DARE DUBU DA DAYA 1001 Mujalladi na Daya 1
BABI NA GOMA SHA BIYU (12): CIGABAN HIKAYAR DAN DAKO DA MATAN BAGADAZA SHIGOWAR KALANDARAWA UKU DA SARKI HARUNAR RASHEED
by @shuraih99
====================================================================
DARE DUBU DA DAYA (ALF LAILA WA LAILA)
BABI NA GOMA SHA BIYU (12): CIGABAN HIKAYAR DAN DAKO DA MATAN BAGADAZA SHIGOWAR KALANDARAWA UKU DA SARKI HARUNAR RASHEED
[DARE NA GOMA]
Fassarar: Shuraihu Usman
====================================================================
A babi na goma sha daya idan mai karatu bai manta ba, mun tsaya a inda Dan Dako ya mayar da dukkan kudinsa ga wadannan 'yan mata guda uku masu kyau a fadar Bagadaza, suka bashi izinin zama tare da su a kan sharadin kada ya yi magana a kan abin da bai shafe shi ba, sannan aka shiga zuba ruwan inabi a karshen DARE NA GOMA SHA DAYA. To yanzu bari mu ji irin wasannin nishadi da baitocin ruwan inabi da suka rera a tsakaninsu, da kuma yadda Kalandarawa guda uku da Sarki Haruna Rasheed zasu shigo wannan fada a cikin wannan DARE NA GOMA.
--- DARE NA GOMA ---
Gari ya waye, Sarki Shahriyar ya fita fada ya gudanar da al'amuran mulki ba tare da ya ambaci batun kisan Shahrazad ba. Babban Waziri ya koma gida yana godiya ga Allah da ya ga 'yarsa tana ci gaba da rayuwa cikin aminci.
Da dare ya tsala a cikin wannan DARE NA GOMA, Sarki Shahriyar ya shigo daki ya kwanta da Shahrazad. Bayan ya gama biyan bukatarsa, sai qanwarta Dunyazad ta tashi daga qasan shimfida ta ce:
"Ya yayata, idan baki fara barci ba, don girman Allah ki qarasa mana labarin Dan Dako da 'Yan Matan nan domin mu ji irin nishadin da suka yi da kuma shigowar baki a cikin wannan dare!"
Shahrazad ta duba wajen Sarki Shahriyar cikin ladabi ta ce: "Zan ci gaba idan har wannan babban Sarki mai daraja ya ba ni izini!" Sarki ya ce: "Fadi ina saurarenki!"
Nan take Shahrazad ta gyara zama ta ci gaba da ba da wannan kyakkyawan labari a cikin wannan DARE NA GOMA kamar haka:
"Bayan Dan Dako ya zauna a gefen wadannan 'yan mata guda uku, sai budurwa mai sayayya (Fahima) ta cika kofin ruwan inabi ta miqa wa budurwa mai kofa (Zubaida). Zubaida ta daga kofin tana kallon dan dako ta rera wasu baitoci tana cewa:
Kada ka sha kofin ruwan inabi face daga hannun amintaccen aboki,
Mutum mai daraja wanda asalinsa da zuriarsa suke da kyau!
Domin ruwan inabi yana qara zakin magana ga mai karamci,
Amma yana zama abin kyama idan ya shiga cikin marar mutunci!
Ta shanye kofinta, sannan ta cika wani kofin ta miqa wa dan dako. Dan dako ya karba ya sumbaci hannunta, maye ya fara baci a kansa yana tangadi, ya rera wasu baitoci yana cewa:
Dukkan abin sha da ke dauke da jini Shari'a ta haramta shi,
Face abu guda daya kacal, wato jinin da ke fita daga itacen inabi!
Ku cika kofuna! Ku dauki dukkan dukiyata ta gado da wadda na samu,
Na fanshi dukkan raina domin wadannan kyawawan idanuwa!
