DARE DUBU DA DAYA 1001 Mujalladi na Daya 1

BABI NA ASHIRIN DA UKU (23): HIKAYAR TUFFA UKU DA WAZIRI JA'AFARU

by @shuraih99

====================================================================

DARE DUBU DA DAYA (ALF LAILA WA LAILA)

BABI NA ASHIRIN DA UKU (23): HIKAYAR TUFFA UKU DA WAZIRI JA'AFARU

[DARE NA GOMA SHA TARA]

Fassarar: Shuraihu Usman

====================================================================

A babi na ashirin da biyu idan mai karatu bai manta ba, mun tsaya a inda budurwa Amina mai kula da qofa ta ba wa Amirul Muminina Haruna Rasheed labarin aurenta da dukan da mijinta ya yi mata da bulalar itacen safarjal har sai da ta suma saboda cizon da saurayi attajiri ya yi mata a kumatu, da kuma yadda 'yan mata ukun nan suka sake haduwa a gida daya a karshen DARE NA GOMA SHA TAKWAS. To yanzu bari mu ji yadda Halifa Haruna Rasheed ya warware dukkan matsalolin wadannan 'yan mata da Kalandarawa, da kuma yadda wani sabon labari mai ban tsoro da al'ajabi na Tuffa Uku ya fara a cikin wannan DARE NA GOMA SHA TARA.

--- DARE NA GOMA SHA TARA ---

Da asuba ta yi gari ya waye, Sarki Shahriyar ya fita fada ya gudanar da al'amuran mulki ba tare da ya ambaci batun kisan Shahrazad ba. Babban Waziri ya koma gida yana godiya ga Allah da ya ga 'yarsa tana ci gaba da rayuwa cikin aminci.

Da dare ya tsala a cikin wannan DARE NA GOMA SHA TARA, Sarki Shahriyar ya shigo daki ya kwanta da Shahrazad. Bayan ya gama biyan bukatarsa, sai qanwarta Dunyazad ta tashi daga qasan shimfida ta ce:

"Ya yayata, idan ba ki fara barci ba, don girman Allah ki qarasa mana labarin abin da ya faru a fadar Sarki Haruna Rasheed da wadannan 'yan mata da Kalandarawa, kuma ki fara mana wani sabon labari mai zaki domin mu debe kewa a cikin wannan dare!"

Shahrazad ta duba wajen Sarki Shahriyar cikin ladabi ta ce: "Zan qarasa labarin sannan in kawo sabo idan har wannan babban Sarki mai daraja ya ba ni izini!" Sarki ya ce: "Fadi ina saurarenki!"

Nan take Shahrazad ta gyara zama ta ci gaba da ba da wannan kyakkyawan labari a cikin wannan DARE NA GOMA SHA TARA kamar haka:

"Amirul Muminina Haruna Rasheed ya ba da umarni aka dauki takarda da tawada aka rubuta dukkan labaran wadannan 'yan'uwa mata guda uku da Kalandarawa guda uku, aka adana su a cikin rumbun taskar tarihin masarautarsa domin zama abin tunawa da koyon darasi ga na baya.

Daga nan sai Halifa ya juya wajen shugabar matayen nan mai suna Zubaida, ya ce da ita: 'Shin kin san inda wannan Jinniya take wadda ta mayar da 'yan'uwanki mata wadannan karnuka?'

Zubaida ta amsa da cewa: 'Ya Sarkin Muminai, sa'ad da ta mayar da ni gida ta ba ni wani zaren gashin kanta, ta ce da ni: a duk lokacin da kike son ganina, ki kona 'yan gashin nan guda biyu a cikin wuta, to nan take zan bayyana a gabanki ko da kuwa ina can bayan dutsen Qaf!'

Halifa ya ce: 'Maza kawo wannan gashi nan!' Zubaida ta kawo gashin, Halifa ya dauki dukkan zaren gashin ya jefa shi a cikin wuta.

Da zarar qamshin konewar wannan gashi ya bazu a cikin zauren fada, sai fadar ta shiga girgiza tana karkarwa! Dukkan mutanen da ke wurin suka ji wata gigitacciyar qara mai rugugi tamkar tsawa, da motsin fukafukai masu tashi a sama, sai ga wannan Jinniya wadda ta kasance macijiya a da ta bayyana a tsaye a gaban Halifa!

