INUWAR SARAUTA ( SHADOWS OF THE CROWN 👑)

HISTORY OF ZAFIRA

by @jiddaahbarkum

*SHADOWS OF THE CROWN 👑*

*THE HISTORY OF ZAFIRA*


*001*


Barkum…..



Tun ƙarnuka da dama da suka gabata, kafin a haifi sarakunan da ake ambato a yau, kafin a gina manyan katangar fada da kuma kafin a ɗaga tutar masarautar a kan manyan ƙofofinta, akwai wasu ƙananan garuruwa da masarautu da ke rayuwa a yankin da daga baya aka sani da Zafira. A wancan lokaci, yankunan ba su da haɗin kai. Kowace al'umma tana da nata jagora, nata dokoki da kuma nata rundunar tsaro. Ana samun rikice-rikice a tsakaninsu saboda filaye, hanyoyin kasuwanci, rijiyoyin ruwa da kuma mallakar yankuna masu albarka. Kasuwanci yana bunƙasa a wasu wurare, amma zaman lafiya bai daɗe. Ƙaramin sabani kan iya rikidewa zuwa babban yaƙi, yayin da wasu shugabanni ke amfani da ƙarfin sojojinsu wajen ƙwace ikon wasu. A cikin wannan yanayi ne wani babban jarumi kuma basarake mai suna Zafir ya bayyana. Zafir ba wai ƙarfin mayaƙansa kaɗai ya sa aka san shi ba. Ya kasance mutum mai hangen nesa, wanda ya fahimci cewa ba za a iya gina ƙasa mai ɗorewa a kan yaƙe-yaƙe kawai ba. Ya fara da haɗa kan wasu shugabanni ta hanyar yarjejeniyoyi, sannan ya kafa runduna guda da za ta kare yankunan da suka amince su kasance ƙarƙashin jagorancinsa. Ba kowa ne ya amince da wannan haɗin kai ba. Wasu sun yi yaƙi, wasu sun gudu zuwa wasu yankuna, yayin da wasu suka miƙa wuya bayan sun fahimci cewa ba za su iya kayar da shi ba. A ƙarshe, Zafir ya yi nasarar haɗa manyan yankunan ƙarƙashin mulki guda. Daga nan aka kafa Daular Zafira. An gina babban birnin masarautar, aka kafa katangar tsaro, aka ware wuraren kasuwanci, aka kuma kafa fadar da za ta zama cibiyar gudanar da mulkin daular. Tun daga wannan lokaci, sunan Zafira ya fara yaɗuwa a tsakanin sauran masarautu.

*ZAMANIN SARAKUNAN FARKO*

Bayan rasuwar Sarki Zafir, ɗansa Nuhman ya gaji sarauta. Sarki Nuhman ya mayar da hankali wajen faɗaɗa iyakokin masarautar. A zamaninsa, an haɗa wasu yankuna da dama da Zafira, an kuma ƙarfafa alaƙar kasuwanci da masarautun da ke maƙwabtaka da ita. Bayan Nuhman, Sarki Abdulmalik ya hau karagar mulki. Shi ne ya kafa manyan cibiyoyin kasuwanci, ya kuma ƙarfafa tsarin tattara haraji da raba albarkatun ƙasa. Ya fahimci cewa ƙarfin masarauta ba ya ta'allaka da yawan sojoji kawai, har ma da arzikin da ke cikinta. Sai Sarki Harith ya biyo bayansa. Mulkinsa ya zo a lokacin da wasu yankuna suka fara ƙalubalantar ikon Zafira. An yi yaƙe-yaƙe a iyakoki, an rasa rayuka, amma a ƙarshe rundunar masarautar ta samu nasarar kare ƙasar. Duk da haka, tarihin waɗannan sarakuna bai kasance cikakke ba. Kowannensu ya bar wani abu a baya; wasu sun bar nasarori, wasu kuma sun bar matsalolin da waɗanda suka gaje su suka yi ta ƙoƙarin magancewa. Amma babu wanda ya yi tsammanin cewa wani babban rikici zai taso a cikin gidan sarautar kansa.

