JAHILCI YAFI HAUKA

Page 2

by @108609042245664568041

Abba da Inna Asabe a tare suka bita da wani mugun kallo mai fitowa daga qasan zuqatansu, Rumaisa ta dan rusuna tana fadin Abba brka da rana, a maimakon amsa wani mugun tsaki yaja yana fadin " daga ina kike?".
 
  Da madaukakin mamaki ta dago tana fadin Abba daga makaranta nake, kafin ta kai qarshen zancen Innah tayi caraf ta amshe da cewa " daga yawon gantali dai kike, a riqa fakewa da makaranta ana tafiya yawon ta zubar". Idan baka dauki mataki ba wlh kana gani za'a haifa maka shege cikin gidanka babu yadda ka iya, tunda kai dai an shanyeka.

  "Waahh! Inaaa ai har duniya ta tashi billahillazi ba'a haifi macen da zata shanyeni ba". Abba ya fada yana zaro manyan idanunsa waje, Rumaisa dai a sanyayen ta fada dakinsu, tana jinjina makirci irinna Innah Asabe, ace mutum ya girma amma bai riqe girmansa ba? donma Daadah Allah ya zuba mata haquri, da ace irin yaran yanzu ne tabbas za'a samu mai nakadawa Inna shegen duka kuma a zauna lafiya.

   Kukan Bilal ne ya katse mata tunanin da take, a rude Abba ke fadin " yi shiru Dan baba yanzu zan samo maka abinci mai dadi ma kuwa". A shagwabe yace "Abba kuma bana son fara da mai". Innah tace toh yi sauri ka samo mishi tunda na lura muguwar matarka, yar bakin ciki ba gamawa zatayi ta bashi ba, tunda take bakin ciki da zuwanshi duniya".

Abba ya nufi qofar gda yana fadin "yanxu zan komo Innah, bari in gani ko Jummala mai shinkafa ta gama a zubo mishi da zafinta".  Daadah kuwa tana ta ayyukanta ko tak! bata ce musu ba, sai da ta dora sanwar, ta shiga daki inda taci karo da Rumaisa na qoqarin fitowa tayata aikin, tunda ta canza kayanta zuwa atamfa mai sauqin kudi.

A tsanake Daadah ke bin fuskar Rumaisa da kallo, duk da tana ta qoqarin boye damuwar, a bakin gado ta zauna tana fadin " Lafiya kika dawo babu walwala? Ai kuwa kamar jira take Daadah tayi magana ta zauna gefenta gami da riqo hannunta, cikin marairaicewa tace "Daadah kudin makaranta ake so."
" wani irin kudin makaranta? Yaushe na baki kudin kika kai? da har zaki ce kudin makaranta?
" Kudin Exam nake nufi Daadah" ta fada tana sake marairaicewa.
Daadah ta danyi jimm sa'annan ta aro jarumta don bata son ta karya mata zuciya, duk da cewa yanzunma jikinta a sanyaye, tace " ba damuwa insha Allah za'a samu yadda za'a yi, na san Ubangiji bazai hana min yadda zanyi ba." ta Kararasa fada damuwarta na gaza boyuwa.