DARE DUBU DA DAYA 1001 Mujalladi na Daya 1

BABI NA GOMA SHA TARA (19): CIGABAN HIKAYAR DAN DAKO DA MATAN BAGADAZA: CIGABAN LABARIN KALANDAR NA UKU

by @shuraih99

====================================================================

DARE DUBU DA DAYA (ALF LAILA WA LAILA)

BABI NA GOMA SHA TARA (19): CIGABAN HIKAYAR DAN DAKO DA MATAN BAGADAZA: CIGABAN LABARIN KALANDAR NA UKU

[DARE NA GOMA SHA BIYAR]

Fassarar: Shuraihu Usman

====================================================================

A babi na goma sha takwas idan mai karatu bai manta ba, mun tsaya a inda Yarima Ajib ya kifar da mahayin Dokin Tagulla daga kan Dutsen Qarfe, jirginsa na tagulla ya kife a teku bayan ya ambaci sunan Allah, ya fada wani tsibiri inda ya gano wani kyakkyawan saurayi dan attajiri da aka boye shi a qarqashin qasa domin tsoron kada Yarima Ajib ya kashe shi a shekararsa ta goma sha biyar a karshen DARE NA GOMA SHA TAKWAS. To yanzu bari mu ji yadda qaddara zata cika a kan wannan yaro da kuma irin balaguron da Tsuntsun Ruku zai yi da Yarima a cikin wannan DARE NA GOMA SHA BIYAR.

--- DARE NA GOMA SHA BIYAR ---

Gari ya waye, Sarki Shahriyar ya fita fada ya gudanar da al'amuran mulki ba tare da ya ambaci batun kisan Shahrazad ba. Babban Waziri ya koma gida yana godiya ga Allah da ya ga 'yarsa tana ci gaba da rayuwa cikin aminci.

Da dare ya tsala a cikin wannan DARE NA GOMA SHA BIYAR, Sarki Shahriyar ya shigo daki ya kwanta da Shahrazad. Bayan ya gama biyan bukatarsa, sai qanwarta Dunyazad ta tashi daga qasan shimfida ta ce:

"Ya yayata, idan baki fara barci ba, don girman Allah ki ba mu wannan labari mai cike da tausayi na Yarima Ajib domin mu ji yadda qaddara ta auku a kan wannan saurayi a cikin wannan dare!"

Shahrazad ta duba wajen Sarki Shahriyar cikin ladabi ta ce: "Zan ba da labarin idan har wannan babban Sarki mai daraja ya ba ni izini!" Sarki ya ce: "Fadi ina saurarenki!"

Nan take Shahrazad ta gyara zama ta ci gaba da ba da wannan kyakkyawan labari a cikin wannan DARE NA GOMA SHA BIYAR kamar haka:

"Kalandar na uku wato Yarima Ajib ya gyara zama ya ci gaba da ba wa Zubaida da sauran bakin da ke falon labarinsa kamar haka:

'Bayan na yi wa wannan saurayi alqawarin cewa zan tsare shi, sai muka ci gaba da zama tare a cikin wannan daki na karkashin qasa. Muka kwashe kwanaki talatin da tara (39) cif muna tare cikin tsananin soyayya da aminci!

Ina yi masa hidima tamkar bawansa: ina dafa masa abinci mai dadi, ina shayar da shi ruwan inabi mai qamshi, muna buga wasan kafta kutse (shatranj), muna rera waqoqi. Ban taba fada masa ko ni wanene ba domin kada hankalinsa ya tashi. Na ji qaunarsa ta mamaye dukkan zuciyata har na riqa jin kamar dan'uwana ne na ciki daya!

A safiyar rana ta arba'in (40)—wato ranar qarshe ta cikar wa'adin shekararsa ta goma sha biyar da kuma cikar wa'adin faduwar mahayin dokin tagulla—sai wannan matashi ya farka daga barci fuskarsa cike da annuri da matsananciyar murna!

Ya rungume ni a qirjinsa yana dariya ya ce:

'Ya dan'uwana, yau ce rana ta arba'in cif! Mun sami nasara, qaddarar mutuwa ta kauce daga kaina! Yau wannan Yarima Ajibu ba zai sami damar kashe ni ba har abada! Gobe da safe mahaifina zai dawo da jirgi ya kwashe mu mu koma gida cikin aminci! Don girman Allah ka tashi ka dafa mani ruwan dumi na yi wanka na tsarkake jikina, sannan ka dauko mani wata cikakkiyar kankana mai zaki ka yanka mani a kan faranti tare da sukari domin na karya kumallo da ita raina ya yi sanyi!'

