ZAYD ARMAAN

A LOVE UNHIDDEN

by @jiddaahbarkum

ZAYD ARMAAN

CHAPTER 120

A LOVE UNHIDDEN

JIDDAAH BARKUM

———

Ta faɗa cikin ƙaramar murya, fuskarta a ɓoye a kafaɗar Zayd. Shi kuwa ya ɗan sauke numfashi, yana kallon yadda ta manne masa kamar ba ta da niyyar ɗago kanta. Ƙaramin murmushi ya bayyana a gefen bakinsa, sannan ya ɗan karkatar da kansa yana ƙoƙarin ganin fuskarta.

"What’s wrong?" Raihana ta girgiza kai a hankali, ba tare da ta ɗago ba. Zayd ya ɗan ɗaga gira. "Are you crying again?" Ta sake girgiza kai. "Then look at me." "Ba zan iya ba." "Why?" Ta ɗan motsa a jikinsa, tana ƙara ɓoye fuskarta. "Saboda…" "Saboda me?" Ta yi shiru. Zayd ya ɗan yi dariya a hankali, irin wacce ba kasafai yake yi ba. Ya kai hannunsa ya shafa bayanta, sannan ya ce, "My Raii."

Ta ji yadda ya kira sunanta cikin wannan sanyin muryar tasa. Ta ɗan ɗago kanta kaɗan, amma ba ta kai ga kallonsa ba. "Hmm?" "Look at me, Habibti." A hankali ta ɗago fuskarta. Idanunta suka haɗu da nasa, sai ta yi saurin son sake kau da kanta, amma wannan karon Zayd ya ɗan riƙe haɓarta. "Don’t run away." Ta yi shiru tana kallonsa. Ya ɗan matsar da babban yatsansa a kan kumatunta, yana nazarin fuskarta. "So, you’ve been hiding all these feelings from me?"

Raihana ta haɗiye yawu. "Ni fa…" "Hmm?" "Ka daina mana." Ta faɗa kamar za ta fashe da kuka. "Na daina me?" "Wannan tambayar." Ya ɗan murmusa. "I haven’t even started asking." Ta turo baki kaɗan, sannan ta sake sunkuyar da kanta. Zayd ya girgiza kai a hankali. "You know what? I have waited long enough to hear you say something like that." Raihana ta ɗago idanunta da sauri. "Me?" Ya ɗan yi shiru, sannan ya ce, "Tun ranar da na fara haduwa da ke, akwai wani abu da yake sa ni tunanin ki. Sometimes I don’t even understand why. I tried to ignore it, but it kept coming back."

Ta saurare shi cikin nutsuwa, zuciyarta na bugawa a hankali. "Ban saba da wannan feeling ɗin ba." Ya faɗa cikin sanyin murya. "I don’t know how to explain it, but I know what I feel whenever you’re around me." Ta ɗan buɗe baki, amma ta kasa cewa komai. Wannan ba irin Zayd ɗin da ta saba gani ba ne. Mutumin da yake magana kaɗan, wanda ba ya son bayyana abin da ke ransa, yau yana zaune yana gaya mata abubuwan da ya daɗe yana ɓoyewa.

Ba ta san lokacin da bakinta ya furta "Da gaske kake?" Ya ɗan ɗaga gira. "About what?" Ta ɗan runtse idanunta. "Abin da ka faɗa ɗazu…" Ya kalleta na wasu seconds, sannan ya amsa ba tare da wasa ba, "I mean every word, wife…" Ta ji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta. A hankali ta sake jingina kanta a kirjinsa, tana murmushi ita kaɗai. Zayd ya ɗora haɓarsa a saman kanta, hannunsa yana shafa bayanta.

Bayan wasu mintuna, sai ta ɗan motsa kamar za ta tashi daga cinyarsa. Amma kafin ta yi hakan, ya tambaya, "Where are you going?" "Zan kwanta…." "Already?" Ta ɗan kalle shi, sai kuma ta sauke kanta ƙasa a hankali, ta ce, "Kana son wani abu ne?" Ya ɗan murmusa. "Stay here." Raihana ta sake sunkuyar da kanta. "Ai na gaji." "Then rest." Ya ja baya ya jingina da headboard ɗin gadon, ya miƙe ƙafafunsa, sannan ya ɗan gyara zamanta a kan cinyarsa har ta jingina da kirjinsa. Sai ya ɗan ja duvet ɗin da ke gefensu ya rufe su da shi. Ya ɗauki hannunta ya riƙe a cikin nasa, yana kallon yatsunta.