*SARKI JALALUDDEEN*

Daga baya, karagar mulki ta koma hannun wani basarake mai suna Sarki Jalaluddeen. Jalaluddeen ya kasance mutum mai hikima, kamun kai da tsananin son zaman lafiya. Ba ya son yaƙi, amma hakan bai sa ya zama mai rauni ba. Yana iya zama mai sauƙin kai ga mutanensa, amma idan aka taɓa martabar masarautarsa, ba ya wasa. A zamaninsa, Zafira ta samu ci gaba sosai. An gyara hanyoyin ruwa, an gina sabbin kasuwanni, an ƙarfafa tsaron iyakoki, sannan aka bunƙasa ilimi da wuraren ibada. Jalaluddeen ya kuma kafa wata muhimmiyar cibiya da ta zama ginshiƙin mulkin Zafira: Majalisar Sarauta. Majalisar ta ƙunshi manyan jami'an gwamnati da masu fada aji waɗanda aikinsu shi ne taimaka wa sarki wajen gudanar da mulki da yanke manyan hukunci. Daga cikin mukaman da ke cikin tsarin masarautar akwai Waziri, Galadima, Madaki, Sarkin Yaki, Alkali da kuma Hakimai. A zamaninsa, an kuma tabbatar da wata doka da ta shafi gadon sarauta. A Zafira, ba wai kasancewar mutum babban ɗan sarki kaɗai ke tabbatar da cewa zai hau karagar mulki ba. Ana la'akari da jinin sarauta, cancantar mutum da kuma amincewar Majalisar Sarauta. Wannan doka ce da daga baya za ta zama sanadin wasu manyan rikice-rikice. Sarki Jalaluddeen yana da 'ya'ya maza biyu. Na farko shi ne Yarima Tahir, babban ɗansa kuma magajinsa na farko. Na biyu kuma shi ne Yarima Azlan, ƙanensa. Tahir ya kasance mutum mai son cigaban masarauta, yayin da Azlan yake da nutsuwa da ƙwarewa wajen harkokin tsaro da gudanar da manyan al'amura. Duk da bambancin halayensu, 'yan'uwan suna da kyakkyawar alaƙa. Jalaluddeen ya tabbatar da cewa dukansu sun samu tarbiyya a cikin tsarin masarautar. Ya san cewa wata rana ɗaya daga cikinsu zai zauna a kan karagarsa. Sai dai bai san irin abubuwan da za su faru kafin wannan rana ba.