Na fashe da kukan farin ciki, na rungume shi na ce: 'Alhamdu lillahi ya dan'uwana! Yau ce ranar murna da kubuta!'

Nan take na tashi na kunna wuta na dafa ruwan dumi. Na yi masa wanka mai kyau, na shafa masa turaren miski da na furen wardi, sannan ya sanya sababbin tufafi na alharini ya kwanta a kan gadon alfarma cike da nishadi yana murmushi.

Bayan haka, sai na dauko wata katuwar kankana mai kyau da na gani a cikin kwanonin abinci, na ajiye a kan wani faranti na azurfa. Na dauko wata qatuwar wuka mai kaifi da sheqi domin na yanka masa kankanar.

Yaron ya kalle ni yana murmushi ya ce: 'Ya dan'uwana, ka miko mani wukar da kankanar nan kusa da ni domin na gani!'

Na dauki farantin kankanar na ajiye a gefen matashin kan gadonsa, na riqe wukar a hannuna na dama, na taka gefen shimfidar gadon domin na haye na zauna a gefensa na yanka masa kankanar.

Amma a daidai lokacin da na daga kafata ta dama na taka a kan shimfidar alharinin gadon, sai wani mummunan kuskure na qaddarar Allah ya auku!

Kafata ta zame a kan sulbin alharinin shimfidar!

Na rasa daidaitona gaba daya, jikina ya karkata na fadi da dukkan qarfina a kan gadon!

Wukar da ke hannuna a zube, sai ta fada daidai a kan qirjin wannan kyakkyawan matashi, ta soke qirjinsa ta kutsa kai har cikin tsakiyar zuciyarsa!

Yaron ya saki wata qaramar ajiyar zuciya: 'Ah!' Jini ya fantsama a kan farar fuskarsa da tufafinsa, idanuwansa suka juye, ya mutu a nan take a cikin dakiqu qanana ba tare da ya sake motsa ko yatsansa ba!

Ko da na ga abin da ya faru da idanuna, sai duniya ta yi mani duhu! Hankalina ya gama tashi, na fadi a kan gawar ina kuka da kururuwa mara misali!

Na riqa yaga tufafina ina dukan kaina a jikin bango ina cewa:

'Wayyo ni Ajib! Wayyo ni mai baqin rabo da masifa! Ashe da gaske ne qaddarar Allah ba ta taba kuskure ba? Na zo domin na cece shi, amma ga shi na kashe shi da hannuna ba tare da na yi niyya ba!'

Ina cikin wannan kuka da hauka, kwatsam sai na ji sautin matuqan jirgin ruwa a bakin teku: ashe mahaifin yaron da bayinsa ne suka iso da wuri domin su taryi dansu lafiya a rana ta arba'in!

Tsoro ya kama ni matuqa, na ce a raina: 'Idan mahaifinsa ya ganni a nan tare da gawar dansa, to lallai zai tabbatar da cewa ni ne na kashe shi da gangan kuma zai sa a yanka ni nan take!'

Na fita da sauri ta kan matakalar benen, na mayar da marfin kofar na rufe, na watsa qasa a kai ba tare da na gama gyarawa ba, sannan na ruga a guje na sake hawa saman wannan katuwar bishiya na boye a cikin ganyayyaki ina leqe!

Ina kan bishiyar ina kallon duk abin da ke faruwa a qasa, sai na ji zuciyata ta tsufa kafin kaina ya yi furfura saboda tsananin zafin baqin cikin da ya riske ni, na shiga rera wadannan baitoci a raina ina cewa:

Sau nawa farin ciki yake guduwa da nufin Allah,

Guduwar da ke buwayar basirar mafi wayon mutane!

Sau nawa baqin ciki ke fara rana da qunci,

Amma kafin rana ta fadi sai ya zama zallar farin ciki!

Sau nawa alheri ke zuwa a bayan qunci da wahala,

Yana sanya zuciyar mai makoki ta cika da matsananciyar murna!

Jirgin ruwan ya tsaya a gabar tsibirin. Sai ga wannan tsoho attajiri da bayinsa guda goma suka sauko, suna tafiya cike da annashuwa da murna, suna dauke da kayan kyaututtuka na alfarma domin tarbar dansa da ya cika shekara goma sha biyar lafiya!

