JAHILCI YAFI HAUKA
Page 4
Miqewa Mus'ab yake shirin yi, Khalid ya dakatar dashi ta hanyar dafe hannunsa, yana qara marairaicewa kamar mace, "please friend help me, am really starving".
wani murmushi Mus'ab ya saki yana fadin "na aikeka yin shaye-shaye ne?I wouldn't get you anything, uban yan girman kai" ya qarasa fada yana balla mishi hararar wasa, sa'annan ya fice, ya bar qofar bude don ya qara qular da amini, dan-uwa kuma other half din nashi.
Khalid kuwa ya bishi da murmushi don yasan bazai iya komawa office dinsa ba, tunda yace yunwa yake ji, to kuwa tabbas Mus'ab bai da sukuni har sai ya samo mishi abinci, haka suka taso since childhood, kasancewarsu cousin's, tare suka taso, rana guda aka kaisu kindergarten, har suka kammala jami'ah a New York, Dad din Khalid ke dauke da nauyin karatun nasu bai taba banbantasu ba, har sutura iri daya yake saya musu. Tafiyarsu jami'ah zamu iya cewa ya janyo lamura dayawa, ciki kuwa har da lalacewar tarbiyar Khalid, duk da kasancewar Hajiya Maama tsayayya kuma jajirtacciya, mai kuma riqo da addini, tsaye take kan tarbiyar tilon danta, sai dai qaddara zamu ce ko sakaci ya sanyashi fara shaye-shaye, da yawon club, hakan kuwa ya faru ne sanadin wani aboki dan kasar Germany da sukayi mai suna Mateo,tun Mus'ab bai ankara ba har dai ya fahimci amininsa ya kauce hanya, ranar yayi kukan da tunda Mamy ta kawoshi duniya bai taba irinsa ba, yashiga tashin hnkli mara misaltuwa, yayi nasiha, yayi fada amma duk a banza, Khalid yayi nisa baya jin kira, ranar da Daddy ya kawo musu ziyara ya fahimci abinda ke faruwa, ga mamakin Mus'ab, Daddy bai wani tashi hankalinsa ba, illa cewa da yayi Khalid yayi qoqari ya bari kafin Hajiya Maama ta fahimci halin da ya shiga, daga nan bai kuma tayar da zancen ba har suka kammala suka dawo Nigeria.
Ranar da Hajiya Maama ta fahimci halin da tilon danta yake ciki, sai da jininta ya hau, a guje akayi asibiti da ita, da kyar likitoci suka ceto ranta, Khalid ya dinga kuka da magiya yana neman gafararta, da kyar dai ya shawo kanta da alqawarin ya daina, sai dai hakan bata samu ba, tun yana buya har dai lamarin ya girma kowa a family ya gane, Mahaifiyar Mus'ab ta tsani abotarsu, a cewarta Khalid manemin mata ne kuma dan iska zai lalata mata future din danta, don haka bata da burin da ya wuce suyi uwar watsi kowa ya kama gabansa, amma hakan bata samu ba, sakamon Daddy da ya ajiye aiki, acewarsa zai huta tunda yara sun girma, ya barwa Khalid da Mus'ab suke running company.
Mus'ab yana fita Office dinsa ya koma yayi placing order a best restaurant din da ya yarda da hygiene dinsu, kasancewar yana zuwa cin abinci a wajen, babu jimawa aka kawo ya karba, ya koma office din Khalid, wannan karon bai tsaya knocking ba ya shiga, sai dai babu kowa a offlice din sai waya da computer dake bude alamar ba nisa mai office din yayi ba, ajiye abincin yayi ya juya zuwa nashi office din dan kuwa akwai tarin ayyuka gabanshi.
Mus'ab na fita Khalid ya fito daga restroom, yaga giftawar wanda ya shigo ya kuma fahimci wane ne, don haka ya saki murmushin dake qarawa fuskarsa kyau, ya janyo abincin a natse ya fara ci, bai wani ci dayawa ba ya miqe ya nufi fridge din dake cikin office din ya bude, subhnlh!! Wasu irin tsadaddun kwalaben barasa ne jere cikin fridge din sunyi wani irin sanyi, jikinsu ya dauki raba na gaske, kwalba daya ya zaro ya balle marfin ba tare da ya nemi cup ba ya daga kwalban ya kai bakinsa, yasha son ranshi sa'annan ya mayar cikin fridge din, ya juya kmr wanda yasha ruwa.
Khalid tsabar yadda giya ta ratsashi, ko bugar dashi batayi, normal ta zama gareshi tabi jininsa, but sometimes idan ya hadata da wani abun yakan bugu har idan yazo office baya iya aikin komai sai barci, haka lokacin tashi yayi, idan anyi sa'a ta dan sakeshi ya tattara komatsanshi zuwa gda, idan kuwa yana make hka zaiyi ta barci, sai idan anyi sa'a Mus'ab bai tafi ba ya lura da motarsa a parking lot, zai tasheshi da qyar ya mayar dashi gda, lamarin dake jefa Mus'ab cikin tashin hankali da tausayin amininsa, tunda ya lura abin ya zame masa kmr ciwo, muddin bai sha ba haka zaka ganshi ba kuzari kmr wani maras lafiy.
*****************
Gidansu Rumaisa an wayi gari da wani irin tashin hanklin da Abba ya dinga sababih, Innah Asabe tana qara tunzurashi, da qara rura wutar lamura, simply because He was asked to pay for his daughter's registration fee, fadi yake baiga amfanin karatun diya mace ba, don haka He wouldn't pay a dime for that.
Daadah tayi nadamar gaya masa yafi sau tarin shurin masaki, ta gwammaci da tayi shiru da zancen akan mugayen kalaman Abba akan diyarsu, zuciyarta zafi take mata, haqurinta na gab da qarewa a wannan karon, a haka ta fito tsakar gdan nasu inda yake share fes, kafin 2hrs Bilal ya lalata ko ina, yayi ta zubar da ruwa a duk inda yaga dama, ba wanda ya isa ya tanka saboda Innah ta tsaya mishi, ta sauke ajiyar zuciya da mayafinta a hannu da alama unguwa zata fita, Innah ta leqo ta tagar dakinta tana fadin
" ke Hajara ina zakije bayan kin kunna wutar rigima"?
Daadah kamar ba zata ce komai ba, da qyar dai tace "zanje gdanmu ne Innah, amma bazan jima ba".
"ki daiji tsoron Allah kada ki kai karar mijinki, don mu a zamaninmu ko duka miji yake miki haquri zakiyi ba kai qara ba".
Murmushi kawai Daadah tayi a ranta tana jinjina son kai irinna Innah, sai kuma ta gyara mayafinta tana fadin "Innah sai na dawo" daga haka ta saka kai ta bar gidan ba tare da ta jira me Innar zata fada ba.