Kuma da yake ita Musulma ce mai tsoron Allah, sai ta yi masa sallama ta ce: 'Amincin Allah ya tabbata a gare ka ya Halifan Allah a bayan qasa!'

Halifa ya amsa mata ya ce: 'Kema aminci da rahamar Allah su tabbata a gareki.!'

Jinniya ta ce: 'Ka sani ya Sarkin Muminai, hakika wannan budurwa wato Zubaida ta shuka mani irin alheri wanda ba zan taba iya biyanta shi ba, domin ta kubutar da ni daga mutuwa ta kuma kashe maqiyina! Na ga irin tozarcin da 'yan'uwanta mata biyu suka yi mata, shi ya sa na dauki fansa a kansu. Da farko na yi niyyar in kashe su ne gaba daya, amma na ji tsoron kada hakan ya bata mata rai, shi ya sa na mayar da su baqaqen karnuka. To amma idan kana son a mayar da su mutane ya Sarkin Muminai, to zan sake su domin faranta maka da ita, domin ni muminar Musulma ce!'

Halifa ya ce mata: 'Mayar da su zuwa asalin surarsu ta mutane! Daga nan kuma sai mu duba shari'ar wannan budurwa Amina mai dauke da tabon bulala a jikinta domin mu binciki al'amarinta; idan gaskiyar labarinta ta tabbata, to lallai zan daukar mata fansa a kan duk wanda ya zalunce ta!'

Jinniya ta ce: 'Ya Amirul Muminina, nan take zan mayar da karnukan nan zuwa mutane, kuma zan tona maka : mutumin da ya aikata wannan zalunci ga wannan baiwar Allah ya doke ta da bulala ya kwace dukiyarta; kuma mutumin nan shi ne mafi kusa da kai a cikin dukkan bil'adama!'

Tana fadin haka, sai ta dauki wani kofi na ruwa, ta tofa wani addu'a a cikinsa da wasu kalmomi da ba a gane ma'anarsu ba, sannan ta yayyafa wannan ruwa a fuskokin wadannan baqaqen karnuka guda biyu, tana mai cewa: 'Ku koma zuwa ga asalin surarku ta 'yan Adam!'

Nan take karnukan suka bace, sai ga su sun koma kyawawan 'yan mata kamar yadda suke a asali! Suka zube qasa suna godiya ga Mahaliccinsu da Ya kubutar da su daga wannan azaba.

Daga nan sai Jinniya ta dubi Halifa ta ce: 'Ya Amirul Muminina, hakika wanda ya zana wa wannan budurwa Amina wadannan bulaloli a jikinta ba wani bane face danka Al-Amin, dan'uwan Al-Ma'amun! Ya ji labarin tsananin kyanta da cikar zatinta, sai ya yi amfani da dabarar masoya ya aure ta a kan ka'idar shari'a, sannan ya yi mata wannan hukunci na duka. To amma a gaskiya ba za a daura laifi a kansa ba, domin ya gindaya mata sharadi mai qarfi ya kuma karbi rantsuwarta a kan Alqur'ani cewa kada ta kalli wani namiji; amma ta karya rantsuwarta ta karkata zuwa ga wani daban! Ya yi niyyar kashe ta ne, amma ya ji tsoron Allah Madaukaki ya wadatu da yi mata wannan duka kamar yadda kuka gani, ya mayar da ita tsohon gidanta. Wannan shi ne asalin labarin budurwa ta biyu, kuma Allah Shi ne Mafi Sani!'

Ko da Halifa ya ji wadannan kalamai daga bakin Jinniya, ya gano cewa dansa ne ya aikata wannan abu, sai ya cika da tsananin mamaki mara misali, ya ce: 'Godiya ta tabbata ga Allah Madaukaki, Mai Iko da Kowa, Wanda Ya nuna mini tsananin rahamarSa, Ya ba ni ikon kubutar da wadannan 'yan mata daga sihiri da azaba, Ya kuma bayyana mani boyayyen sirrin labarin wannan budurwa! To yanzu wallahi za mu yi wani aiki na alheri wanda za a rinka ambatonsa a tarihi bayan ba ma nan!'

