THE UNSPOKEN WORDS
ZAYD ARMAAN
CHAPTER 118
THE UNSPOKEN WORDS.
JIDDAAH BARKUM
———-
Raihana ta shiga gidan da gudu, muryarta na tashi tana kiran Umma cikin farin ciki, “Ummaaa! Umma! Ummaaa!” Mama Sabuwa, wadda take tsaye tana kwashe kayan shanya, ta ji muryar Raihana sai ta firgita, nan take ta saki kayan da ke hannunta, ta juyo tana kallon hanyar da muryar ta fito, “Qalu innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Wace wnn kaman Raihana? Lafiya kuwa?” Ta yi saurin matsowa gaba, tana kallon Raihana wadda ta tsaya tana haki, kamar wadda ta yi dogon gudu, “Raihana, lafiya? Me ya faru?” Raihana ta buɗe baki kamar za ta amsa, amma numfashinta bai daidaita ba, ta yi ƙoƙarin gaishe da Mama Sabuwa, sai dai kalmomin suka kasa fitowa yadda ya kamata, Mama Sabuwa ta ƙara buɗe ido, “Mun shiga uku! A daren nan ya koroki? Malam Hajara! Ku fito mana, akwai matsala!” Ta juya tana kiran yan cikin gidan, cikin wani azababben kira kamar wacce wuta take ci take neman taimako, “Shikenan, ta faru ta ƙare! Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Dama rayuwar nan aka ce ka tsaya iya matsayinka, kwarya ta bi kwarya!” Ta ɗan tsaya tana kallon Raihana, wadda har yanzu take haki, “Yanzu meye amfanin a ce an yi aure, sati biyu kawai har an dawo? Wallahi jikina ya yi sanyi, kamar ma zazzaɓi nake ji!” A lokacin, mutanen gidan suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya, kowa na tambayar abin da ya faru, babu wanda bai fito ba, domin irin yadda Mama Sabuwa take ta kiran mutane ya sa kowa ya ɗauka cewa wani babban al’amari ne ya faru, Umma kuwa tana fitowa daga cikin ɗakinta, gabanta na faɗuwa, da farko ta kalli Mama Sabuwa, sannan idanunta suka sauka kan Raihana, Raihana kuwa ta tsaya tana kallon Mama Sabuwa, ba tare da ta iya cewa komai ba, numfashinta ne kawai ke fitowa da sauri, yayin da farin cikin ganin iyayenta ya hana ta samun nutsuwa, da ta hango Umma, sai ta tafi gare ta da sauri, “Umma!” Ta faɗa tana rungumarta sosai, ta manne a jikinta kamar ƙaramin yaro da ya daɗe bai ga mahaifiyarsa ba, numfashinta har yanzu bai daidaita ba, Umma ma ta rungume ta, tana sauke ajiyar zuciya, duk da farin cikin ganin ɗiyarta, tsoron da ya kama ta bai bar ta ta ji daɗin zuwan ba, ta ɗan janye Raihana daga jikinta, ta riƙe kafaɗunta tana kallon fuskarta da kyau, “Raihana, lafiya? Me ya faru a daren nan?” Muryarta cike take da damuwa, “Me ya kawo ki haka? Ina Zayd ɗin? Kin bar shi ne a gida?” Ta sake kallon fuskarta, tana neman wata alama da za ta bayyana mata abin da ya faru, “Ki gaya min, me ke faruwa?” Raihana ta ɗan sauke numfashi, sannan ta kalli Umma da murmushi, “Mun je unguwa ne fa, Umma, shine ya ce na shigo na gaishe ku,” Umma ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, hannunta har yanzu a kafaɗar Raihana, “Subhanallah! To, me ya sa kika shigo da wannan gudun kamar wadda aka kora daga gida? Kin ba mu tsoro fa!” Raihana ta yi ɗan murmushi, sannan kamar wadda ta tuna da wani abu, ta zabura, “Wayyo Allah! Ban gaishe da Baffa ba fa!” Ba tare da ɓata lokaci ba, ta