DOCTOR AMANI

DOCTOR AMANI

by @khadijaharuna389

💞💞💞💞💞

bismillahir rahamanirrahim 


Da misalin ƙarfe biyar na yamma, Dr. Amani ta koma gida. Duk da cewa ta gaji sosai bayan aikin da ta yi a asibiti, hankalinta bai kwanta ba. Tun lokacin da aka kawo yarinyar da aka yi wa fyade, take jin wani irin abu a zuciyarta wanda ita kanta ba ta san yadda za ta bayyana shi ba.
Tana zaune a kujerar falonta, ta cire takalmanta ta ajiye gefe, sannan ta jingina da kujera tana kallon silin É—akin.
Fuskarta ta yarinyar ce kawai take gani a ranta.
"Ya Allah, me ya kai wannan yarinya cikin irin wannan mummunan hali? Kuma waye ya aikata mata wannan abin?"
Ta furta a hankali.
Ta tuna yadda aka kawo yarinyar cikin jini, jikinta duk ya yi rauni, har da yadda take ta kuka kafin daga baya ta suma. Abin da ya fi damun Amani shi ne, tun bayan da ta farfaÉ—o na É—an lokaci, yarinyar ta kasa yin magana yadda ya kamata. Kamar akwai wani abu da take tsoro, wani abu da ba ta son ya fito fili.
Amani ta É—auki wayarta ta duba lokaci.
"Ko akwai wani abu da ba mu sani ba?"
Ta sake tambayar kanta.
Ta san akwai yiwuwar yarinyar ta shiga wani yanayi na tsananin firgici, amma duk da haka akwai wani abu a cikin lamarin da ya sa ta kasa samun nutsuwa.
Can sai ƙarar wayarta ta katse tunaninta.
Da ta duba, sai ta ga Fadila ce ke kiranta.
Ta É—aga wayar.
"Hello, Fadila."
"Madam Doctor! Ashe kina gida ne? Na kira ki sau biyu amma ba ki É—aga ba."
Amani ta yi murmushi kaÉ—an.
"Eh, yanzu na dawo. Yau na gaji sosai wallahi."
"To, ina zuwa gidan naku yanzu. Ki shirya min wani abin ci, kar ki ce min babu."
Amani ta yi dariya.
"Ke dai ba kya da hankali. To zo mana."
Bayan kusan mintuna talatin, Fadila ta iso gidan.
Fadila kawar Amani ce tun zamanin jami'a. Suna da kusanci sosai, kuma duk da cewa kowacce tana da harkokinta, ba sa bari dogon lokaci ya wuce ba tare da sun ga juna ba.
Aka buɗe mata gate din gidan ta shigo tana sanye da doguwar riga mai kyau, hannunta ɗauke da ƙaramin jaka.
"Amani!"
Ta kira tana shiga falon.
"Fadila!"
Amani ta amsa tana fitowa daga É—akinta.
Suka rungumi juna cikin farin ciki.
"Yau fa kin yi kyau sosai, amma fuskarki ba ta nuna min farin ciki ba. Me ya faru?"
Fadila ta tambaya tana zama a kan kujera.
Amani ta zauna kusa da ita.
"Babu komai, kawai aikin asibiti ne ya É—an dame ni."
"Ke dai kin fi son asibiti a kan komai. Wani lokaci sai na ji kamar za ki aure shi ne."
Amani ta yi dariya.
"Allah ya kyauta."
Fadila ta yi murmushi sannan ta tambaye ta:
"To, ya aikin yau? Akwai wani sabon case?"
Amani ta É—an yi shiru kafin ta amsa.
"Akwai wata yarinya da aka kawo mana yau. An yi mata fyade."
Murmushin da ke fuskar Fadila ya ɓace.
"Subhanallah! Me kika ce?"
Amani ta gyada kai.
"Wallahi Fadila, abin ya taɓa ni sosai. Yarinyar ba ta wuce shekara ashirin ba a ganina. An kawo ta cikin mummunan hali. Mun yi iya ƙoƙarinmu wajen ceton rayuwarta, amma har yanzu tana cikin kulawa ta musamman."
"Allah ya ba ta lafiya. Amma an san wanda ya yi mata hakan?"
"Ba a sani ba tukuna. Abin da ya fi damuna shi ne, akwai wasu abubuwa da suka sa nake tunanin akwai wani abu a bayan wannan lamarin."
