ZAYD ARMAAN

THREE DIFFERENT WORLDS

by @jiddaahbarkum

ZAYD ARMAAN

CHAPTER 128

THREE DIFFERENT WORLDS.

JIDDAAH BARKUM

———-

Seeyama ta tsaya a gaban babban madubin da ke cikin ɗakinta, idanunta a kan hoton fuskarta da ke bayyane a cikin madubin. Amma a zahiri, ba fuskarta take kallo ba. Tunaninta ya yi nisa sosai. Tana kallon kanta ne kamar wadda ta fara ganin wata baƙuwar mutum a gabanta. Wata mace da ta san yadda ake ado, yadda ake jan hankali, yadda ake samun abin da take so, amma ba ta taɓa tsayawa ta tambayi kanta ko tana living her life the right way ba. Ta tuna da yadda ta taso. Seeyama ta kasance yarinya ce da aka sangarta matuƙa. Tun tana ƙarama, ba a saba ce mata a'a ba. Duk abin da ta nuna tana so, ana ƙoƙarin samo mata. Idan ta yi fushi, ana lallashinta. Idan ta yi kuka, ana gaggawar biya mata buƙatarta. Idan ta yi kuskure, ana samun wanda zai kare ta ko ya rage masa laifi. Ta girma cikin jin cewa komai yana iya zama nata idan ta nace. Ba ta saba da ƙin yarda ba. Ba ta saba da jiran lokaci ba. Kuma ba ta taɓa koyon yadda za ta karɓi rashin samun abin da take so ba. A hankali, wannan sangarta ta zama wani ɓangare na halinta. Ta fara ɗaukar son ranta a matsayin abu mafi muhimmanci, ba tare da tunanin how her actions affected other people ba. Amma… Yanzu da take tsaye a gaban madubin, wasu tambayoyi suka fara tasowa a ranta. Yaushe ne na taɓa zama na tambayi kaina me nake yi da rayuwata? Me na sani game da Allah? Ta runtse idanunta na ɗan lokaci. Ta san akwai Allah. Ta san ana yin sallah, ana azumi, ana karatun Alƙur'ani. Ta san waɗannan abubuwa tun tana ƙarama. Amma shin ta taɓa ƙoƙarin fahimtar addininta da gaske? Ta taɓa zama ta nemi sanin Allah, ta koyi abin da yake so daga gare ta, ko ta fahimci dalilin da ya sa aka halicce ta? A'a. Ta fi damuwa da kyawunta, kayan sawa, kuɗi, jin daɗi da kuma yadda mutane suke kallonta. Ta san inda za ta je idan tana son sayen sabon kaya, ta san yadda za ta samu abin da take so daga Mommy, amma ba ta san where to even begin idan tana son koyon addininta ba. Abin ya ɗaure mata kai. Ta tuna da yadda ta kasance tana ganin kanta a matsayin mace mai komai. Kyakkyawar rayuwa, kuɗi, kyau, gata… ta yi tunanin waɗannan abubuwa ne za su cika rayuwarta. Amma me ya faru da ita? Ta shiga cikin abubuwan da ba ta ma san yadda za ta fita daga cikinsu ba. Ta cutar da wanda bai cancanci cutarwa ba. Ta bari son zuciya ta mamaye zuciyarta. Ta yi ƙoƙarin mallakar soyayyar mutum ta hanyar da ba ta dace ba, har ta kai ga jefa lafiyarsa cikin haɗari. Sai ta tuna da bokan. Tunanin abin da ya faru a can ya sa ta buɗe idanunta a hankali. Har yanzu tana jin kalamansa a kunnenta, amma abin da ya fi tsaya mata a rai shi ne yadda ta yi satar fita taje wajen wani katon mashurki A karo na farko, ta fara fahimtar cewa akwai abubuwan da kuɗi ba zai iya saya ba. Akwai matsalolin da babu wanda zai iya warware mata su sai da yardar Allah. Hannunta ya tashi a hankali zuwa kirjinta, ta ɗora shi a kan zuciyarta. "Ya Allah…" Ta furta kalmar a hankali, kusan kamar tana koyon yadda ake kiran ta da gaske. Hawaye suka taru a idanunta. "Shin… zan iya canjawa na dawo wata daban?" Ta tambayi kanta, tana kallon fuskarta a madubi. A wannan karon, ba ta ga kyakkyawar mace mai tsada a gabanta ba. Ta ga mace mai kura-kurai, wadda ta daɗe tana gudun confronting the person she had become. Kuma wataƙila, a yau ne ta fara son sanin yadda za ta gyara abin da ta lalata. Ta sauke numfashi, ta juya daga gaban madubin zuwa kan ƙaramar teburin da ke gefen gadonta. Wayarta na nan, amma hannunta bai nufi gare ta ba. Maimakon haka, ta zauna a gefen gadon, ta yi shiru na ɗan lokaci. Ba ta san duk abin da ya kamata ta yi ba. Ba ta san dukkan addu'o'in da za ta karanta ba. Amma ta san abu ɗaya: ba ta son komawa inda ta fito. A hankali ta miƙe tsaye. Wataƙila lokaci ya yi da za ta fara koyon abin da ya kamata ta koya tun tana ƙarama.

