ZAYD ARMAAN

A LOVE UNFOLDING

by @jiddaahbarkum

ZAYD ARMAAN

CHAPTER 122

A LOVE UNFOLDING

JIDDAAH BARKUM

———

Seeyama ta miƙe ta shiga bathroom. Bayan ta gama wanka, ta shirya cikin wata atamfa mai kyau, ta ɗora mayafinta sosai, tana mai tabbatar da cewa ta fito cikin kamalar matar aure. Ta zauna a gaban mirror, tana kallon yadda fuskarta ta yi ja, yayin da idanunta suka kumbura saboda yawan kukan da ta yi. A hankali ta miƙa hannu ta ɗauko sunglasses ɗinta, ta saka a idanunta. Ba ta son duk wanda ya ganta ya fahimci irin halin da take ciki. She didn’t want anyone asking questions.

Bayan ta gama shiryawa tsaf, sai ta miƙa hannu ta ɗauki wayarta. Kai tsaye ta danna sunan Safina ta kira. A lokacin kusan ƙarfe goma na safe. Wayar ta yi ring sau biyu kafin Safina ta ɗauka. "Hello?" Seeyama ta fara magana cikin muryarta da ta ɗan dusashe. "Ina kike ne?" Safina ta amsa cikin sauƙi. "Ina gida mana. Lafiya?" Seeyama ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce, "Wajen mutumin nan nake son ki raka ni."

Safina ta yi wata dariya a ɗayan ɓangaren wayar. "Kin hanga Kin hango cewa babu wata mafita kenan? Finally, kin yarda za ki koma?" Seeyama ta sake yin shiru. Bayan wasu seconds ta amsa. "Ba abin da kike zato ba ne. Ina so ne in ji, jinin da na gani, daga ina yake? Saboda a iya tunanina, na san ba period ba ne. Kuma a lokaci ɗaya ya zo, ya ɗauke, bai sake dawowa ba. Kin ga kuwa ina da enough reasons na neman sanin daga inda ya fito. Tun lokacin nake sakawa kaina abubuwa a rai, kuma hakan yana damuna. I just want to be sure."

Safina ta ɗan tabe baki. "Wahala ce ba ta ishe ki ba, Seeyama… An ce miki ga solution, kin zauna kinata wani nuƙu-nuƙu. Whatever!" Seeyama ta katse ta. "Za ki shirya kawai ki raka ni, saboda ni na shirya already." Safina ta yi ajiyar zuciya. "Gaskiya sai dai anjima, wajen two. Yanzu haka akwai inda zan je, kuma na riga na yi alkawari. So ki jirani, na gama first." Seeyama ta sauke numfashi tana kallon kanta a mirror. "No qualms at all. Dama zan je gidan Mommy ne. Idan kin gama, just ping me up, sai mu wuce." "Alright, see you then." Safina ta amsa, sannan Seeyama ta kashe wayar.

Ta ajiye wayar a kan dressing table, ta sake kallon kanta a mirror. Ta cire sunglasses ɗin na ɗan lokaci, ta zuba wa idanunta ido. Har yanzu tambayar da take son amsar ta ce ɗaya. Where did that blood come from? Ta sake saka sunglasses ɗin, sannan ta miƙe daga kujerar ta dauki Jakarta da car key ta nufi compound.

Zayd ya koma part ɗin Raihana, amma maimakon ya nufi ɗakin kai tsaye, sai ya zauna a falon, a kan kujera, yana kallon football. Har wajen ƙarfe 9:30 bai tashi ba. Ba wai don yana da wani abin yi ba ne, sai dai yana tunanin tana bacci. He didn’t want to disturb her, especially after the little sleep she had managed to get. Sai da ƙarfe goma daidai sannan ya kashe talabijin, ya miƙe calmly, ya ɗauki wayarsa daga kan center table, sannan ya nufi ɗakin.

Tun daga corridor, ƙamshin turaren wuta ya fara masa sallama. A hankali ya kai hannunsa kan handle ɗin ƙofar, ya murɗa, sannan ya tura ƙofar ya shiga. Idanunsa suka fara yawo a cikin ɗakin a hankali, yana kallon komai. The room was perfectly neat and smelled so nice. Kamar ba cikin ɗakin nan aka kwana ba. Gadon ya yi fes, an shimfiɗa shi da wani kyakkyawan bedsheet, komai yana cikin tsari. Even the smallest details were perfectly arranged. Sai idanunsa suka sauka a kanta.

