ce, ba ta karya ba, kuma tun lokacin da ta dawo daga asibiti ba ta ci komai ba, amma ko yunwar ba ta fi abin da ke damunta a zuciya ba, ta kasa samun abin da za ta ce, don haka ta ci gaba da kallon ƙasa, Hajiya Hauwa ta ɗan girgiza kai, “It’s okay,” sai ta miƙe tsaye, “Bari na samo miki abin da za ki ci, dan, daga yanayinki na ga kamar ba kya jin daɗi, ba zan bar ki haka ba,” da sauri Raihana ita ma ta miƙe, “A’a, Mommy, zan yi yanzu, please, ki zauna kawai,” Hajiya Hauwa ta tsaya cak, ta juyo a hankali, ta kalli Raihana da wani irin kallo kurilla, zaka rantse wnn ne encounter dinsu na farko, Raihana kuwa ta kasa jure kallon, ta sauke idanunta ƙasa, tana murza yatsunta cikin damuwa, “Mommy, I can do it,” ta ƙara faɗa cikin sanyin murya, Hajiya Hauwa ta ɗaga gira, “Really?” Raihana ba ta ce komai ba, Hajiya hauwa kawai ta kura mata ido ta kasa daina kallonta Raihana na jin idanuwanta a kanta ta rasa abinda ke mata dadi a duniya, a dai-dai lokacin ne Zayd, wanda ya ga wasu mutane sun shige zuwa ɓangaren Raihana, ya fasa fita zuwa masallaci, ya juya ya nufi ɓangaren nata, yana tafiya cikin nutsuwa, da ya isa ƙofar falon, sai ya tarar ba a rufe ƙofar sosai ba, don haka ya tura ta a hankali, bai yi wata ƙara ba da zai janyo attention din su, amma da ya shigo, idanunsa suka sauka kan Raihana a tsaye, yayin da Hajiya Hauwa take riƙe da kafaɗunta tana kallonta kai tsaye cikin idanu, Zayd ya tsaya cak, idanunsa suka tsaya a kansu, musamman a kan Raihana wadda ta yi shiru, kanta a ɗan sunkuye, yayin da Hajiya Hauwa take tsaye a gabanta cikin yanayin mai cike da kulawa a hankali ta sake kiranta Raihana,” a hankali Raihana ta ɗago kai, Hajiya Hauwa ta kalleta kai tsaye cikin idanu, sannan ta yi murmushi mai laushi, “I’m your mummy, so lemme take care of youuu.”