JAHILCI YAFI HAUKA

JAHILCI YAFI HAUKA

by @108609042245664568041

 Bismillahir Rahmanir Raheem

Page 01


Dedicated to my dearest brothers 


Safiya ce mai dauke da tarin ni'ima da annashuwa a zuqatan mafiya yawa daga cikin halittun Rabbil izzati, a cikin sauri wanda ya zame mata kmr dole, due to circumstances take shiryawa cikin well ironed uniform dinta, ganin time yana ta tafiya da sauri, kasancewar weather din sanyi ne lokaci yafi gudu.

   A shirye tsaf ta fito ta dan bi gdn nasu da kallo ganin ko ina tsaf, ba tare da ta tsaya bata lokaci ba, ta fito qofar gdnsu inda mai adaidatan da yake kaita school kullum ke jiranta, kasancewar tana fitowa wanka ta kira ta shaida mishi ta kimtsa.

  Fuskarta dauke da waltacccen murmushi ta qaraso gareshi ta dan rusunar da kanta tana fadin " Yaya brka da safiya". Shima da murmushin ya amsa mata da fadin " brka dai Mqlam Rumaisa". A nutse ta shiga adaidatan ba tare da ta sake cewa komai ba yaja adaidatar suka bar layin.
   
  Kai tsaye assembly ground ta nufa, kasancewar duk saurin da take sai da tayi late din da take tsoro, isowarta yayi dai-dai da fara jawabin principal dinsu, cikin hadaddiyar English dinsa yake sanar da students din ana gab da rufe biyan registration din SSCE.

   A zahiri fuskar Rumaisa ta bayyanar da damuwa, yayin da zuciyarta ta cika da tunanin ta ina zata fara neman kudin registration din. A haka dai aka sallamesu daga assembly ground din, ba tare da ta qara fahimtar me ake fada ba. Kai tsaye Class dinsu suka nufa, wannan karon cikin yanga da iyayi irin wanda aka san senior classes dashi. Wunin ranar dai har aka tashi cike take da zullumi, da kuma tunanin yadda zata tunkari gidansu da zancen kudin take, ba don babu kudin biyan ba, sai dai ba za'a biya din bane, saboda ana gani bata kai a kashe wannan kudin saboda ita ba.
    Ana tashi kuwa mai adaidatan da ya kawota shi ya sake zuwa ya mayar da ita, tana sallama kuwa taci karo da daya da tashin hnklin da in da sabo yaci ace ta saba,  sai dai Hausawa kqnce "ba'a sabo da wahala".
   Abbanta tsaye a tsakiyar gidan nasu, yayin da Daadah mahaifiyarta ke qoqarin shirya gawayi cikin mangal dinsu, gefe guda kuwa Innah Asabe ce, wacce ta kasance Kakarsu, mahaifiyar mahaifinsu, tana zaune kan yar kujerar " tayani tsegumi".
    Bilal wanda ya kasance qanin Rumaisa, zaune ya dan jingina da jikin Innah Asabe, yana ta matsar kwallah wanda kana gani kasan na munafurci ne.
   Cikin seconds qalilan Rumaisa ta gama nazqrtar gdn nasu, sai kuma tayi sqllama wannan karon a sanyaye muryarta ke fita, Daadah ta dago a nutse jin yadda diyar tata ta shigo a sanyaye, abinka da mahaifiya, within some seconds ta karanci cewa tana cikin damuwa, amma tana qoqarin dannewa