AMANI
馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒
bismillahir rahamanirrahim
Da misalin karfe takwas na safe, Tariq yana
zaune a falonsa yana duba wasu takardu da suka shafi aikinsa.
Tun bayan abubuwan da suka faru a kwanakin baya, hankalinsa bai gama kwanciya ba. Akwai wasu abubuwa da yake zargi, amma har yanzu bai samu cikakken tabbaci ba.
Wayarsa ta yi kara.
Sadiq ne.
Ya daga wayar.
"Hello, Sadiq."
"Yallabai, ina kwana?"
"Lafiya. Ya binciken?"
Sadiq ya yi shiru na dan lokaci.
"Mun ci gaba da bincike kamar yadda ka umarta. Akwai wasu bayanai da muka samu, amma har yanzu muna kokarin tabbatar da su."
"Madalla. Kada ku yi gaggawa. Ina so duk abin da za mu gabatar ya kasance da cikakken tabbaci."
"An fahimta, Captains."
Tariq ya ajiye takardar da ke hannunsa.
"Ka sani fa, yanzu zan dauki hutun sati daya. Amma ba yana nufin na daina bibiyar wannan al'amari ba. Duk wani sabon abu da kuka samu, ku kira ni."
"To, Captain. Za mu ci gaba da aiki."
"Good. Ka kula da kanka."
Ya katse wayar.
A wannan lokacin Mommy ta shigo falon.
"Tariq, ka gama shirin tafiyar?"
Ya daga kai.
"Eh, Mommy. Komai ya shirya."
"To, ka yi sauri. Salma da Asiya tun da safe suke ta shirye-shirye, Safiyya ma kamar ba za ta gama ba."
Tariq ya yi murmushi.
"Mommy, ni dai na gama. Su kike jira."
Mommy ta girgiza kai tana dariya.
"Ka san halinsu ai."
Ba da jimawa ba, Salma da Asiya suka fito daga dakinsu.
"Yallabai, mun shirya!" Salma ta fada.
Tariq ya kalle su.
"Alhamdulillah. Na fara tunanin sai gobe za ku gama."
Asiya ta yi dariya.
"Ka daina mana. Ai bikin Maryam za mu je, dole mu yi kyau."
Safiyya ta fito daga baya tana gyara mayafinta.
"Ni kam na shirya tun farko. Su ne kawai suke bata lokaci."
Salma ta kalleta.
"Ke kuma wa ya tambaye ki?"
Dukkansu suka yi dariya.
Daddy ya shigo a lokacin.
"To, yaran nan, mu tafi. Kada mu makara."
Tariq ya dauki kayansa, suka fito daga gidan.
Bayan sun isa filin jirgin sama, suka kammala dukkan shirye-shiryen tafiya.
Tariq yana tafiya a hankali tare da Daddy, yayin da Mommy da yaran suke ta hira a bayansu.
Salma tana magana da Asiya game da irin kayan da za su saka a bikin, Safiyya kuwa ta shagaltu da daukar hotuna.
Da suka shiga jirgi, kowa ya samu wurin zama.
Tariq ya zauna kusa da tagar jirgin.
Ya kunna wayarsa na dan lokaci, sai wani sako daga Sadiq ya shigo.
Sadiq: "Captain, muna ci gaba da aiki. Da zarar mun samu karin tabbaci za mu tuntube ka."
Ya amsa a takaice.
Tariq: "To. Ku kula da kanku."
Ya kashe wayar ya jingina da kujerarsa.
Daddy ya kalle shi.
"Tariq, ina fatan za ka yi amfani da wannan hutun ka huta sosai."
Tariq ya juya gare shi.
"In sha Allah, Daddy."
"Ka daina saka kanka cikin damuwa a kowane lokaci. Aiki yana da muhimmanci, amma lafiya ma tana da muhimmanci."
"Na sani, Daddy."
Jirgin ya fara tafiya, suka baro garin.
Ba wanda ya san irin abubuwan da wannan tafiyar za ta haifar a rayuwarsu.
AMANI
Da misalin karfe tara na safe, Amani ta fito daga dakinta sanye da wata doguwar riga mai kyau.
Daddy yana zaune a falo tare da Mommy, ana shirya masa kayan tafiya.
"Assalamu alaikum," Amani ta fada tana karasowa.
"Wa alaikumus salam, Amani ta," Daddy ya amsa.
Ta zauna kusa da shi.
"Daddy, komai ya shirya?"
"Eh, komai ya shirya. Ina fatan ba za ki manta da ni ba idan na tafi."
Amani ta yi dariya.
"Ni kuma in manta da kai? Ai kai ne kake yawan mantawa da mu idan ka tafi."
Daddy ya yi murmushi.
Mommy ta shiga maganar.