Fadila ta gyara zama.
"Me kike nufi?"
Amani ta sauke numfashi.
"Ban san yadda zan bayyana ba. Amma yadda take firgita duk lokacin da wani ya kusance ta, da yadda take ƙoƙarin yin magana amma sai ta kasa, ya sa nake tunanin akwai wani babban sirri da take ɓoyewa. Ko kuma akwai wani abu da ta gani wanda ya fi abin da ya faru da ita tsanani."
Fadila ta girgiza kai.
"Allah ya kyauta. Amma ki kula sosai, Amani. Irin waɗannan abubuwan ba ƙaramin abu ba ne."
"Na sani. Shi ya sa nake son a bi lamarin a hankali."
Sun ci gaba da hira kan wasu abubuwa, suka yi dariya, suka kuma tuna wasu abubuwan da suka faru da su a jami'a.
Daga baya Fadila ta tashi domin komawa gida.
"Ki huta sosai, Doctor. Kuma ki daina É—aukar duk matsalolin duniya a kanki."
Amani ta yi murmushi.
"In sha Allah."
Bayan Fadila ta tafi, Amani ta koma É—akinta. Ta yi wanka, ta shirya abincin dare, sannan ta kwanta.
Amma duk da haka, bacci ya ƙi ɗaukarta.
Ta juya daga wannan gefe zuwa wancan, tunanin yarinyar bai bar ta ba.
A ƙarshe ta rufe idanunta tana addu'ar Allah ya ba yarinyar lafiya, sannan bacci ya ɗauke ta.
WASHE GARI
Da misalin ƙarfe bakwai na safe, Amani ta tashi daga bacci.
Ta yi wanka, ta yi breakfast, sannan ta shirya cikin wata doguwar rigar aiki mai kyau. Ta ɗauki farin coat ɗinta, ta sa ƙaramin agogo a hannunta, ta ɗauki jakarta sannan ta fito.
Ta isa asibitin nata mai suna ROYAL CARE SPECIALIST HOSPITAL da misalin ƙarfe takwas da rabi.
Da shigarta, ma'aikatan asibitin suka gaishe ta.
"Good morning, Doctor."
"Good morning. How is everything?"
"Everything is fine, ma."
Ta wuce zuwa ofishinta, ta ajiye kayanta, sannan ta kira nurse É—in da ke kula da yarinyar.
"Good morning, Doctor."
"Good morning. Yaya mara lafiyarmu?"
"She's stable, Doctor. Amma har yanzu ba ta cika magana ba."
Amani ta gyada kai.
"Okay. Ina son in gan ta yanzu."
Ta É—auki wasu takardu suka nufi É—akin da aka kwantar da yarinyar.
Da suka shiga, sai suka tarar da ita kwance a kan gadon asibiti. Fuskarta ta nuna gajiya, idanunta sun yi ja saboda yawan kuka.
Amani ta ƙarasa kusa da ita.
"Good morning, dear. How are you feeling today?"
Yarinyar ta É—aga idanunta ta kalli Amani, amma ba ta ce komai ba.
Amani ta ja kujera ta zauna kusa da gadon.
"Ki kwantar da hankalinki. Babu wanda zai cutar da ke a nan. Muna nan ne domin mu taimaka miki."
Yarinyar ta buÉ—e bakinta kamar za ta yi magana, amma sai ta sake yin shiru. Hawaye suka gangaro daga idanunta.
Amani ta miƙa mata tissue.
"Kada ki ji tsoro. Duk abin da ya faru, za mu taimaka miki."
Bayan ta duba lafiyarta, Amani ta fito daga É—akin.
Ta kira babban nurse É—in asibitin ta ce:
"Listen, wannan case ɗin yana buƙatar kulawa ta musamman. Ina so a rubuta duk wani bayani game da yanayin da aka kawo ta da kuma duk abin da aka lura da shi tun lokacin da ta iso."
"Okay, Doctor."
Amani ta ɗan yi shiru sannan ta ƙara da cewa:
"Kuma dole ne mu sanar da 'yan sanda. Wannan ba case ne da za mu iya ɗauka a matsayin magani kawai ba. Ana buƙatar bincike, musamman saboda ba mu san wanda ya aikata wannan laifin ba."