wuce wajen Baffa da sauri, da gaske, farin cikin ganin Umma ya sa ta manta da komai da ke kewaye da ita, ta ƙarasa gabansa ta zube, tana gaishe shi cikin ladabi, “Baffa, ina yini?” Baffa ya amsa gaisuwarta, idanunsa a kanta, yana kallonta cikin farin ciki, ya lura da hasken farin cikin da ke shimfiɗe a fuskarta, musamman sabida hasken lantarkin dake tsakar gidan, bayan ta gaishe shi, sai ta juya zuwa wajen Mama Indo, wadda take tsaye tana ta zabga wa Mama Sabuwa harara, Raihana ta gaishe ta cikin ladabi, Mama Indo ta amsa tana kallonta daga sama har ƙasa, sannan ta yi murmushi, “Ma Shaa Allah! Har kin yi kumari, yar nan! In Shaa Allah, mutuwa ce za ta fito da ke daga ɗakinki, duk wani mai mugun abu, ya ƙare a kansa!” Mama Sabuwa ta zabura kamar an taɓa mata ciwo, nan take ta juya da niyyar mayar da martani, “Ke kuma—” “KU DAI KUN JI KUNYA!” Muryar Baffa ta katse ta, yana yi musu tsawa, “Ba ku gajiya sai ku yi da kyau yanzu ai har mijin yarinya ya samu ya ji ku daga waje!” Nan take shiru ya mamaye tsakar gidan, Mama Indo ta haɗe fuska, Mama Sabuwa kuma ta cije baki, kuma duk da haka har yanzu kowacce tana kallon ɗayar da harara, Baffa ya girgiza kai, sannan ya juya ya nufi hanyar fita zuwa wajen Zayd, ya san idan ya biye musu sai ya bar shi a waje ba su gaisa ba ana ta wannan hayaniyar a cikin gida, Raihana kuwa ta janyo hannun Umma, “Umma, zo mu shiga ciki,” Umma ta bi ta, Maryam ma ta biyo bayansu, Bintu kuwa ta koma ɗakinsu tana hamma, domin ita ma barci ya fara ɗaukarta kafin hayaniyar Mama Sabuwa ta tashe ta, a tsakar gida kuwa, an bar Mama Indo da Mama Sabuwa, kowacce ta tsaya a inda take, tana zabga wa ɗayar harara, kuma da alama, babu wadda za ta fara sauke nata har sai ɗayar ta fara! Bayan sun zauna a ɗakin, Umma ta jingina da bayanta tana kallon Raihana da kyau, kallon da take yi mata ya sa Raihana ta fara jin kunya, har ta ɗago hannunta ta rufe fuskarta tana dariya, “Umma, sai kallona kike!” Umma ta yi murmushi, tana sauke ajiyar zuciya, “Me zai hana in kalle ki? Na daɗe ban zauna na kalle ki haka ba, naga kin yi kyau ne,” Raihana ta sake yin murmushi, amma ta kasa cewa komai, ta sunkuyar da kanta, tana wasa da igiyar bag ɗinta, Maryam tayi dariya, sannan ta miƙe tsaye, “Okay, Rayy, ku gaisa da Umma tukuna, zan dawo,” “Toh,” Raihana ta amsa a hankali, Maryam ta fita, ta bar su biyu a ɗakin, Umma ta ɗan gyara zamanta, sannan ta kalli Raihana da kulawa, “Raihana, bakomai ko? Kuna zaune lafiya?” Raihana ta ɗago kai da sauri, “Bakomai, Umma, lafiya kalau, Alhamdulillah,” Umma ta gyada kai, amma ta ci gaba da kallonta, “Allah ya sa haka, na san kin yi aure, kuma yanzu kina da sabon gida da sabuwar rayuwa, abin da nake so kawai shi ne ki riƙa tuna cewa zaman aure yana buƙatar haƙuri, fahimta da kuma hikima, ba kullum komai zai tafi yadda mutum yake so ba,” Raihana ta yi shiru tana sauraronta, Umma ta ɗan kama hannunta, “Allah ya ce a cikin Alƙur’ani: ‘Wa ‘āshirūhunna bil-ma‘rūf’ — ku zauna da matanku cikin kyautatawa,” (Suratun Nisa’i, 4:19), “Wannan yana koya mana cewa