"Habibti." "Uhmm?" ta amsa, idanunta a lumshe, tana jin kamar ba ita ce Raihana da ta sani ba. "Don’t ever think you have to compete with anyone for my attention." Ta ɗago kai a hankali ta kalleshi. "Ban ce ina takara da ita ba." "I know. But I want you to understand something." Ya ɗan dakata, sannan ya ci gaba, "You’re my wife, and so is she. I have responsibilities to both of you. But what I feel for you is something I won’t pretend doesn’t exist." Raihana ta yi shiru. Ta fahimci abin da yake ƙoƙarin gaya mata. Ba ya son ya yi mata alkawarin da zai sa ta manta da haƙƙin ɗayar matarsa, amma a lokaci guda yana son ta san cewa abin da yake ji a kanta ba wasa ba ne. Ta ɗan gyada kai kawai. Zayd ya kalleta, sannan ya ɗan shafa kumatunta. "Good."

Sai ta ɗan ɗaga kai tana kallonsa. "Amma…" "There’s an ‘amma’?" Ta ɗan turo baki. "Eh." "I’m listening." Ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta tambaya cikin sanyin murya, "Tun yaushe ka fara sona?" Zayd ya ɗan yi murmushi. "You want to know?" Ta gyada kai. "I’m still trying to figure that out myself." Ta yi ƙaramin murmushi, ba ta san ma ko zai iya gani ba, sannan ta sake ɓoye fuskarta a kirjinsa. Zayd ya ɗan yi murmushi yana kallonta. "What?" "Nothing." Ya ɗan matse hannunta a hankali. "Sleep, My Rai." Ta ɗago kai da sauri. "Kana ta faɗar wannan sunan." "My Rai?" Ta gyada kai, tana murmushi. Ya ɗan sunkuyar da kansa kusa da ita. "You don’t like it?" Ta yi saurin girgiza kai. "A’a…" "Then I’ll keep calling you that." Ta yi murmushi, sannan ta lumshe idanunta. A wannan karon, ba ta jin buƙatar ɓoye farin cikinta. Ta ji kamar wani nauyi da ta daɗe tana ɗauke da shi ya sauka daga zuciyarta.

Zayd kuwa ya ci gaba da riƙe hannunta, yana kallonta cikin shiru. Bayan ɗan lokaci, ya kai hannu ya kashe fitilar gefen gadon, ɗakin ya nutse cikin duhu mai laushi. A hankali ya zame ya kwanta akan pillow snn ya kwantar da ita a tsakanin ƙafafunsa, sannan ya ɗora kanta a kirjinsa. Ya gyara mata duvet ɗin, sannan ya sumbaci goshinta. "Goodnight, Habibti." "Goodnight…" Ta amsa a hankali, tana jin kamar komai ba a zahiri yake faruwa ba. A daren nan, ba ta yi mafarkin kalaman da take son ya furta mata ba. Domin a karon farko, ta ji su daga bakinsa da kanta.

Da ya fahimci numfashinta ya fara nauyawa, alamun barci ya fara ɗaukarta, Zayd ya ɗan motsa a hankali don kada ya tashe ta. Ya miƙa hannunsa zuwa gefen gadon, ya kunna switch ɗin fitilar ɗakin. Haske mai laushi ya mamaye ɗakin. Ya sake kallonta. Fuskarta a kwance a kan kirjinsa, idanunta a rufe, dogayen lashes ɗinta sun yi mata inuwa a saman kumatunta. Ƙananan lips ɗinta masu ɗan pink sun ɗan turo gaba kaɗan, kamar yadda ta saba yi idan tana barci. Ɗan gashin ta daga gefen kanta ya zubo a kan wuyanta sosai, yayin da sauran gashinta ya bazu a kan bayanta. Fuskarta ta yi fresh sosai, babu alamun damuwa a tattare da ita.