"Ke dai ki daina yi masa surutu. Yana da tafiya mai nisa."
Amani ta juya gare ta.
"To Mommy, ai wasa nake."
Ba da jimawa ba suka shiga mota suka nufi filin jirgin sama.
A hanya, Amani tana ta yi wa Daddy wasu tambayoyi game da tafiyar.
"Yaushe za ka dawo?"
"In sha Allah, da zarar na kammala abin da ya kai ni."
"To, Allah ya dawo da kai lafiya."
"Amin, Amani ta."
Da suka isa filin jirgin sama, suka raka Daddy har inda ya kamata su yi sallama.
Daddy ya rungumi Amani.
"Ki kula da kanki. Kada ki manta da hutawa. Na san kina son aikinki, amma kada ki manta cewa kina da rayuwa a wajen asibiti."
Amani ta yi murmushi.
"To, Daddy."
Ya juya ga Mommy.
"Ki kula da ita."
Mommy ta amsa da murmushi.
"Ka kwantar da hankalinka."
Bayan sun yi sallama, Daddy ya wuce.
Amani ta tsaya tana kallonsa har sai da ya bace daga ganinta.
"Allah ya dawo da shi lafiya," ta fada a hankali.
"Amin," Mommy ta amsa.
Suka nufi motarsu.
A lokacin ne Mommy ta tuna da wani abu.
"Amani, na manta ban gaya miki ba."
Amani ta kalleta.
"Me ne kuma Mommy?"
"Za mu je Kaduna."
Amani ta dan bude ido.
"Kaduna? Yaushe?"
"Gobe za mu fara shirin tafiya. Za mu halarci bikin Maryam da Nabil."
Amani ta yi murmushi.
"Maryam 'yar yayarki?"
"Eh, ita din."
"Subhanallah! Ashe bikin ya yi kusa haka?"
"Eh. An shirya komai. Kuma ina son ki kasance tare da ni a wannan karon."
Amani ta gyara zamanta.
"To, shikenan. Amma Mommy, tsawon kwanaki nawa za mu yi?"
"Ba zan iya cewa ga adadin kwanakin ba tukuna. Amma za mu samu lokacin zama tare da 'yan uwa."
Amani ta yi murmushi.
"Allah ya kai mu lafiya."
"Amin."
FAMILY HOUSE
Babban family house ne da ya kasance cibiyar wannan babban iyali tun shekaru da dama.
Gidan yana da bangarori biyu.
Bangare daya na Nanne ne, kakar Tariq, yayin da dayan bangaren yake na Inna, kakar Amani.
Duk da kasancewar gidan daya, kowace tana da nata bangaren, nata falon da kuma mutanen da suka fi zama tare da ita.
Rashin jituwar da ta dade tana tsakaninsu ya sa iyalan biyu suka kasance kamar ba su da alaka.
Ba wai kawai Nanne da Inna ba ne ba sa shiri. Har ma da wasu daga cikin 'ya'yansu da jikokinsu.
Kowanne bangare yana rayuwa ne da nasa mutanen, ba tare da damuwa da abin da ke faruwa a dayan bangaren ba.
A sakamakon haka, yawancin jikokin gidan ba su san juna sosai ba.
Wasu ma sun san sunayen juna ne kawai.
Alhaji Bashir kuwa, wanda yake da matsayi mai girma a cikin iyalin, ya dade yana bakin kokarin hada kan gidan.
Ya gaji da ganin yadda rashin jituwar manyan gidan yake shafar zuriyarsu.
Shi ya sa ya yanke wata shawara da ta ba mutane da dama mamaki.
Ya kuduri aniyar hada wasu daga cikin jikokinsa aure.
A ganinsa, wannan zai zama wata hanya ta sake hada zumuncin iyalin.
Kuma saboda matsayinsa da kuma yadda kowa yake girmama shi, babu wanda ya isa ya yi masa musu kai tsaye.
Da suka isa Kaduna, Amani da Mommy suka nufi bangaren Inna.
Tun daga kofar gidan za ka fahimci cewa ana wani babban biki.
An kawata wuraren shiga da fitilu masu kyau, an kafa rumfuna, yayin da wasu ma'aikata ke ta kai-komo suna kammala shirye-shiryen bikin.
Amani ta sauka daga motar tana kallon gidan.
"Mommy, gidan nan ya fi yadda nake tsammani girma."
Mommy ta yi murmushi.
"Kin dai ga gidan kakanninku. Gidan da muka taso ."
Amani ta kalli wasu mutane da ke tafiya a dayan bangaren gidan.
"Mommy, su ma 'yan gidan ne?"
Mommy ta bi inda take kallo.
"Eh. Wannan dayan bangaren gidan ne."
"Me ya sa bakwa shiri dasune?"