Nan take Halifa ya aika aka kira masa dansa Al-Amin, ya tambaye shi game da labarin Amina mai kula da qofa; Al-Amin ya fadi gaskiyar lamari a sarari a gaban mahaifinsa ba tare da boye komai ba.

Halifa ya ba da umarni aka kira Alqalai da shaidunsu, da Kalandarawa guda uku, da kuma shugabar matayen wato Zubaida tare da 'yan'uwanta mata biyu da aka karya musu sihiri.

A nan take Halifa ya daura auren 'yan'uwa mata ukun nan ga wadannan Kalandarawa guda uku wadanda ya tabbatar da cewa su 'ya'yan sarakuna ne na gaskiya! Ya nada su a matsayin manyan amintattun fadawansa a fada, ya yanka musu albashi da dukkan abin da suke buqata na sutura da abinci, ya ba su manyan gidaje na alfarma a cikin babban birnin Bagadaza.

Ita kuwa Amina mai kula da qofa, Halifa ya mayar da ita ga dansa Al-Amin, aka sake sabunta daurin aurensu a tsakaninsu cikin girmamawa, ya ba ta dukiya mai dimbin yawa, ya kuma ba da umarni aka sake gina mata wannan fada ta zama mafi kyau da qawa fiye da yadda take a da!

Shi kuwa Halifa da kansa, sai ya auri budurwa ta uku, wato Fahima mai saye-saye, ya kwana da ita a wannan dare cikin nishadi da jin dadi. Washegari kuma ya ware mata wani katafaren sashe na alfarma a cikin fadar masarautarsa, ya sanya mata kuyangi da bayi na musamman da zasu rinka yi mata hidima, tare da kayyade mata kudaden kashewa na kowace rana.

Dukkan mutanen birnin Bagadaza suka yi matuqar mamaki da yaba wa karamcin Halifansu, da adalcinsa, da tsantsar hikimarsa ta sarauta; shi kuma Halifa bai manta ba ya sa aka tattara dukkan wadannan labarai aka rubuta su a cikin manyan littattafan tarihin daular Abbasiyyawa!"

Sa'ad da Shahrazad ta dakata da bayar da wannan labari, sai qanwarta Dunyazad ta saki wani nishi na shauqi ta ce: "Ya 'yar'uwata, wallahi wannan labari ya cika da dadi da ban sha'awa mara misali! Ban taba jin labari mai kayatarwa irinsa ba a duniya! Amma ina roqonki don girman Allah da ki ba mu wani sabon labari domin mu kashe ragowar sa'o'in wannan dare da muke a farke!"

Shahrazad ta yi murmushi ta ce: "Da so da kauna da matuqar murna zan ba da shi idan har wannan babban Sarki mai daraja ya ba ni izini!"

Sarki Shahriyar ya dube ta cikin shauqi ya ce: "Fadi labarinki, kuma ki fada mana shi cikin hanzari!"

Nan take Shahrazad ta gyara zama ta fara ba da wannan sabon labari a cikin wannan DARE NA GOMA SHA TARA kamar haka:

» HIKAYAR TUFFA UKU DA WAZIRI JA'AFARU

"An ruwaito ya kai wannan babban Sarki mai daukaka da cikar daraja, cewa a can zamanin daular Abbasiyyawa, wata rana da daddare Amirul Muminina Haruna Rasheed ya kira babban Wazirinsa Ja'afaru ya ce masa:

'Ina son mu fita cikin dare mu shiga cikin unguwanni da lungunan birnin Bagadaza, domin mu binciki halin da talakawa ke ciki game da shugabanni da alkalai da ke kula da al'amuransu; duk wanda suka koka a kansa sai mu sauke shi daga mukaminsa, duk wanda kuma suka yaba da shi sai mu kara masa girma da daukaka!'

Waziri Ja'afaru ya durqusa ya ce: 'Na ji kuma na yi biyayya ya shugabana!'