Raihana ta yi wanka, sanye take da wata baƙar silk luxury abaya mai laushi, wadda ta zauna a jikinta cikin nutsuwa. Ta ɗaura dankwalin rigar, tana sunkuye a wajen socket, tana kashe burner ɗin turaren wuta. Da jin motsinsa, ta ɗago. Idanunsu suka haɗu na ɗan lokaci, amma da sauri ta kawar da nata. Ta kashe burner ɗin gaba ɗaya, sannan ta miƙe ta tsaya a wajen Tana riƙe da gefen rigar ta da hannayen ta biyu. A hankali ya fara takowa zuwa gare ta. "Baki koma bacci ba?" Ya fada da Wnn sanyayyar muryar ta shi Ta ɗan sunkuyar da kanta. "Na kasa yi." "Kin kasa yi" ya sake tambaya Ya tsaya yana kallonta. Ita kuma idanunta suna ƙasa, ta kasa ɗaga su ta kalle shi. Sai kawai ta yi masa ƙaramin nod, kamar tana ƙoƙarin ƙara tabbatar da amsarta. Ya yi shiru. Just watching her.

Da ta lura ya daɗe bai ce komai ba, sai ta ɗan ɗago kanta. Amma ganin yadda yake kallonta ya sa ta sake sauke idanunta da sauri. Ta fara wasa da yatsun hannunta, tana haɗa su wuri guda. Bayan ɗan lokaci, ta buɗe baki a hankali, cikin sanyin muryarta. "Me za ka ci?" Zayd ya ɗan matsa kusa da ita. Ta dan ja da baya ya sake matsowa ta sake baya har saida ya rage kiriss ta hade da bango snn ya tsaya a hankali yace "Look at me." Ta ɗan maqe kafaɗunta, tana nuna alamun a’a, ba tare da ta ce komai ba. "It’s fine," ya faɗa cikin nutsuwa. "Tunda ba so kike na ci ba." A hankali ta ɗago kanta. "Ina so mana." Ya ɗan karkatar da kansa, yana kallonta. "Then look at me."

A wannan karon ta ɗaga idanunta, suka haɗu da nasa. Duk da kunyar da take ji, ta yi ƙoƙarin ci gabadaya da kallon sa. Zayd ya zuba mata idanu, kamar yana nazarin yanayin fuskarta. "Ask me again." Ta ɗan buɗe baki, amma kalmar ta ƙi fitowa. Ta haɗiye yawu, sannan ta yi magana cikin ƙaramar murya. "Me… za ka ci?" Idanunsa har yanzu a kanta. Calmy yace "Ke." Sai ta yi shiru. Kamar an dauke ruwa Gabanta ya yi wani irin faɗuwa. Ta kasa motsi, ta kasa magana, kawai ta tsaya tana kallon kasa tana jin yadda zuciyarta ke bugawa.

Zayd ya matso sosai, ya ja ta a hankali zuwa bango, bayanta ya haɗu da bangon. Ya tsaya gabanta, yana kallonta cikin nutsuwa. Ba ta ce komai ba sai balain bugün zuciya Ya ɗan sunkuyo gare ta, sannan ya furta cikin ƙaramar murya a hankali yace "zaki bani…" For a moment, kamar numfashinta ya tsaya. Kalmar da ya faɗa ta maimaitu a kunnenta, tana ƙoƙarin fahimtar ko da gaske abin da ta ji kenan. Ta ji wani irin zafi ya bazu daga kirjinta har zuwa kunnuwanta. Her heart was beating so fast, she almost feared he could hear it. Ta sauke idanunta, amma hakan bai taimaka ba. Domin yanzu ta fi jin kusancinsa. Ƙamshinsa ya gauraya da na turaren wuta da ke cikin ɗakin, yana ƙara rikita mata tunani. Yana tsaye gabanta, yana kallonta cikin nutsuwa. Ita kuma ta kasa ɗaga nata idon cikin nasa. She could feel his gaze on her, and somehow, that alone was enough to make her forget every word she had wanted to say.

"Answer me, wife." A hankali, cikin wata irin shagwaɓa da ita kanta ba ta san yaushe ta iya ba, ta furta: "Ni dai ka bariiii…" Zayd ya ɗan ɗaga gira. "Me zan bari?" Ta kasa kallonsa. Da sauri ta ɗaga hannayenta biyu ta rufe fuskarta. "Wannan maganar mana! Kai, ba ka jin kunya ne?" A wannan karon Zayd ya yi dariya, har fararen haƙoransa suka bayyana. Ba dariyar da ya saba yi ba, but a quiet, genuine laugh that made her heart skip another beat.

Ya sake matsowa kusa da ita, sannan a hankali ya janye hannayenta daga fuskarta, ya riƙe su cikin nasa. Ya sunkuyo har ta fara jin numfashinsa a fuskarta. Da sauri ta lumshe idanunta. "Dama miji na jin kunyar matarsa ne?" ya tambaya cikin ƙaramar murya. Ta buɗe baki kamar za ta ba shi amsa, amma babu abin da ya fito. Ya ɗan matso da fuskarsa kusa da tata, yana kallonta. "Kuma ke ma…" ya ɗan dakata, "wannan kunyar da kike ji, ina so na cire ta. Ta ishe ni haka." Raihana ta ji kamar ƙasa ta buɗe ta shige. Ta kasa buɗe idanunta, hannayenta kuma suna nan cikin nasa. A hankali ta yi ƙoƙarin janye su, amma bai sake su ba.