Mommy ta yi shiru na dan lokaci.
"Ina, Amani. Wasu abubuwa na manya ne da ba za ki fahimce su sosai ba yanzu."
Amani ta gyada kai.
Suka shiga bangaren Inna.
Da Inna ta ga Amani, sai ta bude hannayenta.
"Amana ta! Zo nan, bari in rungume ki."
Amani ta karasa da sauri ta rungume ta.
"Inna! Na yi kewarki."
Inna ta shafa kanta.
"Allah ya raya min ke. Kin kara girma, kin kara kyau."
Amani ta yi murmushi.
"Na gode, Inna."
Mommy ta gaishe da Inna, suka zauna suna tattauna batutuwa
Amani kuwa ta yi sallama da wasu daga cikin 'yan uwanta da ta dade ba ta gani ba.
Bayan dan lokaci, ta nufi daki domin ta huta.
A daya bangaren gidan kuwa, Tariq da iyalinsa sun iso.
Nanne tana zaune a babban falo lokacin da aka sanar da ita cewa sun iso.
"Ku shigo da su," ta fada cikin farin ciki.
Tariq ya shiga tare da Mommy, Daddy da sauran 'yan uwansa.
Da Nanne ta gan shi, sai ta yi murmushi.
"Jikana! Ashe ka zo."
Tariq ya sunkuya ya gaishe ta.
"Ina wuni, Nanne?"
"Lafiya lau.
Ta kalli fuskarsa.
"Amma ka yi kama da wanda aikinsa ya hana shi bacci."
Tariq ya yi murmushi.
"Aiki ne kawai, Nanne."
"To, nan za ka huta. Kada ka damu da komai."
Bayan sun dan zauna, Salma da Asiya suka tashi tare da Safiyya domin su je su ga sauran 'yan uwa.
Tariq kuwa ya fito daga falon domin neman iska.
Yana tafiya a cikin tsakar gidan ne sai ya ji wasu suna magana game da shirye-shiryen bikin.
Ya tsaya ya duba wayarsa.
A wannan lokacin ne ya daga kai.
Sai ga wata fuska da ya sani.
Ya tsaya cak.
Amani ce.
Ita ma tana tafiya ne daga dayan bangaren gidan, tana rike da wayarta.
Da ta daga kai ta gan shi, sai ta tsaya.
Idanuwansu suka hadu.
Amani ta dan bude ido.
Tariq?
Shi ma ya yi mamaki.
Ya dade yana kallonta kafin ya dauke kai .
"Assalamu alaikum,
Tariq ya mayar da sallama.
"Wa alaikumus salam."
Ta yi dan murmushi.
"Ban yi tsammanin zan sake ganin ka a nan ba."
Tariq ya gyara tsayuwarsa.
"Ni ma haka. Ashe ke ma kina cikin wannan iyalin?"
Amani ta yi murmushi.
"Eh. Kai fa?"
"Ni ma haka."
Suka yi shiru na dan lokaci.
Tariq ya kalleta.
"Ya aikin?"
"Lafiya kalau."
"Madalla."
Amani ta gyada kai.
"To, sai anjima."
Tariq ya amsa.
"Sai anjima, Doctor."
Amani ta wuce.
Shi kuma ya tsaya yana kallonta na dan lokaci kafin ya girgiza kai da murmushi ya ci gaba da tafiyarsa.
Bai taba tunanin zai sake haduwa da ita cikin irin wannan yanayi ba.
SHAGALIN BIKI
Da dare, an fara gudanar da shagalin bikin.
An kawata gidan da fitilu masu kyau, ana kunna wakokin biki, yayin da mutane ke ta shiga da fita.
Matan gidan sun yi kwalliya iri-iri, maza kuma sun yi ado na musamman.
A bangaren Nanne, Tariq yana zaune tare da wasu daga cikin 'yan uwansa.
Salma da Asiya sun shagaltu da daukar hotuna, Safiyya kuwa tana ta hira da wasu 'yan uwansu.
Tariq ya zauna yana duba wayarsa.
Sadiq ya kira.
Ya daga wayar.
"Hello."
"Yallabai, ya Kaduna?"
"Lafiya. Yaya abubuwa?"
"Muna ci gaba. Akwai wani sabon abu da muka samu, amma ina so mu tabbatar da wasu bayanai kafin mu sanar da kai."
Tariq ya gyara zamansa.
"To, ku ci gaba. Kada ku bar wani abu a baya."
"An gama, Yallabai."
Ya katse wayar.
A dayan bangaren gidan kuwa, Amani tana zaune tare da Mommy da wasu matan iyali.
Tana cikin wata doguwar riga mai kyau, ta yi kwalliya mai sauki wadda ta dace da ita.
