FORBIDDEN LOVE

Page 5

by @oumamani

馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮
         FORBIDDEN LOVE
                      馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮


DijahAM(Oum Amani)




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 



Page 5



*ARWA'S POV*


    A hankali na shiga bude idona sa suka min nauyi, akan Adda Humaira na soma daura idona wacce take zaune tana bawa second child din ta cereal.

Duk da yadda nake Jin kirjina yana min nauyi sai da nayi murmushi na ce "yaushe kuka zo Adda?"

Dagowa tayi ta kalle ni ta ce "ban dade da zuwa ba, da safe Maama ta kira shine nazo"

Gyada kai kawai nayi na tashi zaune, duk jikina bana jin dadin sa ina bukatar wanka da hot water.
"Bara nayi wanka Adda, bana Jin dadin jikina"

"Hakan ya kama ta, kiyi alwala don har azahar anyi" 

Duk da nayi mamakin lokacin dana dauka ina bacci amma ban sake cewa komai ba, wanka nayi da ruwa mai zafi sosai ina tuno abinda ya faru jiya amma kuma hawayen yaki zubo min.

A hankali na ce "Kana ina Rhys, Baaba aure zai min"

Sai da na fada sannan hawayen ya shiga sauko min da gudu. Ina hawaye na nayi alwala na fito. Ba kowa a dakin hakan ya min daidai, a gurguje na shirya cikin simple gown wacce bata karasa kafa ta ba. Hijab na saka na sallah na babba na hau kan sallaya na fara yin sallolin dake kai na.

Duk sujjada in nazo sai na roki Allah ya zaba min abinda yafi alkhairi a rayuwa ta. Ina idar wa azkar nayi na jinginar da kai na a jikin gado ina tunanin rayuwa ta.

Maama ce ta shigo dauke da tray, bani da karfin da zan tashi na karbi tray din, dole sai da ido kawai nake bin ta.

Zama tayi a gabana bayan ta ajiye tray din, bata ce min komai ba bayan amsa gaisuwa ta sai Mug din tea data miko min. Karba nayi na shiga sipping a hankali idona a kasa.

The silence is very awkward amma kuma bana son magana, ban son ita ma tayi magana don ina tsoron abinda zata ceh.

Rabin tea din na sha kawai na ajiye mug din akan tray. Plate din waffles Maama ta miko min, ban mata musu ba na dauki guda daya na cinye sa. Wipes na dauka na g枚臒e hannu na da baki na, jinginar da kai nai a jikin bed din ina rufe ido na.

"Ya jikin naki?" Maama ta fada bayan ta bata goshi na.

Ba tare dana rufe ido na ba na ce "Alhamdulillah"

Numfashi ta fesar mai zafi ta ce "ki yi wa mahaifin ki biyayya Arwa"

Bude idona nayi na kalle ta ina sakar mata Murmushin da kana gani kasan bana dadin rai bane na ce "In sha Allah, kar ki damu Maama. Na bar wa Allah zabi in har Habeeb ne mafi alkhairi a gare ni Allah ya tabbatar in ba shi bane Allah ya musanya min da mafi alkhairin sa"

Shiru Maama tayi tana kallon diyar tata cike da wani irin tausayi. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Allah ya miki albarka ya shiga d眉kkan al'amuran ki"

"Ameen Ya Allah" na fada ina zame wa na kwanta kawai akan carpet din. Rufe ido na nayi ban bude ba, Ina jin Maama ya lullube ni da duvet ta fice.

Ban san lokacin da bacci ya dauke ni ba sai farka wa da nayi sbd kiran magriba da ake yi. Da sauri na shiga toilet nai alwala...

Ina zaune a gurin da nay sallah har aka Kira Isha, sallah ta nayi na hada da shafa'i da wutr sannan na koma kan bed na zauna, waya ta na janyo ina ganin missed calls din mutane. Hudu na Haala sai biyar na Habeeb ragowar kuma na wajen aiki neh. Na Haala kawai na kira inda tana dauka ta fara mitar na share ta ban dauki wayar ta ba. Shiru na mata sai da ta gama maganar ta tas sannan na ce mata bani da lafiya.