Zayd ya kasa kawar da idanunsa daga gare ta. Ya ɗan matsar da kansa, yana kallonta kamar yana son haddace kowane ƙaramin detail na fuskarta. His eyes lingered on her lips, sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali. Zuciyarsa ta yi wani irin skipping. Ya daɗe yana kallonta, har ya ji kamar da zai iya kwana yana kallon wannan kyakkyawar fuskar ba tare da gajiya ba. Idanunsa suka sake komawa kan lips ɗinta. A hankali ya ɗan haɗiye yawu, yana jin wani irin sha’awar sumbatar ta. Ya zuro harshensa ya lashi lips dinsa still staring at her soft lips

Amma bai so ya yi wani abu da zai sa ta fara jin tsoron kusancinsa. Yanzu da ta fara sakin jikinta a gabansa, da ta fara nuna masa abin da take ji ba tare da ta ɓoye komai ba, ba ya son ya yi gaggawar lalata wannan sabon confidence ɗin nata. Ya ɗan matsar da hannunsa a bayanta, yana kallonta na wasu seconds. A hankali ya sunkuyar da kansa, ya kai lips ɗinsa kan nata, ya sumbace ta cikin nutsuwa. Sumbatar ta kasance mai laushi, ba tare da ya tashe ta ba. Ya ɗan tsaya na ɗan lokaci, sannan ya janye kansa yana sauke ajiyar zuciya. Ya kalleta kuma, sannan ya miƙa hannu ya kashe fitilar.

Duhu ya sake mamaye ɗakin. Ya sake jawo ta jikinsa, ya rungumeta sosai, kamar uwa da ta fito daga ɗakin haihuwa ɗauke da sabon jaririnta, tana tsoron ko da ɗan motsi zai raba ta da abin da ta daɗe tana jira. Ya gyara kansa a kan matashin kai, ya ɗora haɓarsa a saman kanta, hannunsa yana kewaye da ita. A wannan daren, Zayd bai ji kamar yana riƙe da matarsa kawai ba. Ya ji kamar yana riƙe da wani ɓangare na zuciyarsa da bai san yana nema ba sai yau.

Karfe shida na safe. Haske ya fara kutsowa ta labulen ɗakin, yayin da Zayd ya buɗe idanunsa a hankali. Ya ɗan motsa hannunsa, sai ya ji wani abu mai dan nauyi a saman kirjinsa. Ya sauke idanunsa. Raihana ce. Ta yi ƙane-ƙane a jikinsa, kanta a kan ƙirjinsa, hannunta ɗaya a naɗe a wuyansa, ɗayan kuma ta ɗora a gefen cikinsa. Ƙafafunta ma suna nan kan nasa, kamar ba ta son ko ɗan tazara ta shiga tsakaninsu. Zayd ya ɗan kalli agogon gefen gadon. Karfe shida! Ya ɗan runtse idanunsa na seconds kaɗan. Ya makara sallar Asuba kenan. Ya sake kallon Raihana, yana tunanin ta inda zai fara tashi ba tare da ya tashe ta ba. Amma da ya yi ƙoƙarin motsa jikinsa, sai ta ƙara manne masa. Ya sauke ajiyar zuciya.

"My Raii…" Babu amsa. Ya ɗan karkatar da kansa, ya matso da bakinsa kusa da kunnenta. "Wake up, Habibti." Ta ɗan motsa, amma ba ta buɗe idanunta ba. "Babyy," ya sake kiranta a hankali. A wannan karon ta buɗe idanunta a hankali. Ganin fuskarsa kusa da tata ya sa ta yi ƙasa da ido, sannan ta sauke fuskarta a kan kirjinsa tana ɗan turo baki. Zayd ya kalleta. "Wake up, let’s pray. Mun makara." Kamar an tuna mata wani abu, sai idanunta suka buɗe sosai. Nan take ta tuna da abin da ya faru a daren jiya, har zuwa kan yadda ta manne masa, da yadda ta yi barci a jikinsa har wayewar gari. Da sauri ta ɗago jikinta daga kansa, ta matsa gefe, sannan ta juya masa baya. Kunyarta ta dawo mata gaba ɗaya.

