MASARAUTA : ALKAWARIN GIMBIYA AMAL

JININ SARAUTA

by @khadijaharuna389

πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

bismillahir rahamanirrahim 


Bindigar ba ta harbi Amal ba. Zulaiha ce ta tura Amal, ita ta karbi harbin a kafada!

Jama'a sun firgita. Zayd ya yanke igiyar da ke hannunsa da dutse, ya mike ya kama Faisal.

Faisal ya fadi, bindigar ta fadi. Larabawa sun fara harbin iska.

Sarki Usman ya gane asirinsa ya tonu. Ya yi ihu:

"KU KAMA FAISAL! SHI NE MACI AMANA!"

Amma Faisal ya yi gudu, ya hau doki ya gudu cikin daji.

Zayd ya rungume Amal. Zulaiha na kwance cikin jini.

"Zulaiha!" Amal ta yi kuka.

Zulaiha ta yi murmushi.

"Gimbiya... na cika alkawarina..."

Amal ta dauki Zulaiha, Zayd ya dauke ta suka kai Asibiti.

by Cutie