Da isarsu tsakiyar tsibirin, sai suka ga qasar da ke saman kofar a birkice take ba kamar yadda suka barta ba. Tsohon ya cika da mamaki, bayin suka kakkabe qasar da gaggawa suka bude marfin katakon suka shiga ciki.

Ba a jima da shigarsu ba, sai wata gigitacciyar kururuwa da kukan kade-kade suka barke daga kasan ramin!

Kukan ya cika dukkan tsibirin da amo mai ban firgici!

Jim kadan sai ga bayin nan suka fito suna jan gawar wannan matashi a lullube da farin alharini yana zubar da jini, wukata tana kafe a qirjinsa!

A bayansu kuwa sai ga tsohon attajirin nan, bayinsa biyu suna riqe da shi domin ya suma ya fadi a kasa baya numfashi!

Tsohon bai farfado daga sumarsa ba sai da yamma ta kusa yi. Ko da ya bude idonsa ya ga gawar dansa guda daya tilo a kwance a gabansa, sai ya saki wata qaqqarfar qara, ya riqa dukan fuskarsa da kansa, yana cire gemunsa da gashin kansa, ya riqa zuba toka a kansa yana rera wannan doguwar qasidar kuka mai ban tausayi yana cewa:

Zuciyata ta tsage da radadin rabuwa da masoyana,

Kuma qorama biyu na hawaye suna kwarara daga idanuna!

Tare da shi dukkan fatana da burina suka tafi—kash yaya zanyi!

Wace dabara ce ta rage mani da zan fada ko na aikata?

Da ma ban taba zuba idanuna a kan fuskarsa ba,

Wace mafita ce idan hanyoyin rayuwa suka qunqe?

Wane magani zai kwantar da radadina a lokacin da shauqi,

Ke ruruwa tamkar garwashi a cikin hanjina da zuciyata?

Da ma na taka tafarkin mutuwa a tare da shi tun dā,

Da wannan mummunan bugun rabuwa bai taba samunmu ba!

Ina roqon Allah Mai Jinqai Ya nuna mani tausayinsa,

Ya hada rayukanmu kada Ya sake raba mu har abada!

Yaya albarkarmu ta kasance yayin da muke zaune a qarqashin rufi guda,

Muna rungume da juna cikin nishadi ba tare da tunanin baqin ciki ba!

Har sai da qaddara ta harbe mu da kibiyar rabuwa,

Kash wane ne zai iya daurewa irin wannan ciwo na rabuwa?

Kibiyar mutuwa ta kakkabe lu'u-lu'un wannan zamani,

Wanda safe ta ganshi a matsayin mafi kyawun abin haskawa!

Na yi kuka yayin da halinsa ke magana yana cewa:

Kash ya dana, da ma mutuwa ta jinkirta kwananka!

Wacece mafi sauqin hanya da zan bi domin na hadu da kai,

Ya dana wanda nake son fansar raina domin shi?

Idan na kira shi da rana—a'a! Rana tana faduwa;

Idan na kira shi da wata—a'a! Wata yana disashewa!

Kash ga wannan mummunar musiba da hukuncin kwanaki,

Wurin da kake a zuciyata babu wata soyayya da zata taba maye shi!

Mahaifinka yana kallonka a rude amma ya fidda rai,

Da cewa dabara ko hikima zata iya kaucewa qaddara!

Wani mugun ido ne ya jefa dalasuminsa a kanka a yau,

Kuma mummunan tozarci ya auku kamar yadda aka qaddara!

Yana gama wannan waqa, sai tsohon ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya mai zafi: 'Hah!' Ruhinsa ya fita daga jikinsa, ya fadi a kan gawar dansa ya mutu a nan take saboda tsananin zafin ciwon zuciya!

Bayin suka fashe da wani sabon kuka da salati! Suka dauki gawar maigidansu da gawar dansa suka zuba su a cikin jirgin ruwa, suka kwashe dukkan kayan da ke dakin qarqashin qasa suka shigar da su cikin jirgi, sannan suka tada jirgin suka kama hanya suka bace a cikin teku!

Ina kan bishiya ina kallon wannan mummunan al'amari, hawaye yana kwarara daga idanuna har sai da rana ta fadi!