Nan take Halifa ya canza tufafinsa zuwa na talakawa, shi da Wazirinsa Ja'afaru da babban Sarkin Yakinsa Masrur, suka fito cikin duhun dare suka shiga yawo a cikin tituna da kasuwannin birnin Bagadaza.

Suna cikin tafiya a cikin wani qaramin lungu mai qunci, sai suka yi arba da wani tsoho tukuf mai yawan shekaru! Tsohon nan yana dauke da komar kamun kifi da wani kwando na sanya kananan kifi a kansa, a hannunsa kuma yana riqe da sandar dogaro; yana tafiya a hankali cikin kasala da nishi yana rera wadannan baituka na kuka da bakin ciki:

Suna ce mani: Kana haskawa a matsayin haske ga bil'adama,

Tare da iliminka tamkar daren da cikakken wata ke haskaka shi!

Sai na amsa musu: Ku dakata da barkwancinku da zolayarku;

In babu sa'a da rabo meye amfanin ilimi? Bawan Allah ne marar galihu!

Idan har zasu kai ni jingina tare da ilimina a aljihuna,

Da litattafaina na karatu da qalamina na rubutu,

Ko abincin yini guda ba za su iya karbata a matsayin jingina ba;

Tamkar neman biyan bashi ne a ranar hisabi da tashin qiyama!

Lallai yaya talaka zai yi a cikin wannan qunci na rayuwa,

Tare da rayuwar qasqanci da matsananciyar buqata:

A lokacin zafi ya gaza samun abincin da zai ci;

A lokacin sanyi kuma murhun wuta shi kadai ne abin farin cikinsa!

Karnukan titi suna tararsa da haushi da cizo,

Kowane wawa kuma yana tarbarsa da zagi da hantara!

Idan ya daga muryarsa yana kukan rashin adalcin da aka yi masa,

Babu mai tausaya masa ko sauraronsa, ko da kuwa yana kan gaskiya;

Yayin da qunci da masifu irin wadannan suka dabaibaye shi,

To mafi alherin masaukinsa shi ne kwanciya a cikin qabari!

Ko da Halifa Haruna Rasheed ya ji wadannan baituka masu sosa zuciya, sai ya juya wajen Waziri Ja'afaru ya ce masa: 'Duba wannan talaka ka saurari baitocinsa, lallai suna nuni ne a kan tsananin buqatarsa da kuncin da yake ciki!'

Daga nan sai Halifa ya matso kusa da tsohon ya ce masa: 'Ya kai wannan dattijo, wace irin sana'a kake yi?'

Tsohon ya amsa da cewa: 'Ya shugabana, ni masunci ne mai iyali da 'ya'ya da nake ciyarwa; na fita tun tsakar rana har zuwa wannan sa'a ta dare amma Allah bai qaddara mani samun ko da kifi guda daya ba da zan ciyar da iyalina! Ba ni da ko da abin da zan bayar jingina domin in sayi abincin dare; na tsani rayuwata kuma mutuwa nake buri a yanzu!'

Halifa ya dube shi da tausayi ya ce: 'Shin zaka iya komawa tare da mu zuwa gabar kogin Dijla ka jefa komarka a kan sa'ata da rabona, kuma duk abin da ya fito a cikin komar zan saya daga gare ka a kan dinare dari cif na zinare?'

Ko da tsohon masunci ya ji wannan batu, sai ya cika da matuqar murna ya ce: 'A kan kaina da idona! Zan koma tare da ku!'

Suka koma tare da shi zuwa gabar kogin Dijla. Masuncin ya jefa komarsa a cikin ruwa, suka jira na dan wani lokaci; daga nan ya shiga jawo igiyar komar a hankali har ya janyo ta zuwa bakin gaba.

Sai ga wani babban akwati mai nauyin gaske wanda aka kulle shi da kwado ya fito a cikin komar!

Halifa ya duba akwatin ya daga shi, ya ga yana da matuqar nauyi. Nan take ya zaro dinare dari biyu cif na zinare ya miqa wa tsohon masunci ya sallame shi ya kama gabansa cikin farin ciki!