Zayd bai bar Raihana ta tashi daga jikinsa ba sai da ya tabbatar ta ci abincin da ke gabanta sosai. Duk lokacin da ta ce ta ƙoshi, sai ya ɗan kalli plate ɗin, ya sake miƙa mata wani ɗan abin ci. "Just one more bite, sweetheart." Raihana ta girgiza kai tana tura Baki, amma shi ya ɗan ɗaga gira. "Are you sure? Kin gama kuwa?" Ta gyada masa kai, tana mai nuna masa plate ɗin da ya kusa zama babu komai. Sai ya yi murmushi, ya ajiye cokalin. "Good girl. At least yanzu na tabbatar kin ci abinci sosai." Ya ɗauki cup ɗin tea ɗin ya miƙa mata. Ta karɓa ta sha kaɗan kafin ta mayar masa. Bayan ya tabbatar ta ƙoshi, sai ya gyara mata gashinta da ya basu a baya, ya ɗa share wani abun plantain da ya makale a gefen bakinta. "Now, I can finally relax." Raihana ta yi murmushi kaɗan, tana kallonsa. Kaima Kaci toh Sai ya dan langwabe Kai waye zai bani ni Ta tsaya tana kallonsa sai kuma a hankali ta Mika hannu ta dauki spoon din da ya gama bata ta fara bashi zayd ya bude baki zai karba idanunshi Akan Fuskarta amma ita taqi kallonsa Haka ta dinga basa Tana avoiding eye contact da shi har saida yace shima ya koshi A hankali ya miƙe tsaye, sannan ya sake sunkuyowa ya ɗauke ta a hannunsa kamar ya dauki wata jaririya Ta yi saurin kama wuyansa, tana kallonsa da Baki a ture. "Again?" ta tambaya a hankali. "Yes, again. What did you expect?" Ya amsa yana murmushi, kafin ya nufi kan gadon ya zaunar da ita a hankali. Ya fara da kashe babban fitilar ɗakin, sannan ya ɗan buɗe curtains ɗin window ɗin. Hasken waje kaɗan ya shigo cikin ɗakin, yana reflecting a wasu sassan bangon da kayan ɗakin. Sai ya kunna plasma ɗin dake bangon, ya zaɓi wani romantic movie mai suna The Notebook. Bayan ya tabbatar komai ya yi daidai, sai ya dawo inda Raihana take. Ya hau gadon, ya jingina bayansa da headboard ɗin, sannan ya miƙa hannunsa gare ta. "Come here, my love." Raihana ta matsa kusa da shi, shi kuma ya ɗago ta a hankali ya ɗora ta a jikinsa, har kanta ya sauka a kan kirjinsa. Ya kankame ta da hannayensa biyu, ɗaya yana riƙe da ita a kafaɗa, ɗayan kuma sai ya zame shi yana shafa bayanta a hankali. Ya sunkuyo ya yi kissing tsakiyar kanta. Raihana ta sauke ajiyar zuciya a hankali, kafin ta ɗago hannayenta ta rungume kugunsa. Ta lumshe idanuwanta tana jin daɗin yadda yake riƙe da ita. Zayd ya yi murmushi, ya sake yi mata kissing a tsakiyar kanta. "Habibti…" "Uhmm?" ta amsa a hankali. "Kin ga yadda na kunna miki plasma ɗin?" A hankali ta ɗan ɗago kanta ta kalli wajen plasma ɗin, sannan ta sake maida kanta kirjinsa. "Hmm." Zayd ya yi murmushi. "I've watched this movie so many times, but I always told myself that one day, In Shaa Allah, zan sake kallonsa tare da matata." Raihana ta lumshe idanunta, tana jin wani irin daɗi a ranta. Ta sake kwantar da kanta a kirjinsa, murmushi yana bayyana a fuskarta. Zayd ya lura da murmushin nata, sai ya ci gaba da magana cikin wata murya mai laushi. "You know something, my Raii? There is something I've wanted to