kyautatawa da mutunta juna suna da muhimmanci a zaman aure, ke ma ki yi ƙoƙarin kyautata wa mijinki, ki girmama shi, ki kuma riƙe mutuncinki, kada ki ɗauki kowane abu da zafi, amma kuma kada ki riƙa danne abin da ke damunki har ya zama wani babban abu, idan akwai matsala, a nemi hanyar magana cikin nutsuwa,” ta ɗan tsaya, sannan ta ci gaba da cewa, “Kuma Manzon Allah ﷺ ya ce: ‘Mafi alherinku shi ne mafi alheri ga iyalinsa,’ (Tirmidhi), don haka, zaman aure ba wai haƙuri daga ɓangare ɗaya kawai ba ne, kyautatawa, tausayi da fahimtar juna suna da muhimmanci daga ɓangarorin biyu,” Raihana ta gyada kai a hankali, tana jin kalaman Umma suna shiga zuciyarta, Umma ta ɗan matse hannunta, “Ki tuna kuma, ke ba ke kaɗai ba ce a gidan, za ki riƙa fuskantar abubuwa daban-daban, amma kada ki bari su sa ki manta da kanki ko da Allah, ki riƙa addu’a, ki kiyaye mutuncinki, kuma ki tuna cewa duk abin da ya dame ki, kina da Umma da za ki iya zuwa ki yi mata magana ban kuma ce ki dauko sırrın gidanki dan ina mahaifiyarki ki fadamin ba, a’a abında dük ya shige miki duhu kike neman shawara a kai shi nake nufi,” idanun Raihana suka yi rau rau, ta matsa kusa da Umma, ta ɗora kanta a kafaɗarta, “Na gode, Umma,” Umma ta shafa bayanta a hankali, “Allah ya miki albarka, ya ba ki zaman lafiya da mijinki, ya kuma sanya alheri a cikin aurenki, abin da nake so shi ne ki kasance cikin farin ciki,” “Ameen, Umma,” Raihana ta rungume ta sosai, tana jin daɗin kasancewa a kusa da ita, a wannan lokacin, kamar duk damuwar duniya ta yi nisa da ita, gidan da ta taso, muryar Umma, da wannan nutsuwar da take samu a jikinta duk sun tuna mata cewa komai canzawar rayuwa, har yanzu tana da inda za ta koma ta samu ƙauna da shawarwari, a daidai lokacin da Raihana take rungume da Umma, sai sukaji motsin labule daga ƙofar ɗakin, Baffa ya leƙo kansa ciki, yana kallon su, “Raihana, ki taso ku tafi, dare ya yi fa,” Raihana ta ɗago kanta daga kafaɗar Umma, “Toh, Baffa,” Baffa ya gyada kai, sannan ya juya ya fita, Raihana ta sauke ajiyar zuciya, ta miƙe tsaye tana ɗaukar jakarta, ta juya ta kalli Umma, amma kallon da take yi mata ya nuna kamar za ta fashe da kuka, ba ta son tafiya da wuri, musamman bayan ta samu damar zama kusa da mahaifiyarta, Umma kuwa ta fahimci abin da ke zuciyarta, ta gyada mata kai a hankali, “Ki je, Allah ya tsare ki,” “Ameen,” Raihana ta amsa cikin rawar murya, ta ƙara rungume Umma na ɗan lokaci, sannan ta saki jikinta ta fito daga ɗakin, Maryam na tsaye a wajen tana jiranta, da ta ga Raihana ta fito, sai ta kama hannunta suka fara tafiya tare har zuwa ƙofar gidan, Zayd yana tsaye a jikin motarsa, hannunsa ɗaya a aljihu, fuskarsa kamar yadda aka saba gani calm and composed, da Maryam ta gan shi, sai fuskarta ta haska da fara’a, “Assalamu alaikum, Yaya Zayd,” “Wa alaikumus salam,” ya amsa cikin sakin fuska, ya kalleta na ɗan lokaci, sannan ya tambaya, “Kin ƙi zuwa ko?” Maryam ta fashe da dariya, “Na zo fa! I think last week Thursday,” sai ta juya ta kalli Raihana, “Dama baki gaya masa cewa na zo ba!” Raihana