*SARKI TAHIR: MULKIN BABBA*

Bayan rasuwar Jalaluddeen, Yarima Tahir ya hau karagar mulki. An naɗa shi a matsayin Sarki Tahir a gaban Majalisar Sarauta, manyan hakimai da wakilan al'ummomin Zafira. Hawan sa karaga ya zo da farin ciki ga wasu, yayin da wasu ke kallon sabon mulkin da shakku. Tahir ya kasance sarki mai son zaman lafiya, amma bai yarda a raina dokokin masarautarsa ba. A zamaninsa, an ƙarfafa rundunar tsaro, an gyara tsarin tattara haraji, sannan aka ƙara bunƙasa kasuwanci tsakanin Zafira da sauran masarautu. Ya kuma yi ƙoƙarin rage ƙarfin wasu manyan masu fada aji waɗanda suka saba yin amfani da kusancinsu da gidan sarauta wajen cin moriyar talakawa. Wannan mataki bai yi wa kowa daɗi ba. Wasu daga cikin masu fada aji sun fara kallon Tahir a matsayin sarki mai tsaurin ra'ayi. Sun saba da samun damar yin duk abin da suka ga dama, amma sabon tsarin mulkinsa ya fara hana su wannan damar. Duk da haka, Tahir bai ja da baya ba. A rayuwarsa ta iyali, yana da ɗa mai suna Yarima Mus'ab, wanda shi ne magajinsa na farko. Mus'ab ya kasance ɗan gidan sarauta, jikan Jalaluddeen kuma magajin gidan mahaifinsa. Ƙanin Tahir, Azlan, ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da yake dogara da su. Azlan yana da babban matsayi a cikin harkokin tsaro da gudanar da masarauta, kuma yana taimaka wa ɗan'uwansa wajen tabbatar da zaman lafiya. Amma mulkin Tahir bai daɗe ba kamar yadda mutane suka yi zato. Bayan wasu shekaru, wani mummunan al'amari ya girgiza Zafira. Sarki Tahir ya rasu. Rasuwarsa ta zo ne a lokacin da Mus'ab bai kai matsayin da zai iya jagorantar masarauta shi kaɗai ba. Mutane sun shiga jimami. Fadar sarki ta cika da baƙin ciki, yayin da manyan jami'an gwamnati suka fara taro domin tattauna makomar daular. A cikin Majalisar Sarauta aka fara samun sabani. Wasu sun so a naɗa Mus'ab a matsayin sarki, sannan a kafa masa majalisar riƙon ƙwarya har sai ya kai shekarun da zai iya gudanar da mulki. Wasu kuwa sun yi ganin cewa wannan ba lokaci ba ne na gwaji. Akwai buƙatar shugaba mai cikakken ƙarfi da gogewa, wanda zai iya kare masarautar daga duk wata barazana. A ƙarshe, bayan tattaunawa mai tsawo, Majalisar Sarauta ta amince da naɗa Yarima Azlan a matsayin sabon Sarkin Zafira. Haka ne Azlan ya zama sarki bayan rasuwar babban ɗan'uwansa. Sai dai wannan naɗi bai share tarihin Tahir ba. Mus'ab ya ci gaba da kasancewa ɗan tsohon sarki, jinin gidan sarauta kuma ɗan gidan da ya taɓa zama a kan karaga. Wasu sun amince da shawarar majalisa. Wasu kuma sun ci gaba da ganin cewa ya kamata a riƙe gadon Tahir har sai ɗansa ya girma. Amma ba kowa ne yake iya faɗin abin da ke zuciyarsa ba a cikin fadar sarki.

*MULKIN SARKI AZLAN*

Sarki Azlan ya karɓi ragamar mulki a lokacin da Zafira ke buƙatar zaman lafiya fiye da komai. Ya yi ƙoƙarin ci gaba da kyawawan manufofin ɗan'uwansa, amma salon mulkinsa ya bambanta. Azlan ya fi son tattaunawa, yana sauraron shawarwari, kuma yana ba mutanen da yake amincewa da su damar shiga harkokin gwamnati. A zamaninsa, Zafira ta ci gaba da bunƙasa. An ƙarfafa ilimi, an bunƙasa kasuwanci, an inganta hanyoyin sufuri, sannan aka ƙarfafa alaƙar masarautar da sauran ƙasashe. Fadar sarki ta zama cibiyar manyan tarurruka, liyafar sarauta da kuma shawarwarin da suka shafi makomar daular. Amma duk da zaman lafiyar da ake gani a fili, wasu abubuwa sun fara sauyawa a bayan labule. Manyan iyalai sun fara samun ƙarfin iko. Wasu jami'an gwamnati sun fara amfani da kusancinsu da sarki wajen cimma burinsu. Daga cikin manyan jami'an da suka samu matsayi a wannan zamani akwai Waziri Rufa'i. Rufa'i mutum ne mai ilimi da iya magana. Yana da basira wajen harkokin gwamnati, kuma a fili yana nuna biyayya ga sarki. Yana cikin mutanen da Azlan yake amincewa da su wajen gudanar da manyan al'amuran masarauta.