tell you for a very long time." Ta ɗan motsa kanta a kirjinsa, tana sauraron sa. "Do you know how much I love you?" Raihana ba ta amsa ba, sai dai ta ƙara matsa jikinta kusa da nasa. Zayd ya shafa bayanta a hankali. "I think I've loved you much longer than I even realised. Right from day one, when you stopped my convoy…" Ya yi murmushi yana kallon wani wuri kamar yana sake ganin wannan ranar a gabansa. "Kin san me ya sa na gan ki daban a ranar?" Raihana ta ɗan ɗago kanta tana kallonsa, sannan ta gyada kai a hankali. Sai ya yi murmushi. "Every woman I had come across in a situation like that would always try to do something special to get my attention. Some would try to impress me, some would try to get close, and others would simply look for a reason to attract me." Ya ɗan dakata, kafin ya ci gaba. "But you? You did none of that." Ya yi ƙaramar dariya. "You fought me. You accused me. You stood there looking at me like I was the one who had committed a crime." Raihana ta ɗan yi murmushi tana sauraron sa. "Har kika ce…" Ya ɗan tsaya, yana kwaikwayon yanayin yadda ta faɗi maganar a ranar. "Ni kuma ina jiran boss ɗinka ya fito." Zayd ya yi dariya a hankali har hakoransa suka fito Raihana ta tura baki, ta ɓoye fuskarta a kirjinsa saboda kunya. "Stop it…" Amma shi sai ya ƙara dariya, yana shafa bayanta. "I still remember that day so clearly. You had no idea who you were talking to, and honestly, I don't think you even cared." Ta ɗaga kanta kaɗan, sannan ta faɗa cikin sanyin murya. "I didn't know…" Zayd ya yi shiru na ɗan lokaci. Raihana ta ɗan ƙara rungume shi, sannan ta ƙara da wata murya mai laushi. "I didn't know Cewa soulmate dina ne a ciki." Zayd ya tsaya cak. Ya kalli tsakiyar kanta, murmushi mai zurfi yana bayyana a fuskarsa. Kalaman nata sun taɓa wani wuri a zuciyarsa da ba ya iya bayyana wa. A hankali ya saki ɗan murmushi, sannan ya ɗago ta daga kirjinsa yana son ya kalleta. Amma Raihana ta ƙi buɗe idanunta. Ta san yana son ya kalle ta, kuma hakan ya ƙara sanya ta jin kunya. "Habibti…" Ta yi shiru. "Look at me, sweetheart." Ta make kafada a hankali. Zayd ya yi murmushi, sannan ya matsa kusa da ita. A hankali ya haɗe goshinsa da nata, yana kallon fuskarta da idanunta har yanzu suke a rufe. "Habibti…" "Hmm?" "Kin amince nine soulmate ɗinki?" Raihana ta yi ƙaramin murmushi, sannan ta gyada kai ba tare da ta buɗe idanunta ba. Zayd ya lumshe nasa idanun na ɗan lokaci, yana jin yadda zuciyarsa ta cika da wani irin farin ciki. Ya sake manna kissing a goshinta. "That's my girl." Sannan ya mayar da ita a kirjinsa, ya ƙara rungumeta sosai, yana shafa bayanta a hankali yayin da fim ɗin ke ci gaba da gudana a plasma ɗin. Amma a zahiri, babu wanda ya ke sha'awar kallon fim ɗin a wannan lokacin. Zayd yana jin daɗin kasancewarta a jikinsa, ita kuma tana jin daɗin sanin cewa mutumin da ta taɓa tsayawa a gabansa tana ƙalubalantarsa, yanzu shi ne ya zama mafakarta. And neither of them wanted that moment to end.