Budurwa mai sayayya ta sake cika kofi ta miqa wa 'yar'uwarta dake zaune kan karaga (Amina), ita kuma Amina ta daga kofinta cike da annashuwa ta rera baitoci tana cewa:
Ku kawo kofuna na zaki da dadi a nan take!
Ku cika mani kofi taf mai cike da daula!
Ina neman marmarin maɓulɓular ruwan rai,
Domin na wanke dukkan baqin cikin duniya!
Dan dako ya miqe tsaye a gaban Zubaida, ya sunkuyar da kansa cikin natsuwa ya ce: 'Ya shugabata, ni bawanki ne kuma dan aikenki na gaskiya!' Ya shiga rera waqa yana cewa:
Ga bawan bayinki a tsaye a bakin kofarki yana maraba,
Yana yabon dimbin alherinki da kyaututtukan da kika yi masa!
Ya ke wannan ma'abociyar kyau, shin zai sami izinin zama,
Domin ya ji dadin kyan fuskarki da ba za ta taba rabuwa da qauna ba?
Zubaida ta dube shi da fara'a ta ce: 'Sha abin shanka cikin aminci da walwala!' Ta miqa masa wani kofi mai cike da tsohon ruwan inabi mai jajen launi tamkar wuta. Dan dako ya karba ya sumbaci kofin ya rera wata waqa yana cewa:
Na ba ta tsohon ruwan inabi mai kama da jajayen kumatunta,
Wanda ke sheqi tamkar harshen wutar da ke ruruwa a tanda!
Ta sumbaci bakin kofin tana murmushi ta tambaye ni:
'Ta yaya zaka ba wa mutane kumatunsu domin su sha a kofi?'
Na ce da ita: 'Wadannan hawaye ne na zuciyata da suka dahu,
Saboda tsananin zafin shauqin da ke cika qirjina!'
Budurwar ta dube shi ta mayar masa da amsa da wani baiti tana cewa:
Idan har ka zubar da hawayen jini a kaina ya kai wannan aboki,
To ka bar ni na sha su da kaina domin darajar kanka da idanunka!
Suka shanye kofuna, suka ci gaba da rawa, da dariya, da kade-kade har sai da mayen ruwan inabi ya gama mamaye kwakwalwarsu gaba daya!
A wannan lokaci, sai budurwa Zubaida ta tashi tsaye, ta cire dukkan tufafin jikinta ta zama tsirara haihuwar uwarta, ta fada cikin wannan katafaren tafki na marmara mai dauke da ruwan wardi tana wanka tana feshin ruwa!
Bayan ta fito daga ruwan, sai ta zo daidai gaban dan dako, ta zauna a kan cinyarsa da gwiwoyinsa, ta nuna masa kanta da jikinta ta ce da shi cikin tsokanar barkwanci: 'Ya kai mai dako, gaya mani wane suna kake kiran wannan abu?'
Dan dako ya dube ta yana zazzare idanuwa da maye ya ce: 'Ina kiran shi da tsagewar marmara!'
Zubaida ta fashe da dariya ta ce: 'Kai tir da kai! Wannan wane irin sunan gaba-da-gaba ne haka?' Ta dan buge wuyansa a hankali ta ce: 'Sunansa shi ne Lambun Jin-dadi da Annashuwa!'
Daga nan sai budurwa ta biyu (Fahima) ita ma ta tashi, ta tube kayanta ta shiga cikin ruwan tafkin marmara tana iyo. Ko da dan dako ya kalli tsiraicin jikinta a cikin ruwa mai kyalli, sai ya kasa daurewa, ya rera wasu zafafan baitoci yana cewa:
Idan na kwatanta siffarki da reshe mai yabanya a lambun gona,
To na yi babban kuskure mara iyaka a cikin maganata!
Domin shi reshe yana da kyau ne idan yana sanye da cikakkun ganyayyaki,
Amma ke kin fi kowane kyau a duniya a lokacin da kike tsirara ba tare da tufafi ba!