Zayd ya kalleta na ɗan lokaci, amma bai ce komai ba. Ya dai gyara zamansa, ya sauka daga gadon, sannan ya wuce bathroom. Bayan ya yi wanka ya ɗauro alwala, ya fito. Ya sake kallon Raihana wacce take Zaune a kan gadon, har yanzu ba ta gama sakin kanta daga kunyar da take ji ba. "Go and perform wudu. Let’s pray, mun makara already." Ta yi masa ɗan nodding. Zayd ya wuce zuwa wardrobe, ya ɗauki kayan da zai saka, yayin da Raihana ta sauko daga gadon a hankali ta nufi toilet. Ba ta daɗe ba ta fito, ta karasa kan sofa ta dauko hijab ɗinta bayan ta kammala alwala. Zayd ya riga ya shimfiɗa musu sallaya. Ya gyara ta sosai, sannan ya tsaya yana jiranta. Da ta ƙarasa, ya tadda kabbara ya fara ya jan su sallah.

Suka yi sallar Asuba cikin nutsuwa. Bayan sun idar, Zayd ya zauna ya fara adhkar ɗinsa a hankali. Raihana ma tana zaune kusa da shi, tana bin bakinsa, tana maimaita abin da yake furtawa. Muryarsa a hankali take fitowa, ita kuma tana sauraro tana biye da shi. Haka suka ci gaba har suka kammala. Sai Zayd ya ɗaga hannayensa ya fara addu’a. Raihana ma ta ɗaga nata, tana cewa amin a wasu wuraren. Bayan sun gama, suka shafa fuskokinsu. Zayd ya juyo gare ta, sannan ya miƙa mata hannunsa domin su yi musabaha. "Sabahul khair, Habibti." Raihana ta fara kallon hannunsa da ya miƙo mata, sannan ta ɗago idanunta ta kalleshi. Shi kuwa yana nan yana kallonta, idanunsa a ɗan lumshe, fuskarsa cike da nutsuwa. Da sauri ta sauke idanunta, ta ɗago hannunta a hankali ta saka a cikin nasa. "Sabahul khair…" Suka gaisa. Amma kafin ta janye hannunta, Zayd ya riƙe shi a hankali, ya ɗago shi zuwa bakinsa sannan ya sumbaci bayan hannunta. Raihana ta kasa motsi na ɗan lokaci. Ya sake kallonta, yana riƙe da hannunta. "Did you sleep well?" Ta ɗan gyada kai, ba tare da ta iya kallonsa sosai ba. "Alhamdulillah…" Zayd ya ɗan murmusa yana kallonta kamar zai cinyeta Good ya furta a hankali

A ɗayan ɓangaren, Seeyama kuwa. Tun bayan fitarsu ta kashe wayarta, ta kwanta tana ta tunanin inda Zayd da Raihana suka je. Safina ta yi ta kiranta, amma ba ta sake kallon wayar ba. A ƙarshe ma, kashe ta yi gaba ɗaya. Ta yi ta juye-juye a kan gadonta, tana tunanin ko sun je wani wuri ne ko kuma Zayd ya shirya wani abu na musamman da ba ta sani ba. Ba ta san lokacin da barci ya ɗauketa ba, kuma ko dawowarsu ba ta ji ba. Da misalin ƙarfe huɗu na asuba ta farka. Ta buɗe idanunta a hankali. Ta zauna, tana kallon ƙofar ɗakin. Ta ɗauki wayarta ta duba lokaci. Har aka kira sallar Asuba, babu Zayd, babu alamunsa. Bai zo ya tasheta ba, kamar yadda yake yi duk asubar duniya. Ko dai ba su kwana a gidan ba? Ta faɗa a ranta, kafin ta miƙe daga kan gadon. Ta nufi tagar ɗakin, ta yaye labulen a hankali tana leƙen compound ɗin. Idanunta suka sauka kan parking lot. Motar Zayd ce. Ta ɗan tsaya tana kallonta, kamar tana son tabbatar da abin da take gani. A hankali ta saki labulen, ta dawo cikin ɗakin. Ta zauna a gefen gadonta, ta ɗora hannayenta a kan cinyoyinta, sannan ta zubawa wuri guda ido lost in thought Ta ɗan cije leɓenta, tana jin wani irin rashin daɗi yana tasowa a ranta.