Motar da Alhaji ya aiko ta tsaya a gaban wani katafaren guest house mai matuƙar kyau. Direban ya fito da sauri, ya zagaya ya buɗe mata ƙofar baya. "Madam, mun iso." Bintu ta gyara zaman abayar da ke jikinta, sannan ta dauki handbag din ta ta sauko daga motar tana kallon ginin da ke gabanta. "Wannan ne?" "Yes, madam. Alhaji yana ciki." Ta gyada kai, ta bi bayansa yayin da yake yi mata jagora zuwa cikin ginin. Da suka shiga, Bintu ta fara kallon-kallo. Gaskiya ba ƙaramin kuɗi aka zuba a wannan wuri ba. Komai ya kasance luxurious, daga irin tiles ɗin da ke shimfiɗe a ƙasa zuwa manyan chandeliers ɗin da suka rataye a saman falon. Manyan kujeru ne masu tsada, kayan ado na musamman, manyan hotuna da kuma wani irin ƙamshi da ya cika wajen. Komai ya yi kyau sosai, har ma ya so ya yi yawa. Kamar dai ba da kuɗin da ake fafutuka wajen nema aka hada wajen ba Bintu ta ɗan buɗe baki tana kallon wani babban chandelier da ke saman falon. Wow! Ta furta a ranta. A haka ta ci gaba da bin direban har suka isa babban falon da ke cikin guest house ɗin. A can ne ta hango wasu maza biyu zaune a kan manyan kujerun alfarma. Da farko ta yi tsammanin mutum ɗaya ne kawai za ta samu, amma ganin mutumin da ke gefensa ya sa ta ɗan rage saurin tafiyarta. Alhaji sabo yana zaune a kan kujera mai faɗi, wani katon mutum mai duhun fata ne, jikinsa a cike, musamman cikinsa wanda ya fito sosai a gaban rigar babbar farar shaddar da yake sanye da ita. Yana da wata babbar fuska mai fadi, idanuwansa ƙanana ne jajaye ga kuma gemunsa da ya cika gefen fuskarsa. Abokinsa kuwa bai sha bamban da shi sosai ba. Shi ma babban mutum ne, baƙi sosai, mai katon ciki da ya yi kama da wanda ya sha zama yana cin abinci ba tare da wani motsa jiki ba. Yana sanye da wata shaddar da ta matse a jikinsa, ta fito da uban cikinsa kamar an kifa kwarya yayin da wani katon gold watch ya yi masa ado a hannu. Bintu ta tsaya na ɗan daƙiƙa tana kallonsu. Na shiga uku !. Gaskiya ba irin mutanen da ta yi tsammanin za ta tarar ba ne. Idan da kawai ta gan su a wani wuri, da wuya ta yi tunanin za ta iya zama a gabansu tana murmushi haka. Amma kuɗi… Kuɗi da son duniya sun kawo ta nan. Ta haɗiye yawu, ta gyara fuskar ta sannan ta ɗora murmushin dole a fuskarta. Alhaji ya hango ta, nan take ya washe baki cikin farin ciki. "Ahhh! Bintu! My beautiful girl!" Ya miƙe tsaye yana buɗe hannayensa. "Welcome, welcome! Please, come in. I've been waiting for you." Bintu ta matsa kusa da su, tana murmushi kamar komai yana mata daɗi. "Good afternoon, Alhaji." Alhaji ya dan matso ya mata wani side hug snn ya sake ta yana kallonta "Afternoon, my dear. How are you? Hope the journey wasn't stressful?" "I'm fine, thank you." "That's good. That's very good." Ya nuna mata wata kujera da ke gabansa. "Please, have your seat." Bintu ta zauna a hankali, tana ƙoƙarin kada ta nuna irin rashin jin daɗin da take ji a ranta. Ta sake kallon falon, sannan ta dawo da idanunta kansu. Alhaji Sabo ya juya ga abokinsa. "By the way, let me introduce you to my friend. This is Alhaji Kabiru. One of my closest friends." Kabiru ya gyara zaman sa, sannan ya kalli Bintu daga sama har ƙasa. "Ahhh, so this is the beautiful Bintu we've been hearing about?" Ya yi murmushi, yana kallonta da wani irin kallo da ya sa Bintu ta ɗan motsa a kujerarta. Alhaji