Masrur da taimakon Halifa suka dauki akwatin a kafadunsu suka nufi fada kai tsaye. Suka ajiye shi a tsakiyar daki, aka kunna kyandirori a gefe da gefe. Waziri Ja'afaru da Masrur suka fasa kwadon akwatin suka bude shi, sai suka tarar da wani babban kwando na ganyen dabino da aka daure shi da jan zare.

Suka yanke zaren suka bude kwandon, sai suka ga wani yanki na kafet a ciki; suka cire kafet din, a qarqashinsa kuma suka ga mayafin mace da aka ninke shi gida hudu; suka cire mayafin, sai suka yi arba da wani mummunan abu mai ban firgici a kasan akwatin!

Wata kyakkyawar budurwa ce matashiya, mai tsananin kyau da haske tamkar danyar azurfa, wadda aka kashe ta aka gutsattsura namanta zuwa gunduwa goma sha tara cif!

Ko da Halifa Harunar Rasheed ya kalli wannan gawa, sai ya saki wani gigitaccen kuka yana cewa: 'Wayyo ni Allah!' Hawaye suka shiga kwarara daga idanuwansa a kan kumatunsa!

Ya juya wajen Waziri Ja'afaru a fusace ya daka masa tsawa ya ce: 'Ya kai wannan mugun Waziri! Shin a zamanin mulkina za a kashe bayin Allah a gutsattsura su a jefa a cikin kogi su zama nauyi da alhaki a wuyana a ranar hisabi da tashin qiyama? Wallahi tallahi dole ne mu daukar wa wannan mata fansa a kan wanda ya kashe ta, kuma za a kashe shi da mafi munin kisa!'

Sannan Halifa ya qara da cewa da babbar murya: 'Na rantse da girman zuri'ar Abbasiyyawa da na fito daga cikinta, idan har baka kawo mani wanda ya kashe wannan budurwa ba domin mu yi mata adalci a kansa, to wallahi zan sa a rataye ka a bakin qofar fadata, kai da mutane arba'in cif daga cikin 'yan'uwanka da danginka na Barmakawa a gefenka!'

Halifa ya cika da tsananin fushi da kuna. Waziri Ja'afaru ya durqusa cikin tsoro ya ce: 'Ka ba ni wa'adin kwanaki uku ya shugabana!' Halifa ya ce: 'Na ba ka wannan wa'adi!'

Waziri Ja'afaru ya fito daga fada ya nufi gidansa yana cikin tsananin bakin ciki da tashin hankali, yana cewa a ransa: 'Ta yaya zan iya gano wanda ya kashe wannan budurwa a cikin wannan katafaren birni domin in kawo shi gaban Halifa? Idan kuma na kawo wani daban wanda ba shi ne ya kashe ta ba, Allah zai kama ni da alhakin kisan ran da ba shi da laifi! Wallahi ban san abin da zan yi ba!'

Ja'afaru ya zauna a gidansa yana juyayi har tsawon kwanaki uku ba tare da ya fita ba. A rana ta hudu, sai Halifa ya aiko babban dogarinsa domin ya tafi da Ja'afaru zuwa fada.

Da Ja'afaru ya shiga gaban Halifa, sai Halifa ya dube shi da idanuwan fushi ya ce: 'Ina wanda ya kashe wannan budurwa?'

Ja'afaru ya amsa da cewa: 'Ya Sarkin Muminai, shin ni mai kula da mutanen da aka kashe ne a asirce da zan san wanda ya kashe ta a cikin duhun dare?'

Halifa ya fusata qololuwar fusata da jin wannan amsa! Nan take ya ba da umarni a kafa maratayi a bakin babbar qofar fada domin rataye Ja'afaru, kuma ya sa mai shela ya fita cikin titunan Bagadaza yana shela da babbar murya yana cewa:

'Duk wanda yake son ganin yadda za a rataye Ja'afaru Barmaki, babban Wazirin Halifa, tare da mutane arba'in cif daga cikin 'yan'uwansa da danginsa na Barmakawa a bakin qofar fada, to ya zo ya kalla!'

Duk mutanen birnin Bagadaza daga kowane lungu da saqo suka yi cincirindo suka fito domin ganin kisan Ja'afaru da danginsa, alhali ba su san ainihin dalilin da ya sa za a kashe su ba!