*DOKAR GADON SARAUTAR ZAFIRA*

Tsawon ƙarnuka, Zafira ta riƙe wata muhimmiyar doka game da gadon sarauta. Ba a tabbatar da sabon sarki ta hanyar haihuwa kawai ba. Akwai muhimman abubuwa uku da ake la'akari da su: Na farko: Jinin Sarauta. Dole ne wanda zai hau karaga ya kasance daga gidan daular Zafira. Na biyu: Cancanta. Dole ne ya kasance mutum mai iya jagorantar al'umma, kare masarauta da kuma gudanar da harkokin mulki. Na uku: Amincewar Majalisar Sarauta. Majalisar ce ke tabbatar da cewa wanda aka zaɓa zai iya riƙe amanar daular. Wannan doka ta sa gadon sarauta ya kasance abu mai muhimmanci fiye da burin mutum guda. Amma a duk lokacin da aka sami sarauta, ana samun waɗanda suke ganin cewa su suka fi cancanta. Wasu suna neman karaga saboda sun haƙura da jiran lokacinsu. Wasu kuma suna ganin cewa an tauye musu haƙƙin da ya kamata su mallaka. A irin wannan yanayi ne burin mutum zai iya zama barazana ga rayuwar wasu.

*AL'ADU DA TSARIN MASARAUTAR*

Zafira tana da wasu al'adu da suka zama ginshiƙin rayuwar masarautarta. A duk lokacin da aka naɗa sabon sarki, ana gudanar da Hawan Sarauta, babban biki da ke haɗa manyan jami'ai, hakimai, mayaƙa da jama'a daga sassa daban-daban na ƙasar. Ana kuma gudanar da taron Majalisar Juma'a, inda manyan masu fada aji ke zuwa fadar sarki domin tattauna muhimman al'amuran masarauta. Akwai kuma ranar gaisuwar sarki, inda wakilan yankuna ke zuwa domin gabatar da rahotanni da kuma sabunta mubaya'arsu. Daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci a fadar akwai tambarin daular Zafira, wanda ake amfani da shi a kan takardun hukuma, hatimai da muhimman kayan sarauta. Wannan tambari ba ado kawai ba ne. Alama ce ta ikon gidan sarauta da kuma tarihin daular.

*TSOHON TARIHI, SABON RIKICI*

A yau, Zafira tana ƙarƙashin mulkin Sarki Azlan. Yana da 'ya'ya maza biyu: Yarima Aimaan da Yarima Imam. Aimaan shi ne babba, mai shekara talatin. Yana da burin zama sarki kuma yana kallon kansa a matsayin magajin da ya fi kowa cancanta. Imam kuwa yana da shekara ashirin da bakwai. Shi mutum ne mai nutsuwa, wanda ba ya son siyasar fada, duk da cewa yana da basira da zuciyar tausayi. Akwai kuma Mus'ab, ɗan marigayi Sarki Tahir, wanda yake da matsayi na musamman a gidan sarauta. A idon mutane, waɗannan samari suna rayuwa ne cikin wata tsohuwar masarauta mai cike da tarihi da al'adu. Amma tarihi ba ya mutuwa kawai saboda an daina magana a kansa. Wasu tsoffin rikice-rikice suna jiran lokacin da za su sake bayyana. Wasu yarjejeniyoyi ba a taɓa mantawa da su ba. Wasu mutane suna rayuwa da sirrin da ba su taɓa bayyana wa kowa ba. Kuma wasu suna jiran damar da za su sauya makomar daular. A Zafira, karaga ba ta taɓa zama kujerar zinariya kawai ba. Karaga amanar da take buƙatar jini, sadaukarwa da gaskiya ce. Amma idan aka gina mulki a kan ƙarya fa? Idan wanda ake kira magaji ba shi ne wanda ake tsammani ba fa? Kuma idan tarihin da aka koya wa mutane ya kasance wani ɓangare ne kawai na gaskiya fa? A cikin wannan masarauta, kowa yana da nasa labarin. Kowa yana da abin da yake nema. Kowa yana da abin da yake ɓoyewa. Kuma duk wanda ya kuskura ya nemi inuwar kambun, dole ne ya kasance a shirye domin fuskantar abin da ke ɓoye a ƙarƙashinsa. For the crown does not only carry power. It carries the weight of every secret that built it.