Ko da budurwar ta ji wadannan baitoci, sai ta yi murmushi ta fito daga tafkin, ta zo ta zauna a kan cinyarsa tana tsokanarsa da sunayen barkwanci, shi kuma yana fadin maganganun dariya har sai da matan suka riqa kwashewa da dariya suna faduwa a kan bayansu!
A qarshe dai sai shi kansa Dan Dako ya tashi tsaye ya cire dukkan tufafinsa, ya fada cikin tafkin marmara yana iyo yana feshin ruwa! Da ya fito sai ya zauna a gabansu ya ce: 'Ku kuma gaya mani wane suna kuke kiran wannan nawa?'
Suka riqa fadin sunayen ban dariya suna cewa: 'Dan qaramin qusa!' Shi kuwa ya kwashe da dariya ya ce: 'A'a, sunansa Giwa Mai Rushe Ganuwa!' Dakin ya cika da wata gigitacciyar dariya da shewa wadda ba a taba jin irinta ba!
Suna cikin wannan matsanancin maye da annashuwa, kwatsam sai suka ji ana buga kofar gidan da qarfi: 'Qwan! Qwan! Qwan!'
Bugun kofar bai hana su nishadinsu ba, amma Zubaida ta sanya tufafinta ta kalli Fahima ta ce: 'Maza ki duba ko su wanene a bakin kofa a wannan tsakiyar dare!'
Fahima ta tafi bakin kofa ta leqa ta wata 'yar kofa ta sirri. Sai ta tarar da wasu mutane guda uku Kalandarawa na qasar Farisa: kowannensu gashin kansa, da gemunsa, da girarsa duk a aske suke sumul! Kuma kowannensu idonsa na dama a tsiyaye yake yana gani da ido daya kacal!
Sun roqe ta da ta basu mafaka saboda tsoron jami'an tsaron birni.
Fahima ta dawo ta shaida wa 'yan'uwanta. Zubaida ta ce: 'Bude musu su shigo, amma ki karanta musu sharadin da aka rubuta a jikin kofa cewa: WANDA YA YI MAGANA A KAN ABIN DA BAI SHAFE SHI BA, ZAI JI ABIN DA BA ZAI YI MASA DADI BA!'
Fahima ta bude kofa ta shigar da su bayan sun amince da sharadin.
Ko da Kalandarawan nan guda uku suka shiga falon, suka ga kyan fadar da kyan wadannan mata, da kuma Dan Dako zaune a tsakiya yana takama tamkar maigida, sai suka zaci cewa dan dako shi ne babban sarkin gidan!
Dan Dako ya gyara zama cike da takama ya ce: 'Barka da zuwa ya ku fakirai! Ku zauna a gefena ku ci abinci ku sha ruwan inabi, amma kada wani ya kuskura ya tambayi abin da bai shafe shi ba!'
Kalandarawa suka sunkuyar da kai cikin ladabi suka ce: 'Mun amince ya shugabanmu!' Suka zauna aka kawo musu abinci da ruwan inabi suka ci suka qoshi.
Bayan sun kammala, sai Kalandarawan suka zaro molonsu suka shiga rera waqoqi masu dadi da ban tausayi, suna kada kai suna kuka mai sanyaya zuciya. Dakin ya qara cika da wata sabuwar raye-raye da shauqi.
Suna cikin wannan hali, kwatsam sai aka sake jin wani sabon bugun kofa mai amo fiye da na farko: 'Qwan! Qwan! Qwan!'
Fahima ta sake zuwa kofa ta leqa, sai ta ga wasu mazaje guda uku sanye da tufafin attajiran Mosul masu kwarjini, tare da wani qaton bawan daji baqi mai takobi a bayansu.
Wadannan mutane ba wasu bane face SARKI HARUNA RASHEED, da Wazirinsa JA'AFAR AL-BARMAKI, da Hauni MASRUR!
