HUKUNCIN KISA
๐๐๐๐
bismillahir rahamanirrahim
Kurkurkun fada ba wuri bane da Gimbiya ta taba zuwa.
Kasa dako ne, ruwa na digo daga sama. Warin fitsari da jini.
A tsakiya, Zayd a daure yake. Hannayensa daure a baya. Fuskarsa cike da duka. Jiya dare an buge shi.
Amal da Zulaiha sun iso a boye. Zulaiha ta baiwa mai gadi zinaren kunne daya, ya bar su su shiga na minti biyu kacal.
Zayd! Amal ta fadada a hankali, ta runtuma zuwa gare shi.
Zayd ya daga kai. Idanunsa suka haskaka da ganinta.
Amal? Me kike yi a nan? Ki tafi! Idan Sarki ya ganki...
Yi shiru. Ta fito da takardun daga mayafinta. Ka duba. Ka duba abin da mahaifina ya yi.
Zayd ya karanta takardar da idanu masu rawa. Sai ya yi shiru mai tsanani.
Don haka... don haka suka saida kauyena? Mahaifina, mahaifiyata, kanwata... an sayar da su kamar akuya?
Amal ta kamo hannunsa.
Ba zan bar hakan ta faru ba. Na san yadda zan ceci ku.
Ta kalle shi cikin ido.
Za su yanke maka kai gobe da safe. Amma akwai hanya daya. Sai ka auri ni.
Zayd ya bude baki.
Me?
Aure. Idan na ce na amince na auri makiyayin da ya kubutar da ni daga masu garkuwa da mutane, to fada ba zai iya kashe mijina ba. Doka ce ta Dausayi. Mijin Gimbiya ba a kashe shi a bainar jama'a.
Amma kina tauraruwar sama! Ni kasa ne! Sarki ba zai taba...
Sarki ba zai amince ba, Amal ta katse shi. Amma jama'a za su amince. Idan na fadawa jama'a gaskiya gobe a kasuwa, a gaban kowa, cewa Larabawa za su kwashe su a matsayin bayi, jama'a za su tashi. Kuma Faisal...
Muryar mai gadi daga waje.
Lokaci ya cika! Ku fita!
Amal ta matse hannun Zayd na karshe.
Gobe karfe bakwai a kasuwa. Ki jira ni. Idan na yi nasara, za mu rayu tare. Idan na fadi...
Ba ta karasa ba. Ta fita da gudu.
Washegari. Kasuwa.
Duk Dausayi sun taru. Larabawa sun iso da motoci manya, da sarฦoฦi. Sarki Usman yana zaune a kan karaga, fuska babu annuri. Yarima Faisal tsaye kusa da shi yana murmushi.
A tsakiyar kasuwa, Zayd a gurfane, wuya a bude za a yanke.
Mai shela ya yi shela.
Wannan mutumin ya yi kokarin kashe Gimbiya Amal! Hukuncinsa shine a yanke masa kai!
Jama'a sun yi shiru. Wasu na kuka.
Amal ta fito daga cikin fada. Ta sanya kayan Gimbiya masu tsada. Kowa ya juyo ya kalle ta.
Amal ta daga murya. Murya mai karfi da ba a taba ji irinta ba.
KARYA NE! TA YI IHU.
Duk kasuwa ta yi tsit. Sarki ya mike.
AMAL! KIYI SHIRU!
Ba zan yi shiru ba, Baba! Ta dago takardun da ta samu a kogo. Saboda kai ka sayar da mu! Ka sayar da mutanenka! Ga takardar shaidar ka!
Ta jefa takardun a kasa, iska ta dauke su, jama'a suka fara karantawa.
Tashin hankali ya tashi a kasuwa.
Sarki Usman ya fara rawa. Faisal ya rasa murmushi.
A hankali, Faisal ya fito da wani abu daga mayafinsa. Bindiga karama. Ya nuna Amal.
Idan kin tona asirina, Gimbiya, to ki mutu da sirrin naki.
Ya ja kara.
Amal ta rufe ido.
Bang! Karan bindiga ya tashi a kasuwar Dausayi.
Wayyo! Wanene bindigar ta harba? Shin Amal ta mutu? Ko Zayd ya kubuta?
by Cutie