RAUDAH
๐๐๐๐
bismillahir rahamanirrahim
Washegari, lecture ta fara.
Lecturer ta ce, "Yau ba zamu yi lecture ba. Yau kowa zai fada mana rayuwarsa ta gida. Mu san junanmu."
Duk aji ya yi dariya. Su dai 'ya'yan masu kudi ne.
*Nafisa ta fara.*
Ta tashi jikinta sanye da kaya masu tsada
"A gidanmu, mom ma'aikaciyace. dad kuma yana da kata faran kamfani gidan mu babbane munada masu aiki dayawa.
Ta yi shiru kadan, murmushinta ya bace.
"Amma Mom bata taba zama a gida ba. Kullum meeting. Baba kullum travel. Ni kadai nake zaune a gida mai dakuna 10. Shi ya sa kullum nake zaune cikin kadaici takarasa cikin damuwa
Duk aji ya yi shiru.
*Farhan ya tashi.*
"Ni kuwa, Baba na yana so in zama kamar shi. Yana cewa, 'Farhan, ka karanta Business, ka gaji kamfani.' Amma ni, ina son zama Chef. Kullum idan Mama tana girki a kitchen, ni nake taimaka mata ina yanka albasa. Mama tana cewa, 'Farhan, ka bar kitchen.' Amma ni a kitchen nake jin dadi."
Kowa ya yi dariya kadan.
*Hauwa ta tashi.*
"Ni 'yar Sarki ce. A gidanmu ana girmama ni. Amma ba a taba barin ni in yi komai da kaina ba. Ba a barin ni in wanke plate, ba a barin ni in taimaki Mama. Kullum ma'aikata ne. Wani lokaci ina kishi da 'yan aji na da suke taimaka wa iyayensu. Ni ina son in ji kamar ni ma 'ya ce, ba Sarauniya ba."
Raudah ta ji zuciyarta ta buga. Su ma suna da matsalarsu.
*Raudah ta tashi.*
Duk idanu sun koma kan ta.
Ta tashi a hankali, hijabinta pink yana haskakawa.
"Ni Raudah ce. Daga Mararaba."
Ta shaki iska.
"A gidanmu, ba mu da ma'aikata. Ni ce ma'aikaciyar gidanmu. Kullum ina tashi 5 na safe, in taimaki Mama tana soya kosai. Sai in wanke kayan Baba, in share gida, sannan in zo makaranta. Idan na dawo, ina taimaka wa Mama tana sayar da atamfa."
Ta yi murmushi.
"Gidanmu karami ne. Daki daya. Amma idan Baba ya dawo daga aikin napep, muna zaune tare muna ci abinci tare. Mama tana mana dariya. A gidanmu, babu shiru. Akwai hayaniya, akwai dariya, akwai soyayya. Kudi ba ya nan, amma gida yana nan."
Aji ya yi shiru kamar an kashe wuta.
Nafisa ta ji hawaye na taho mata.
*Sultan ya tashi.*
"Ni Sultan ne. Dan Alhaji Sadiq. Gidanmu a Asokoro. Muna da komai. Ba na taimaka wa kowa. Mama tana da ma'aikata. Ni sarauta aka haife ni. Kuma ni ne na farko a komai a wannan University."
Ya duba Ahmad.
"Ba ni da matsala. Rayuwata ta cika."
*Ahmad ya tashi.*
Ya tashi a hankali. Ya yi shiru na dan lokaci kafin ya yi magana. Ya duba taga.
"Ni Ahmad ne."
"Gidanmu ma babba ne. mahaifina Ministan kudine momma kuma tana da kamfani. Amma tun ina yaro, ni kadai nake. daddy yana Abuja, momma tana Lagos. Ni da ma'aikata muke zaune.
Ya zauna.
Sam sultan ba haka yaso ba yaso aiwa labarinta dariya haka kawai yaji baya sonta ya tsani talaka
A zuciyarsa ya rantse, "Yau ta samu mutunci. Gobe zan nuna mata cewa Royal Haven ba Mararaba ba ne."
Karrarrawar tashi ta yi.
Raudah ta fita a hankali, tana tunanin maganganun Nafisa, Farhan da Hauwa. Ta gane 'ya'yan masu kudi ma suna da kuka a zuciya.
Ahmad ya bita da kallon tausayi har ta futa amma bawanda ya isar yagane make kan fuskarsa
by Cutie