Na sauko daga kan bishiya na tafi cikin wannan daki na karkashin qasa na zauna a wurin da yaron ya mutu, na rera wasu baitoci cike da kuka ina cewa:

Ina kallon gurabun takunsu, ina kuka da zafin radadi,

A kan kango da kufan gidansu nake kuka da shauqi!

Ina roqon Wanda Ya qaddara rabuwarsu a wannan wuri,

Wata rana Ya azurta mu da baiwar saduwa da aminci!

Na kwashe wata guda cif ina kuka da zama a cikin wannan daki ina roqon gafarar Allah.

Bayan wata guda, wata rana na fito bakin teku domin na sha iska, sai na ga wani abin al'ajabi: na ga cewa ruwan tekun ya ja da baya sosai har ya qafe, qasa ta bushe ta bayyana tsakanin tsibirin da babban tudu na qasa!

Na yi murna qwarai na rera wasu baitoci ina cewa:

Wataqila qaddarata zata juyo da linzaminta da alheri,

Zamani ya kawo natsuwa ko da an san shi da kishi!

Ya ciyar da fatana gaba, ya biya mani dukkan bukatata,

Ya mayar mani da kwanakin qunci su zama kwanakin alheri!

Na zura kafafuna a cikin yashi na shiga tafiya a kan busashen kasan tekun har sai da na tsallaka zuwa babban tudu!

Na yi ta tafiya a cikin hamada har tsawon kwanaki da yawa. Wata rana da yamma, sai na hango wani babban haske mai sheqi daga nesa tamkar wuta tana ci!

Na nufo wurin cike da zumudi, amma da na matso kusa sai na ga ashe ba wuta ba ce: wata katafariyar fada ce mai hawa-hawa da aka kera kofofinta da jajayen tagulla masu sheqi, wadanda ke haskawa idan hasken rana ya doke su!

Na zauna a bakin babbar kofar fadar domin na huta. Ban jima da zama ba, sai ga wasu matasa kyawawa guda goma (10) suka fito daga cikin fadar!

Kowannensu sanye yake da tufafin alfarma na sarauta, amma abin da ya fi ba ni matuqar mamaki: KOWANNENSU IDON DAMANSA A TSIYAYE YAKE SUMUL! Kowannensu yana gani da ido guda daya kacal tamkar an cire idon da wuka! A tare da su kuma akwai wani dattijo tsoho mai matuqar kwarjini.

Ko da suka ganni, suka yi mani sallama suka tambaye ni labarina. Na kwashe dukkan abin da ya same ni tun daga Dutsen Qarfe har zuwa kisan saurayin qarkashin qasa na fada musu.

Suka cika da mamaki suka tausaya mani, suka shigar da ni cikin wannan katafariyar fada. Na ga falon yana dauke da shimfidu guda goma sha daya na shudayen tufafi na makoki.

Muka zauna, tsohon nan ya kawo mana abinci da ruwan sha muka ci muka qoshi.

Amma yayin da dare ya raba, sai matasan nan guda goma suka kalli tsohon suka ce: 'Ya shugabanmu, lokacin al'adarmu ya yi! Kawo mana abin da aka saba!'

Tsohon ya miqe ya shiga wani daki, ya fito dauke da kwanoni guda goma a kansa, kowanne a lullube da shudin kyalle, a saman kowane kwano kuma akwai kyandir yana ci.

Tsohon ya ajiye kwanonin a gaban kowannen matasan nan, sannan ya yaye mayafan: ashe babu komai a cikin kwanonin face toka, da baqin gawayi da baqin kasko!

Nan take wadannan matasa guda goma suka tattare hannayen rigarsu, suka sa hannu a cikin tokar nan da kaskon, suka shiga shafawa a fuskokinsu da kawunansu har fuskokinsu suka yi baqi wulik! Suka shiga dukan qirjinsu da goshinsu suna kuka mara misali suna cewa:

'Mun kasance a cikin aminci da daula amma son zuciyarmu da rashin haqurinmu sun jefa mu a cikin wannan tozarci da makanta!'

Suka yi ta wannan kuka da makoki har asuba ta kusa yi, sannan tsohon ya kawo musu ruwa suka wanke fuskokinsu suka sauya tufafi suka kwanta barci!

Na kwashe wata guda cif ina zama tare da su, kuma a kowace rana da daddare sai sun aikata wannan makoki na shafa toka a fuska!