Ya ɗan matso kusa da ita, idanunsa a kan nata, sannan ya furta cikin ƙaramar murya mai cike da taushin yanayi: "I want to feel your warmth all over me, Habibti." Raihana ta ji zuciyarta ta sake buguwa da ƙarfi. Ta buɗe idanunta a hankali, suka haɗu da nasa, kafin ta sake sunkuyar da kanta, tana jin kunya ko da numfashinta ya fara sauyawa. Ya dago hannunshi daya ya dago da kanta a hankali ta bude idanunta nan suka sauka fess cikin nashi Suka ci gaba da kallon juna, babu wanda ya fara kawar da idanunsa. For a few seconds, komai ya yi shiru a tsakaninsu, sai ƙamshin junansu da sautin numfashinsu. Haryanzu yana nan riƙe da ɗayan hannunta Ya sauke wanda  ya rike habarta zuwa fuskarta, yana shafa gefen kumatunta da bayan yatsunsa. Idanunsu har yanzu a haɗe suke. A hankali ya matsar da babban yatsansa zuwa leɓɓanta, yana bi a hankali kamar yana nazarin yanayinsu. Raihana ta ɗan buɗe baki, sannan ta haɗiye yawu. Her heart was racing, and she could barely hold his gaze.

Zayd ya ɗan sunkuyo kusa da ita, ba tare da ya cire idanunsa daga nata ba. "I want to kiss these lips, wife. I've been dying to do it, but only with your permission." Ya ɗan dakata, yana kallonta cikin nutsuwa. "Should I?" Raihana ta kasa amsawa nan take. Ta ji yadda kunya ta mamaye ta, amma a wannan karon ba ta kawar da idanunta gaba ɗaya ba. Ta tsaya tana kallonsa, lips dinta a hankali suka motsa kamar za ta yi magana, amma muryarta ta ƙi fitowa. "Please…" ya sake faɗa a hankali, yana ci gaba da shafa leɓɓanta da babban yatsansa.

Wallahi, ita kanta ba ta san abin da ya faru da ita ba. Kamar hankalinta ya ƙaurace mata. She couldn’t even think straight with him standing that close, looking at her like that. Kafin ta ankara, sai kawai ta tsinci kanta da gyada Kai alamar "ehh" Ai kuwa, da ya ga hakan, wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskarsa. He had his answer. A hankali ya fara matsowa da fuskarsa saitin tata. Raihana kuwa ta lumshe idanunta da sauri, tana jin yadda jikinta ya fara rawa a hankali. Ta kasa tunanin komai face kusancinsa da bugun zuciyarta da ya ƙi sassautawa.

Zayd ya ɗan dakata na ɗan lokaci, yana kallon fuskarta, sannan a hankali ya ɗora bakinsa a kan nata. At first, it was a soft kiss. A gentle touch, almost like he was giving her time to get used to him. Amma da ta yi ƙaramin motsi na amsa masa, sai ya ƙara matsowa, ya ɗan karkatar da kansa, yana sumbatar ta da wani irin longing da ya daɗe yana dannewa. Ya cafkii harshen ta, this time a little deeper, his hand resting gently Akan kumatunta ya rike Fuskarta while the other held her hand.

Raihana ta kasa gane yadda lokaci ya tsaya mata. Ta ji kamar duk wani tunanin da ke kanta ya ɓace. Hannunta da ke cikin nasa ya ɗan matse shi, yayin da ɗayan ta kai kan ƙirjinsa, kamar tana neman wurin riƙewa. Zayd ya ɗan ja da baya na ɗan lokaci, amma bai yi nisa ba. Goshinsu na haɗe yana kallonta yayin da ita kuma take ƙoƙarin samun nutsuwarta. Zayd ya ɗan ja da baya na ɗan lokaci, amma bai cire bakinsa daga nata gaba ɗaya ba. Kafin ta samu damar buɗe idanunta sosai, sai ya sa hannayensa a kugunta, ya ɗago ta sama.