Aka kafa maratayan rataya, aka tsayar da Waziri Ja'afaru da 'yan'uwansa Barmakawa a qarqashin igiyoyin rataya a shirye domin aiwatar da hukuncin kisa!

Yayin da dukkan idanuwan jama'a ke jiran alamar Halifa domin a zare igiya, mutane kuma suna ta kuka saboda tausayin Ja'afaru da 'yan'uwansa Barmakawa, can katsam! Sai ga wani kyakkyawan saurayi matashi mai kyan fuska da tufafin alfarma, mai haske tamkar wata mai zuba ruwan haske, mai baqaqen idanuwa masu kyalli, da goshi fari fat tamkar furen gona, da kumatun da suka yi ja tamkar furen wardi, da 'yar suma a kumatunsa inda gemu ke fita, da wani baqin tambari na miski a gefen fuskarsa; ya shiga kutsawa ta tsakiyar taron jama'a da hanzari har ya tsaya a gaban Waziri Ja'afaru!

Saurayin ya kalli Ja'afaru ya ce da shi: 'Aminci ya tabbata a gare ka daga wannan qunci ya shugaban amirori kuma mafakar talakawa! Ni ne mutumin da ya kashe wannan mata da kuka samu a cikin akwati! Saboda haka ka rataye ni a maimakonta ka daukar mata fansa a kaina!'

Ko da Waziri Ja'afaru ya ji wannan furuci daga bakin saurayin, sai ya yi murna da kubutar ransa da ta danginsa, amma kuma a lokaci guda ya yi matuqar bakin ciki da tausayin wannan kyakkyawan saurayi!

Suna cikin wannan magana, can katsam sai ga wani tsoho dattijo mai yawan shekaru ya shiga kutsawa ta cikin taron mutane da gudu har ya isa wajen Ja'afaru da wannan saurayi!

Tsohon ya yi gaisuwa sannan ya ce da babbar murya: 'Kada ka yarda da kalaman wannan saurayi ya kai wannan Waziri mai daraja! Wallahi babu wanda ya kashe wannan budurwa face ni kadai! Ka dauki fansarta a kaina a wannan sa'a!'

Saurayin ya juya wajen tsohon ya ce: 'Ya Waziri, wannan tsoho ne mai tsananin tsufa wanda bai san abin da yake fada ba! Ni ne na kashe ta, ka dauki fansa a kaina!'

Tsohon ya daka masa tsawa ya ce: 'Ya dana, kai matashi ne saurayi kuma ya kamata ka rayu a duniya; ni kuwa tsoho ne da na qoshi da duniya na kosa in tafi! Ni ne na kashe ta ba shi ba!'

Waziri Ja'afaru ya cika da tsananin mamaki, ya ce a ransa: 'Wallahi kisan daya daga cikinsu ya fi mani sauqi fiye da kisan kaina da na 'yan'uwana Barmakawa!'

Nan take Ja'afaru ya dakatar da kisa, ya kama hannun saurayin da na tsohon ya shiga da su fada a gaban Amirul Muminina Harunar Rasheed.

Ja'afaru ya zube ya ce: 'Ya Sarkin Muminai! Ga wanda ya kashe wannan budurwa na kawo shi gabanka!'

Halifa ya dube su ya ce: 'Ina wanda ya kashe ta a cikinsu?'

Saurayin ya ce: 'Ni ne ya Amirul Muminina!' Tsohon kuma ya ce: 'A'a, ni ne na kashe ta ya shugabana!'

Halifa ya dube su cikin mamaki ya ce wa Ja'afaru: 'Dauki su duka biyun ka tafi ka rataye su!'

Amma Ja'afaru ya ce: 'Ya shugabana, idan har daya ne kacal ya kashe ta, to yaya zai dace a kashe mutum biyu a kan kisan mutum daya?'

Halifa ya juya wajen saurayin ya dube shi da kyau ya ce masa: 'Fada mani gaskiya, me ya sa kuka kashe wannan baiwar Allah, kuma me ya sa kake ikirarin kisan alhali wannan tsoho ma yana ikirari?'