A qarshe dai na kasa jurewa! Na tashi tsaye a gabansu na ce: 'Don girman Allah ku bayyana mani sirrin abin da ya sa kuke shafa wannan toka a fuska, da kuma abin da ya sa dukkaninku kuke da ido daya daya!'

Matasan suka dube ni cike da damuwa suka ce: 'Ya kai wannan saurayi, ka daina wannan tambaya! Domin idan har muka gaya maka sirrin nan, to kai ma zaka rasa idonka na dama ka zama mai ido daya kamar yadda muke! Gara ka zauna a yadda kake mu kuma mu tafi, domin mawaqi ya ce:

Gara ka zauna a yadda kake mu kuma mu tafi,

Domin abin da ido bai gani ba, zuciya ba za ta yi kuka a kansa ba!'

Na ce da su: 'Ko da zan rasa idona ba zan taba barinku ba har sai na ji wannan sirri kuma na je wurin da kuka je!'

Ganin cewa na dage firitsitsi, sai suka ce: 'To ka sani cewa idan ka tafi baka da sauran dawowa wurinmu har abada!'

Nan take suka kawo wani babban rago mai kiba suka yanka shi, suka fede fatarsa tas.

Suka miqa mani wata wuka mai kaifi suka ce mani: 'Shiga cikin wannan fatar rago ka shimfida kanka a ciki, mu kuma za mu dinke bakin fatar da zare ta yadda zaka zama tamkar gawar rago!

Jim kadan wani gagarumin tsuntsu mai matuqar girma da tsoro mai suna TSUNTSUN RUKU zai sauko daga sama! Zai dauka cewa gawar rago ce, zai cafke ka da manyan akafansa ya luluka sama da kai har zuwa qololuwar wani babban tsauni mai hadari da babu wanda zai iya hawa shi da kafafunsa!

Da zarar ya sauka a kan tsaunin, sai ka zaro wukarka ka yanke zaren fatar ragon ka fito kana daka masa tsawa! Tsuntsun zai tsorata ya tashi ya bar ka a can! Daga nan sai ka yi tafiyar rabin yini zaka ga wata katafariyar fada ta zinare mai kofofi dari! Ka shiga ciki zaka cika burinka, kuma daga nan ne dukkanmu muka rasa idanunmu!'

Na yi matuqar murna da wannan bayani! Na shiga cikin fatar ragon, suka dinke ni tamau!

Bamu jima da yin haka ba, sai muka ji wata gigitacciyar qara a sararin samaniya!

Duniya ta yi duhu tamkar hadari ya taso—ashe TSUNTSUN RUKU ne ya bude fukafukansa masu girman gaske ya rufe hasken rana!

Tsuntsun ya sauko qasa, ya cusa manyan akafansa masu kaifi a cikin fatar ragon da nake ciki, ya daga ni da dukkan qarfinsa ya luluka sama zuwa cikin giza-gizai!..."

A daidai wannan gaba, sai hasken alfijir ya fara ketowa a sararin samaniya, Shahrazad ta ga safiya ta yi, sai ta dakata da zancenta mai dadin sauraro ta yi shiru!

Dunyazad ta dube ta da matuqar sha'awa da shauqi ta ce: "Kai ya yayata! Lallai wannan labari ya cika da zakin kunne, da dadi, da cikar nishadi da ban al'ajabi mara misali!"

Shahrazad ta yi murmushi ta dube ta ta ce: "Ai wannan ba komai ba ne idan aka kwatanta shi da labarin da zan fada muku a dare mai zuwa, idan har Allah Ya raya ni kuma wannan babban Sarki ya qyale ni?"

Ko da Sarki Shahriyar ya ji wannan batu, sai ya ce a ransa: "Wallahi ba zan kashe ta a yau ba, sai na ji sauran wannan kyakkyawan labari mai ban mamaki!"

Wayewar gari ke da wuya, Sarki ya fita fada ya gudanar da al'amuran mulki yana bayar da umarni da hani har dare ya sake rufowa, shi kuwa babban Waziri ya koma gida fuskarsa cike da farin ciki da godiyar Allah da ya ga 'yarsa tana ci gaba da rayuwa cikin aminci!

(A nan muka kawo qarshen DARE NA GOMA SHA BIYAR da kuma BABI NA GOMA SHA TARA cif!)

====================================================================