Masarauta

GUDU A DUHUN DAJI

by @khadijaharuna389



๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•

bismillahir rahamanirrahim 




Dajin Dausayi duhu ne, ciyawa mai kauri. Amal ba ta taba shiga irin wannan duhun ba.

Takalminta ya cire, mayafinta ya makale a kaya. Amma hannun Zayd na rike da nata, ba ya sakinta.

Zayd, ina zaka kai ni? Ta ce tana haki, muryarta na rawa.

Inda babu wanda zai raba mu. Inda ba gimbiya bace, ba makiyayi bane. Mu mutane ne kawai.

Suka tsaya karkashin wata bishiya babba. Zayd ya juyo ya kalle ta. Fuskar Amal cike da gumi da tsoro, amma idanunta suna haske a cikin duhu.

Amal, idan Sarki ya sani, zai kashe ni. Ki sani.

Ta girgiza kai.

Idan ya kashe ka, ni ma zan mutu. Ba zan auri Faisal ba. Wallahi ba zan auri shi ba.

Zayd ya yi shiru. Sai ya matso kusa da ita. Ya daga hannu ya share gumin dake fuskarta.

Zan kare ki. Ko da da rai na.

A daidai lokacin ne, wani hasken wuta ya bayyana a nesa. Hasken fitilu masu yawa. Muryoyin mutane.

Sun biyo mu! Zayd ya ce.

 Taji  muryar Yarima Faisal tana ihu.

KU NEMO SU! GIMBIYA TANA CIKIN HADARI! MAKIYAYIN YA SACE TA!

Amal ta rude.

tace  karya ne! Ni ban fada ba an sace ni!

Zayd ya san dabarar Faisal. Idan ya ce an sace Gimbiya, to duk fada zai nemi su a matsayin masu laifi.

Ba mu da lokaci, Zayd ya ce. shigawannan kogon. Shiga ciki. 

Ya tura ta cikin wani karamin kogo da ke bayan bishiyar. Kogo ne kunkuru, amma duhu ne sosai.

Shiga ki boye. Kada ki fito komai ya faru. Ki ji ni?

A'a! Ba zan bar ka ba!

Ki yi shiru! Zayd ya rufe bakinta da hannu a hankali. Idan sun kama ni, ki gudu ki koma fada ki ce ni na tilasta ki. Ki ce ni makiyayi ne na sace ki. Sai ki kubuta.

Hawaye ya cika idanun Amal.

A waje, hasken fitilu ya kara kusantowa. Ana jiyo takun dawaki.

Zayd ya fito daga bakin kogon, ya tsaya a waje, ya bar Amal a ciki ita kadai.

Ya daga hannayensa sama.

Ni ne! Ni na sace Gimbiya! Ga ni nan!

Amal a cikin kogo ta rufe bakinta da hannu don kar a ji kukan da take yi.

An kama Zayd.

Me zai faru da Amal da ke boye a cikin kogo? Shin Faisal zai ganota


 by Cutie