Saurayin ya sunkuyar da kansa ya fashe da kuka sannan ya ce:

'Ya Sarkin Muminai, ka sani fa wannan budurwa da kuka samu a cikin akwati, matata ce kuma 'yar baffana, 'yar wannan tsoho da kake gani a gabanka, domin shi ne baffana kuma mahaifinta! Na aure ta a matsayin budurwa, Allah Ya albarkace mu da 'ya'ya maza guda biyu tare da ita. Ina matuqar qaunarta kuma ita ma tana sona qwarai da gaske, ban taba ganin wani aibi a tare da ita ba a dukkan rayuwar aurenmu!

Kusan wata guda da ya wuce, sai ta kamu da wata 'yar rashin lafiya mai tsanani. Na yi ta jinyarta da kowane irin magani har sai da zazzabin ya sauka daga jikinta.

Wata rana tana murmurewa daga rashin lafiyar, sai na ce mata: "Mene ne kike marmarin ci a yanzu ya abin qaunata?"

Ta dube ni da raunanniyar murya ta ce: "Marmarin tuffa nake yi! Ina matuqar son in ci tuffa guda daya kafin in mutu, ko kuwa in shaki qamshinta!"

Nan take na tashi na fita cikin gari na nufi dukkan shagunan 'ya'yan itatuwa a fadin birnin Bagadaza; amma ko da a kan dinare guda na nemi tuffa daya ban samu ba! Na dawo gida ina mai tsananin bakin ciki na ce mata: "Ya 'yar baffana, wallahi na duba ko'ina ban samu ko da kwaya daya ba!"

Ganin ban samu ba sai jikinta ya sake yin sanyi, rashin lafiyarta ta qaru qwarai a wannan dare, hankalina ya tashi qololuwar tashi saboda tsoron kada ta mutu!

Da asuba ta yi gari ya waye, sai na sake fita na zagaya dukkan gonaki da lambunan da ke wajen birnin Bagadaza daya bayan daya, amma ban sami ko da kwayar tuffa daya ba.

A qarshe sai na hadu da wani tsohon mai kula da lambu, na tambaye shi game da tuffa, sai ya ce mani: "Ya dana! Wannan 'ya'yan itace abu ne mai matuqar wuya da qaranci a wannan zamani a qasarmu, kuma a yanzu ba za ka taba samunsa ba a ko'ina face a cikin babban lambun Amirul Muminina da ke birnin Basra, inda mai kula da lambun yake ajiye shi na musamman domin abincin Halifa!"

Ko da na ji haka, sai na dawo gida zuciyata cike da damuwa; to amma saboda tsananin soyayya da tausayin matata, sai na yanke shawarar yin wannan doguwar tafiya domin neman abin da take so!

Na yi shiri na kama hanya na nufi birnin Basra. Na kwashe kwanaki goma sha biyar cif ina tafiya a kan hanya zuwa da dawowa! Na isa lambun Halifa a Basra, na sayi tuffa guda uku cif a wurin mai lambun a kan dinare uku na zinare!

Na taho da su cikin hanzari har na shigo gida na ajiye su a gaban matata. To amma a wannan lokaci zazzabinta ya riga ya tsananta sosai, ba ta ma damu da tuffar ba, ta bar su a ajiye a gefen shimfidarta; ta kwashe kwanaki goma cif tana fama da wannan ciwo, sannan daga baya ta fara samun sauqi har ta warke sarai.

Bayan ta samu lafiya, sai na fita daga gida na tafi shagona na kasuwanci na zauna ina cinikina kamar yadda na saba.

Kusan tsakar rana, sai ga wani babban baqin bawa mai muni da katuwar sura, dogo tamkar mashi mai fadin qirji tamkar benci, yana wucewa ta gaban shagona yana jefa wata kyakkyawar tuffa a sama yana wasa da ita a hannunsa!

Ko da na ga tuffar, sai na shaida cewa irin tuffar nan ce da na kawo daga Basra! Sai na ce masa da sanyin murya: "Ya wannan bawan kirki, don Allah sanar da ni a ina ka sami wannan tuffa domin ni ma in je in sayi kamarta?"