Sabo ya yi dariya. "Yes, this is her. Bintu, meet my friend." Bintu ta ɗan gyada kai. "Nice to meet you, sir." Kabiru ya yi murmushi mai faɗi, sannan ya ɗan matsa gaba a kujerarsa. "Honestly, Alhaji, ka samu kayan marmari." Ya ce yana kallon Bintu. "Gaskiya kana ganin komai nata luntsum-luntsum, kamar burodi na nutso a shayi." Ya fashe da dariya, yana kallon Alhaji Sabo "Amma dai gaskiya, kar a yi sabgar nan babu ni." Alhaji ya ƙara dariya, ya girgiza kai. "Kabiru, you and your mouth!" Bintu kuwa ta tsaya tana kallonsu. Murmushin da ke fuskarta bai gushe ba, amma a cikin ranta tana jin kamar za ta yi amai. Ta haɗiye yawu, ta juya idanunta zuwa kan wata katuwar flower vase da ke gefen falon, tana ƙoƙarin kau da tunaninta daga irin kalaman da ta ji. Ya Allah, me ya kawo ni nan? Ta tambayi kanta a zuciyarta. Amma sai ta sake kallon kayan alatu da ke kewaye da ita, ta tuna da yadda Mommy ta yi mata magana kafin ta fito. Ta gyara zama, ta sake ɗora murmushin dole a fuskarta. Alhaji kuwa bai lura da komai ba. Ya ɗauka Bintu tana jin daɗin hirar ne, saboda har yanzu tana zaune cikin nutsuwa, ba ta nuna musu wani abu ba. "Bintu, would you like something to drink? Juice ko ruwa, anything?" Ta ɗan girgiza kai. "I'm fine, thank you." "Are you sure? You can have anything you want." "I'm okay, Alhaji." Ya gyada kai, sannan ya sake kallon abokinsa. "Let's give her some time to settle down first." Ya fada da yarabanci Kabiru ya ɗan gyada kai, amma idanunsa har yanzu suna kan Bintu yana bin ta da wani mayen kallo Ita kuwa ta sauke nata idanun zuwa kan hannayenta da ke kan cinyarta, tana jiran kawai ta ga yadda wannan ziyara za ta ƙare. Bayan kamar 5 minutes Alhaji Sabo ya ɗan gyara zaman shaddarsa, sannan ya miƙe tsaye yana kallon abokinsa. "Toh, bari mu ɗan gaisa da ita a ciki ko? Ko zaka tafi ne, ko kuwa zaka jira?" Kabiru ya fashe da dariya, ya jingina bayansa da kujerar yana kallon Alhaji Sabo "Na tafi? Ina zan je kuma? Ai ina nan, ina jiranka." Ya sake yin wata dariya, sannan ya ɗaga hannunsa yana yi masa nuni. "A fito lafiya fa. A dai rage mun ko sidin kwano ne!" Alhaji Sabo ya girgiza kai yana dariya. "Kai Kabiru, wallahi ba ka da dama!" "Me zan yi? Ai gaskiya nake faɗa." Kabiru ya ƙara dariya, sannan ya ɗan gyara zamansa yana kallon Bintu. Ita kuwa Bintu tana zaune ne tana kallonsu, murmushin da ta ɗora a fuskarta yana nan, amma a zuciyarta tana jin kamar ta tashi ta bar wurin tun kafin su ƙarasa hirar. Alhaji ya juya gare ta. "Darling, come with me, please." Ta ɗan gyada kai, ta miƙe a hankali tana daukar handbag dinta. Alhaji ya fara tafiya, ita kuma ta bi bayansa, tana jin har yanzu idanun Kabiru suna kanta. "Enjoy your stay, beautiful girl!" Kabiru ya faɗa cikin dariya. Bintu ta juyo kaɗan, ta yi murmushin dole. "Thank you, sir." Sannan ta sake bin Alhaji. Yayin da suke tafiya, Kabiru ya sake kiran Alhaji Sabo "Alhaji!" Alhaji ya tsaya ya waiwayo. "Me kuma?" Kabiru ya yi murmushi, ya ɗaga yatsansa. "Kar ka manta da maganata fa!" Alhaji Sabo ya yi dariya, ya kaɗa masa fingers biyu. "Just sit down and behave yourself!" Kabiru ya fashe da dariya, ya koma ya jingina da kujerarsa. Bintu kuwa ta ci gaba da bin Alhaji, tana ƙoƙarin kada ta waiwayo. A zuciyarta kuwa, tana roƙon Allah kawai ya sa wannan zaman ya zama gajere.