"Yes, Doctor. Zan sanar da management."
Amani ta gyada kai.
"Ina kuma so a tabbatar da cewa an kiyaye duk wata shaida ta likitanci bisa ƙa'ida, kuma yarinyar ba za a matsa mata ta yi magana ba sai lokacin da ta samu nutsuwa."
Ta koma ofishinta tana nazarin takardun mara lafiyar.
Amma a wannan lokacin, wani sabon al'amari ya fara tasowa a wajen asibitin.
A AMEER MANSION
A wani katafaren gida da ke cikin unguwar masu hannu da shuni, wato Ameer Mansion, hankalin kowa ya tashi.
Gidan na dangin Alhaji Suleiman Ameer ne, wani attajiri da ya yi fice wajen harkokin kasuwanci da manyan gine-gine. Gidan kuwa ya fi kama da wani ƙaramin fada.
Manyan ƙofofin ƙarfe ne masu ado da ruwan gwal, akwai manyan motoci a harabar gidan, yayin da masu gadi ke tsaye a wurare daban-daban.
A cikin babban falon gidan kuwa, wata mata ce zaune a kan kujera mai tsada. Fuskarta cike take da damuwa, tana riƙe da wayarta tana yawan duba lokaci.
"Har yanzu ba ku same ta ba?"
Ta tambayi wani mutum da ke tsaye a gabanta.
Mutumin ya sunkuyar da kansa.
"Ba mu same ta ba, Hajiya. Mun bincika wurare da dama, amma babu wanda ya san inda take."
Matar ta miƙe tsaye cikin fushi.
"How is that possible? Tun jiya nake gaya muku ku nemo min ita! Ba zan yarda a ce yarinyar nan ta ɓace haka kawai ba."
A wannan lokacin wani dattijo ya fito daga É—aya daga cikin manyan É—akunan gidan.
"Me ke faruwa a nan tun safe? Me ya sa kuke ta hayaniya?"
Duk suka juya suka kalle shi.
Mutumin ya kasance Alhaji Suleiman Ameer, shugaban gidan.
Matar ta kalle shi.
"Alhaji, har yanzu ba a gano inda yarinyar take ba."
Alhaji Suleiman ya tsaya cak.
"Me kika ce?"
"Na ce har yanzu ba a gan ta ba."
Ya yi shiru na É—an lokaci, sannan ya juya ga mutumin da ke tsaye.
"Ina son a nemo ta. Ko a ina take, ku tabbatar kun gano inda take."
"To, Alhaji."
Ya É—aga hannu alamar su fita.
Da mutanen suka fita, sai ya juya ya kalli matar.
"Kin tabbatar babu wanda ya san abin da ya faru?"
Matar ta yi saurin kallonsa.
"Me kake nufi da wannan tambayar?"
Alhaji Suleiman ya matso kusa da ita, ya rage muryarsa.
"Ina nufin abin da ya faru da ita kafin ta bar gidan nan."
Matar ta yi shiru.
Ta yi ƙoƙarin magana, amma sai ta kasa.
Alhaji Suleiman ya girgiza kai.
"Allah ya sa ba a yi abin da nake tunani ba."
Ya juya ya nufi É—akinsa.
Matar kuwa ta tsaya a wurin tana kallon bayan sa.
A hankali ta zauna, ta É—auki wayarta, ta kira wani lamba.
Da aka É—aga wayar, sai ta ce cikin wata murya mai sanyi:
"Hello. Ina son in san ko an gano inda take."
Sai ta saurara na É—an lokaci.
"Me? A asibiti?"
Idanunta suka zaro.
"Wane asibiti?"
Ta sake saurara, kafin ta furta a hankali:
"Royal Care Specialist Hospital?"
Ta kashe wayar, ta dafe goshinta.
"Ya Allah! Wannan fa ya zama babban matsala."
Amma abin da matar ba ta sani ba shi ne, yarinyar da ake neman ta a Ameer Mansion ita ce wadda ke kwance a gadon asibitin Dr. Amani.
Kuma abin da ya faru da ita ba ƙaramin sirri ba ne.
Wani babban al'amari ne da zai iya girgiza rayuwar gidan Ameer baki É—aya.

💞💕💕💕