Da sauri Raihana ta miƙa hannayenta zuwa wuyansa, ta riƙe shi sosai. Ƙafafunta kuma suka zagaye kugunsa, tana manne da shi saboda ba ta yi tsammanin zai ɗauke ta ba. A hankali ya janye bakinsa daga nata. Wani ƙaramin numfashi ya kuɓuce mata unexpectedly, wanda ya sa Zayd ya ɗan yi murmushi yana kallonta. "Habibti…" ya kira ta cikin wata rikitacciyar murya. Amma ita ina! Da sauri ta ɓoye fuskarta a wuyansa, tana jin kunya. Ya daidaita riƙonsa, yana tabbatar da tana cikin comfortable pose, sannan ya ɗan ɗago fuskarsa ya sumbaci kumatunta. "Look at me." Ta girgiza kanta a hankali, har yanzu ta ƙi ɗagowa. "Babyyy…" ya ja sunan yana Jin wani wani yanayi na ratsa jinin jikinsa

A hankali ta ɗago, idanunsu suka haɗu. Ya yi mata wani ɗan murmushi, kafin ta ankara ya sake haɗa bakinsu. This time, he held her closer against him. Raihana ta ƙara manne masa, hannayenta a wuyansa, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri. She had no idea how she had gone from being shyly embarrassed to being wrapped in his arms like this. Ba ta san lokacin da ita ma ta fara mayar masa da martani ba. Da farko a hankali take yi, cikin ɗan shakku, kamar har yanzu tana jin nauyin abin da take yi. Amma da ta ji ya ɗan sassauta sumbatar, sai ta samu ƙarfin gwiwar mayar masa da ita. Ta ɗan matsa bakinta kan nasa, hannayenta kuma suka ƙara ƙarfafa riƙonsa a wuyansa.

Wannan karon Zayd ne ya ɗan rikice. Bai yi tsammanin Raihana za ta fara mayar masa da sumbatar haka ba. Da ya lura da yadda take tsotsar harshensa sai ya sake cafkar na ta, yana tsotsar ta cikin wani irin ƙauna da kewar da ya daɗe yana dannewa. Raihana ta lumshe idanunta sosai, ta manta da kunyar da take ji a farkon lokacin. Abin da kawai take ji shi ne kusancinsa, hannayensa a kugunta, da yadda yake riƙe da ita kamar ba ya son ya sake ta. A hankali ya fara takawa da ita zuwa hanyar gadon ɗakin, still kissing her, kamar yanzu ne suka fara gano wannan sabon yanayin da ke tsakaninsu.

A babban falon Ummie, Anty Mariya ce zaune a kan kujera, tana karɓar cup ɗin shayi daga hannun Ummie wadda ta zauna kusa da ita. Sun ɗan yi hirar gida da iyali, kafin Ummie ta dawo da maganar da take son ji tun zuwan Mariya. "To, ya ku ka yi da Raihana?" Anty Mariya ta ɗan ɗago kai daga cup ɗin shayin da take riƙe da shi. "Lafiya lau. Masha Allah, yarinyar nan tana da nutsuwa." Ummie ta yi murmushi. "Allah ya ƙara mata. Amma dai, Mariya, ba fito wa kika yi kika ce  mata Hauwa ba ta da kirki ba ko?" Anty Mariya ta fashe da dariya. "Ummie! Tsoron Hauwa kike ji ne?" Ummie ta kalleta, ta ɗan girgiza kai. "Idan ma haka na faɗa mata menene? Na ga duk kin damu." "Ba haka nake nufi ba, Mariya." Ummie ta gyara zamanta, ta kalleta da kyau. "Kin ga yarinyar nan surukar mu ce. We can’t be too open with her just yet. A hankali za ta fahimci komai da lokaci. Ba na son ta fara jin wasu abubuwa tun kafin ta fahimci yadda dangantakar iyali take."

Anty Mariya ta ajiye cup ɗinta a kan table, tana murmushi. "To, ai kawai magana na yi mata cikin hikima. Ba wani abu ba." Ummie ta ɗan yi murmushi, ta girgiza kai. "Kin san dai ina son komai ya tafi cikin nutsuwa." "Na sani, na sani," Anty Mariya ta amsa tana dariya. Bayan sun ɗan yi wasu maganganu, Anty Mariya ta sake dawowa kan maganar Raihana. "Gaskiya Ummie, Zayd ya samu mace." Ummie ta ɗago ta kalleta. "Me kika gani?" Anty Mariya ta yi murmushi. "Ga kyau, ga ladabi, ga kunya. Kai, komai dai da kika sani namiji yana so a wajen mace, Wallahi yarinyar nan ta haɗa su. Ba wai kyau kaɗai ba, akwai nutsuwa da tarbiyya a tattare da ita. Even the way she talks, akwai mutunci a cikin maganarta." Ummie ta yi murmushi mai cike da jin daɗi. "Alhamdulillah. Allah ya sa ta zama alheri a gare shi, ya kuma sa shi ya zama alheri a gare ta." "Amin," Anty Mariya ta amsa. "Ni dai na ji daɗin yadda na same ta. Allah ya kiyaye musu soyayyarsu daga evils eyes dan akwai su." Ummie ta amsa da murmushi, tana jin wani irin daɗi a zuciyarta. A gare ta, farin cikin ɗanta da kwanciyar hankalin matansa abu ne mai muhimmanci fiye da komai.