"Amma Arwa shine baki yi min ko message ba" Haala ta fada kamar zata fashe da kuka.

Ban bata amsar tambayar ta ba sai ce wa nayi "Baaba ya ce next week zai daura min aure da Habeeb"

Kamar an dauke wuta haka Haala tayi shiru. Can ta ce "are you okay?"

Kun ga that's my girl, shiyasa nake kaunar ta. Bata tambaye ni mai ya faru ba ko wani abu, kawai ta fara tambaya ta  whether i'm okay or not.

Bana cikin yanayin farin ciki amma sai da nayi murmushi "Haala ya zan yi, duk yadda zan yi don na fahimtar da iyaye na kin san nayi amma Baaba....." numfashi na sauke kawai ina kokarin mayar da hawayen idona na ceh "na bar wa Allah zabi Haala, duk abinda yake alkhairi Allah ya zaba min. Kin ga har ynxu ban san Rhys yana ina ba kuma......" ban karasa ba sbd Adda Humaira data shigo hannun ta rike da Neehal.

Sallama nayi wa Haala na bude wa Neehal hannu Ina sakar mata murmushi. Da gudu ta saki Adda tazo ta rungume ni, daga ta nayi cak na dora akan cinya ta ina murmushi na ce "babyn wace wannan"

Cikin maganar ta da bata fita sosai ta ce "Beben Aty Awaa"

Dariya muka saka ni da Adda, Adda ma zama tayi a gefe na muna hira. Basu bar gidan ba sai after 10..



   Kwana na biyu ko kofar daki na ban leka ba, already na dauki leave a wajen aiki, ko abinci sai dai maids su kawo min, in kuma Maama tana nan ita ta kawo min.
Baaba kuwa dama tun ranar daya fada min aurar da ni zai yi ban kara ganin sa ba. Ni hakan ma ya min.

     Shirya wa na gama cikin ash luxury abaya data min kyau sosai, na saka ash ZARA flat shoe. Gucci bag dina na dauka tare da key din mota ta Black model S Tesla, Baaba ne ya siya min lokacin dana fara zuwa aiki.

Mun yi da Haala zamu hadu a restaurant din mu don nima ina bukatar fresh air din, yau saura kwana biyar Baaba ya daura mun aure kamar yadda ya ce.

Maama bata gida ta tafi asibiti don haka ba wanda na ma sallama na shige mota ta kawai na fita.

Tun da na shiga compound din restaurant din gaba na yake faduwa. Wani irin tsinkewar zuciya nake ji da wani irin yanayi da nake ji kamar na koma gida. Na kusa 10mins a mota na kasa bude wa na fita, sbd tsinkewar zuciyar da nake ji kamar na koma gida amma kuma wani abu mai karfi yana danne tunanin a rai na.

Dole na bude kofar bakina dauke da bismillah na fita.  

A hankali nake tafiya cikin wani irin sanyin jiki. 

A dai dai entry din kamar almara na dan take riga ta nayi gaba zan fadi, ga tsantsin tiles ga tsantsin takalmi na. Na gama saddakar wa faduwa zan yi don haka kawai na rufe ido na bayan na rungumi embarrassing kai na da zan yi da hannu biyu biyu.
   Sai dai a maimaikon na fadi din sai wasu large hands da suka ruko waist dina masu masifar dumi, dumin su kadai ji nake kamar yana burning skin dina, brain dina bai gama daukar abinda ya faru ba ynxu kamshin turaren sa ya shiga hanc谋 na da mugun karfi.

Idona dana rufe na bude suka shige cikin light brown din idon sa..  numfashi na naji yana neman dauke wa sbd ganin wanda ke tsaye a gaba na.......






Saura kwana biyar amaryar Habibu馃拑馃馃檶馃徎

Abin acan a莽an馃 ni dai ban gane mai Maama take nufi da amaryar mu ba. Aure saura kwana biyar ko maganin sanyi baa bamu ba馃槴馃

Na ce waye wannan neh kuma馃檶馃徎馃拑

Kuna da wanda kuke zargi馃槑


Na ce a dinga sambado min kwamenta fah馃槀馃槀馃槀



Comments and share please





***