Ana hira, ana dariya, wasu kuma suna ta yaba wa yadda aka shirya bikin.
Amani tana saurare ne sai ta ji an ambaci sunan Tariq.
"Wallahi Tariq ya girma. Tun yana karami nake ganinsa," wata mata ta fada.
Wata ta amsa.
"Eh, kuma yanzu ya zama babban mutum."
Amani ba ta yi magana ba.
Amma sai ta tuna da haduwarsu ta ranar.
Ashe mutumin nan dan gidan nan ne?
Ta yi dan murmushi ita kadai.
Mommy ta lura.
"Aman, me ke baki dariya?"
Amani ta dawo daga tunaninta.
"Babu komai, Mommy."
Mommy ta kalleta da dan murmushi.
"To, shikenan."
Amani ta dauki kofin ruwan da ke gabanta ta sha.
Amma ba zato ba tsammani sai tunaninta ya koma ga yadda Tariq ya tsaya yana kallonta da mamaki lokacin da suka sake haduwa.
Mutumin nan dai...
Ta girgiza kai kadan.
Ta mayar da hankalinta kan hirar da ake yi.
Ba wani abu ba ne a gare ta. Kawai mamakin haduwa da wanda ta sani a wani wuri ne.
Ko kuwa haka take son ta dauka.
A daidai lokacin da shagalin bikin yake gudana, Alhaji Bashir yana zaune a wani daki tare da wasu manyan iyali.
An kawo masa shayi, ya karba ya ajiye a gabansa.
Ya kalli dattawan da suke tare da shi.
"Yanzu dai ina ganin lokaci ya yi da za mu fara magana a kan abin da muka dade muna shiryawa."
Daya daga cikinsu ya gyada kai.
"Alhaji, muna sauraronka."
Alhaji Bashir ya yi shiru na dan lokaci.
"Na dade ina kallon yadda wannan gida yake rayuwa. Gida daya, iyali daya, amma zuciyoyin mutane sun rabu gida-gida."
Ya kalli daya daga cikin dattawan.
"Ba na son in bar wannan duniya ba tare da na ga an hada wannan iyali ba."
Dattijon ya amsa.
"Allah ya ba ka tsawon rai, Alhaji."
Alhaji Bashir ya gyada kai.
"Abin da na yanke shawara shi ne, za mu hada wasu daga cikin jikokinmu aure. Ina son a sake gina zumuncin da ya lalace."
Wani daga cikin dattawan ya yi magana.
"Amma Alhaji, kana ganin yaran za su amince?"
Alhaji Bashir ya kalle shi.
"Ba na son a dauki wannan a matsayin wasa. Na san abin da nake yi. Kuma ina son a yi komai cikin mutunci da bin ka'ida."
Ya yi shiru na dan lokaci.
"Lokaci zai zo da kowa zai fahimci dalilin wannan shawarar."
Da dare ya yi, Amani ta koma dakinta.
Ta cire kayanta na shagali ta zauna a gefen gado.
Ta dauki wayarta tana duba wasu sakonni.
Amma duk da gajiyar ranar, wani lokaci tunaninta yana komawa ga abubuwan da suka faru.
Ta tuna da mamakin da ta yi lokacin da ta sake ganin Tariq.
Ta yi murmushi kadan.
Ta ajiye wayarta ta kwanta.
A dayan bangaren gidan kuwa, Tariq yana zaune yana magana da Daddy.
"Ka ji dadin bikin?" Daddy ya tambaye shi.
"Eh, Daddy. Alhamdulillah."
"To, ka yi kokarin ka dan huta. Ka san hutun sati daya kawai aka ba ka."
Tariq ya yi murmushi.
"In sha Allah."
Amma a lokacin da ya shiga dakinsa, ya tuna da haduwarsa da Amani.
Ya yi dan murmushi.
"Doctor Amani..."
Ya girgiza kai ya kashe fitilar dakin.
Bai san dalilin da ya sa ya tuna da ita ba, amma ya bar tunanin ya wuce.
A wannan daren, mutane da dama sun kwanta suna tunanin irin abubuwan da za su faru a bikin.
Amani ba ta san cewa Alhaji Bashir yana da wani babban shiri da ya shafe ta ba.
Tariq kuma bai san cewa hutun da ya zo yi a Kaduna zai iya sauya masa rayuwa ba.
Nanne da Inna kuwa, kowacce tana cikin bangarenta, ba tare da sanin cewa shawarar Alhaji Bashir za ta iya sake tayar da tsohuwar rashin jituwarsu ba.
Amma abu daya ya tabbata.
Wannan bikin ba bikin Maryam da Nabil kawai ba ne.
Shi ne farkon wasu sauye-sauye da za su sauya rayuwar wannan iyali gaba daya.
by Cutie