Suna yawo a cikin gari a boye domin ganin halin da jama'a ke ciki, sai suka ji sautin kade-kade da waqoqi daga wannan fada, Sarki ya nace cewa lallai sai sun shiga ciki sun ga abin da ke faruwa!
Waziri Ja'afar ya yi amfani da ladabi ya fada wa Fahima cewa su attajirai ne baki da suka bace a hanya kuma suna tsoron jami'an tsaro.
Fahima ta dawo ta shaida wa Zubaida. Zubaida ta amince aka bude musu aka shigar da su bayan an kafa musu sharadi: 'Kada ku tambayi abin da bai shafe ku ba!'
Ko da Sarki Haruna Rasheed da Wazirinsa suka shiga cikin falon, sai idanuwansu suka raina fata! Ga 'yan mata guda uku masu tsananin kyau, ga Dan Dako mai maye, ga Kalandarawa guda uku kansu a aske sumul kowannensu da ido daya!
Waziri Ja'afar ya kalli Sarki a boye ya ce: 'Ya shugabana, wannan wuri cike yake da al'ajabi!' Sarki ya ce: 'Bari mu zuba musu ido mu ga qarshen lamarin!'
Aka kawo wa Sarki da mutanensa abinci da ruwan inabi suka zauna a gefe. Dan Dako ya dube su yana dariya ya ce: 'Ku ci ku sha ya ku 'yan Mosul, amma ku kiyaye sharadin gidan nan!' Sarki Haruna Rasheed ya yi murmushi ya ji dadin barkwancin dan dako.
Suka ci gaba da shaye-shaye da nishadi har dare ya raba sosai, kowa ya cika da annashuwa.
Amma kwatsam, yayin da dare ya doshi gabar asuba, sai budurwa Zubaida ta miqe tsaye daga kan kujerarta.
Murmushin fuskarta ya bace gaba daya, idanuwanta suka kada suka yi jajir, fuskarta ta canza ta zama mai matuqar cika da damuwa da makoki!
Zubaida ta kalli 'yar'uwarta Amina ta ce da wata kakkausar murya mai cike da kuka:
'Ya 'yar'uwata, lokacin da aka saba ya yi! Lokacin cika rantsuwarmu ta kowane dare ya riske mu! Maza tashi ki fito da su yanzu-yanzu!'
Ko da Amina ta ji wannan umarni, sai jikinta ya dauki rawa, ta miqe da hanzari ta shiga wani daki na cikin gidan..."
A daidai wannan gaba, sai hasken alfijir ya fara ketowa a sararin samaniya, Shahrazad ta ga safiya ta yi, sai ta dakata da zancenta mai dadin sauraro ta yi shiru!
Dunyazad ta dube ta da matuqar sha'awa da shauqi ta ce: "Kai ya yayata! Lallai wannan labari ya cika da zakin kunne, da dadi, da cikar nishadi da ban al'ajabi mara misali!"
Shahrazad ta yi murmushi ta dube ta ta ce: "Ai wannan ba komai ba ne idan aka kwatanta shi da labarin da zan fada muku a dare mai zuwa, idan har Allah Ya raya ni kuma wannan babban Sarki ya qyale ni?"
Ko da Sarki Shahriyar ya ji wannan batu, sai ya ce a ransa: "Wallahi ba zan kashe ta a yau ba, sai na ji sauran wannan kyakkyawan labari mai ban mamaki!"
Wayewar gari ke da wuya, Sarki ya fita fada ya gudanar da al'amuran mulki yana bayar da umarni da hani har dare ya sake rufowa, shi kuwa babban Waziri ya koma gida fuskarsa cike da farin ciki da godiyar Allah da ya ga 'yarsa tana ci gaba da rayuwa cikin aminci!
(A nan muka kawo qarshen BABI NA GOMA SHA BIYU cif!)
====================================================================