ta yi saurin harararta tana murguda baki Maryam ta ƙara dariya, tana jin daɗin yadda Raihana take ƙoƙarin ɓoye kunyarta, Raihana ta ɗan sunkuyar da kanta, sannan ta ce a hankali, “Kin ce na gaya masa ne?” Zayd ya zuba mata idanu, yana kallonta ba tare da ya ce komai ba, Raihana kuwa ta ɗauke kai, ta ƙi kallonsa, ta mai da hankalinta ga jakarta kamar ita ce abu mafi muhimmanci a gabanta, Maryam ta yi dariya sosai, “Toh, kaga ba laifina ba ne!” Zayd ya yi ɗan murmushi kawai, ba tare da ya ce komai ba, sai ya buɗe bayan motar, ya fara fitar da wasu ledoji da aka shirya a ciki, tsaraba ce da ya saya musu tun bayan ya ajiye Raihana a gidan Anty Mariya lokacin da ya je masallaci ya yi sallar Isha bai shiga gıdan anty Mariya ba saida ya tsaya ya musu tsarabar, ya miƙa wa Maryam kayan, Maryam ta karɓa da mamaki, tana kallon kayan sannan ta kalle shi, “Wow! Yaya Zayd, har tsaraba ka saya mana?” Zayd bai ce komai ba, sai dai ya gyada kai a hankali, Maryam ta yi murmushi mai faɗi, “Angode sosai, Allah ya saka da alkhairi,” “Ameen,” ya amsa a hankali, Maryam ta sake kallon kayan cikin farin ciki, tana godiya a ranta, ba ta yi tsammanin zai yi tunanin kawo musu wani abu ba, musamman ganin yadda ya zo da Raihana kawai don ta gaishe su, Zayd ya rufe bayan motar, sannan ya zagaya ya buɗe wa Raihana ƙofar gaba, Raihana ta ɗan tsaya na daƙiƙa, ta kalle shi a taƙaice kafin ta shiga motar a hankali, bayan ta zauna, sai ya rufe ƙofar a hankali, ya zagaya ya shiga ta ɓangaren direba, Maryam ta ɗan ja baya daga motar, tana daga musu hannu, “Allah ya kiyaye hanya!” Raihana ta ɗaga mata hannu daga cikin motar, murmushi dauke a fuskarta, Zayd kuwa ya kunna motar, sannan ta fara tafiya a hankali, Maryam ta tsaya a ƙofar gidan tana musu waving, idanunta na bin motar har sai da ta ɓace daga ganinta, sai ta sauke ajiyar zuciya, tana kallon hanyar da suka bi ta juya ta koma cikin gidan, tana riƙe da tsarabar da Zayd ya ba su, sai wajen ƙarfe 11:45 suka shigo gida, Raihana tana fitowa daga motar tana gyara handbag ɗinta, yayin da Zayd ya rufe motar ya yi locking, ba tare da ɓata lokaci ba, ta nufi ɗakin nasa kai tsaye, duk da cewa a yanzu tana iya shiga ɗakinta ba tare da jin wani irin tsoro ba, amma dai ta daina kwana a ciki, tana zuwa ne kawai idan akwai wani abu da take buƙata, ta ɗauko ta dawo, ta saba da wannan arrangement ɗin, gaskiya zuwa yanzu, shi kuwa Zayd, bayan sun shiga gidan, ya zauna a falo na wasu mintuna, ya ɗan jingina da sofa, yana duba wayarsa kafin daga baya ya miƙe ya nufi ɗakinsa, Raihana kuwa har ta yi wanka, ta saka wata riga da wando na cotton masu kyau, sannan ta ɗaura hula a kanta, tana zaune a gefen gadon, tana kallon wani wuri cikin tunani, tun ranar da Zayd ya koma ɗakin Seeyama, ita ma ta dawo kwana a kan gadon sa, ta yi ƙaura daga kan sofa zuwa kan gadon ba wai ya hana ta kwanciya a kan gadon ba dama itace tayi niyyar kwanciya akan kujerar, sai kwatsam ta tuna da Sadiya, maid ɗinta, “Allah! Tun da muka tafi ban ma leƙa ta ba,” ta miƙe da sauri, tana shirin zuwa ta duba ko yarinyar tana buƙatar wani abu, amma a lokacin da ta buɗe ƙofa, sai suka kusa karo da juna, shi zai shigo, ita kuma za ta fita, da ta hango shi, sai ta yi saurin ja da baya, “Sorry…” Ta faɗa a hankali tana ba shi hanya, Zayd bai ce komai ba, ya wuce ya shiga ɗakin, ita kuma ta fita ta sauka downstairs, inda ɗakin Sadiya yake, ta tarar da yarinyar cikin barci, ta ɗan tsaya a ƙofar tana kallonta, sannan ta ja mata ƙofar a hankali, ta tabbatar ba ta tayar da ita ba kafin ta koma sama, lokacin da ta shiga ɗakin, Zayd yana cikin bathroom yana wanka, ta kalli gadon, sannan ta nemi waje ta zauna, bayan wasu mintuna, sai ta kwanta a gefe, tana jiran barcin ya ɗauke ta, ba ta daɗe da kwanciya ba, sai taji motsin ƙofar bathroom, Zayd ya fito, ɗaure da towel a ƙugunsa, ruwan wankan har yanzu yana ɗigowa daga gashin kansa, ya ƙarasa gaban madubi ya ɗauki abin shafawa, yana yi wa kansa grooming, bayan ya gama, ya nufi wardrobe ya zaɓi jallabiya, ya saka, ya ɗauki turarensa ya fesa a jikinsa, ƙamshin ya bazu a ɗakin, har ya iso inda Raihana take kwance, ta gefen ido ya kalleta, yana iya ganin yadda ta takure a gefen gadon, ta naɗe jikinta kamar wadda ba ta son ta ɗauki wani wuri da ya fi wanda take kai, bai yi magana ba, ya ƙarasa wajen gadon, ya miƙa hannu ya ɗauki pillow ɗaya, sannan ya ɗauki ɗayan duvet ɗin da ke gefe, Raihana na jin duk motsinsa, da farko ta ɗauka zai kwanta a ɗayan gefen gadon, saboda haka ta ci gaba da kwanciyarta, idanunta a rufe, amma hankalinta yana kansa, ba wai ta juya masa baya ba ne dama, a’a, tana kallon inda yake ne kawai, sai dai ta rufe idanunta kamar mai barci, sai dai lokacin da ta ɗan buɗe idanunta ta ga yana hanyar fita, ɗauke da pillows da duvet, sai zuciyarta ta buga da wani irin sauri, kafin ta gama tunanin abin da za ta yi, sai ta miƙe da sauri, wallahi, kawai ta tsinci kanta a tsaye, ba ta ma san lokacin da ta miƙe ba, “Wai… ina za ka je kuma?” Muryarta ta fito a hankali, amma akwai wata damuwa a cikinta wadda ita kanta ba ta fahimci daga ina ta fito ba, Zayd ya tsaya cak, hannunsa na riƙe da pillow da duvet, amma bai juyo ba, he remained still for a few seconds, kamar yana son tabbatar da cewa ita ce ta yi masa wannan tambayar, daga nan sai ya juya a hankali, ya kalleta, a karon farko tun da ya san ta, yau tana tsaye tana kallonsa kai tsaye cikin ido, ba kallon da take yi masa na sace ba, ba kuma kallon da take saurin kaucewa ba, wannan karon, idanunta sun tsaya a kansa bata ko kiftawa, shi ma ita yake kallon Raihana ta ji yadda zuciyarta take bugawa, amma duk da haka ba ta yi saurin ɗauke idanunta ba, she didn’t even look away this time, ta tsaya a inda take, hannayenta a haɗe a gabanta, tana jiran amsarsa, Zayd ya ɗan ɗaga gira, “Akwai wani abu da kike buƙata ne?” Raihana ta ɗan haɗiye yawu, amma idanunta har yanzu suna kan nasa, duk da yadda zuciyarta ke beating da mahaukacin race a cikin ƙirjinta, ya sake tambaya, cikin sanyin muryarsa, “Me kike buƙata?” Ta buɗe baki, amma kalmar farko ta ɗan makale a maƙogwaronta, cikin sanyin murya, ta ce, “Kai…”