Bawan ya kwashe da dariya ya ce mani cikin izgili: "A wurin budurwata na samo ta! Na yi tafiya na dade ban nan, da na dawo gida sai na tarar da ita a kwance ba ta da lafiya, ga tuffa guda uku a ajiye a gefenta! Ta ce mani: 'Mijina wawa marar wayo ya yi tafiyar kwanaki goma sha biyar zuwa birnin Basra ya sayo mani su a kan dinare uku!' Sai muka ci muka sha tare da ita, sannan na dauki wannan tuffa guda daya daga wurinta na fito!"

Ko da na ji wadannan kalaman batanci daga bakin wannan bawa ya Amirul Muminina, sai duniya ta yi mani baqiqqirin! Hankalina ya tashi qololuwar tashi, na rasa inda nake!

Na tashi nan take na rufe shagona, na nufi gida a guje ina mai tsananin fushi da kuna da kishi da suka turnuqe zuciyata!

Da shigata gida, sai na duba gefen shimfida inda tuffar suke, sai na ga tuffa guda biyu ne kacal, babu ta ukun!

Sai na tambayi matata na ce: "Ya 'yar baffana, ina tuffa ta uku take?"

Ta dago kanta a hankali cikin rashin sani ta ce: "Wallahi ya dan baffana ban san inda ta tafi ba!"

Jin wannan amsa tata sai ya tabbatar mani da cewa lallai bawan nan gaskiya ya fada, kuma cin amana ta yi mani!

Nan take fushi ya rufe mani idanu, na zaro wukata mai kaifi, na haura kanta ta baya na danne qirjinta ba tare da na sake yin wata magana ba, na yanka wuyanta da wuka!

Daga nan na fille kanta, na gutsattsura namanta da gabobinta zuwa gunduwa goma sha tara cif! Na nade ta a cikin mayafinta da wani tsumman kafet, na dinke su a cikin wani kwando na ganyen dabino, na saka a cikin wannan akwati na kulle shi da kwado!

Na dora shi a kan alfadarata da kaina cikin duhun dare, na tafi bakin kogin Dijla na jefa akwatin a cikin ruwa da hannuwana biyu!

Na koma gida ba tare da wani ya san abin da ya faru ba. Amma da shigata gida, sai na tarar da babban dana yana kuka mai tsanani, alhali a wannan lokaci bai san abin da na yi wa mahaifiyarsa ba!

Na ce masa: "Me ya sa kake kuka ya dana?"

Yaron ya amsa mani yana kuka yana cewa: "Dazu na dauki daya daga cikin tuffar nan guda uku da ke gefen mama, na sauka qasa zuwa cikin lungu domin in yi wasa da ita tare da 'yan'uwana. Muna cikin wasa sai ga wani babban baqin bawa mai tsayi ya cafke tuffar daga hannuna ya ce: 'A ina ka sami wannan?' Sai na ce masa: 'Babana ne ya yi doguwar tafiya zuwa birnin Basra ya sayo wa mamata da ba ta da lafiya, har da wasu guda biyu a kan dinare uku!' Amma bawan nan bai saurare ni ba; da na sake roqonsa ya ba ni tuffata, sai ya doke ni ya kakkabe ni ya tafi da ita! Na ji tsoron kada mama ta yi mini fada idan ta ji na rasa tuffar, shi ya sa na gudu tare da qanina zuwa bayan gari muka buya har sai da yamma ta yi! Kuma yanzu tsoron maman nake ji, don girman Allah baba kada ka fada mata don kada ciwonta ya qaru!"

Ko da na ji wadannan kalamai daga bakin dana qanqane, sai na fahimci cewa ashe bawan nan qaryar sharri ya yi wa matata! Na gane cewa na kashe matata 'yar baffana bisa kuskure da zalunci alhali ba ta da wani laifi ko qanqani!

Duniya ta yi mani baqiqqirin! Na fashe da wani matsanancin kuka mai cin rai! Can sai ga baffana, mahaifinta ya shigo gida; na sanar da shi dukkan abin da ya faru, shi ma ya zauna a gefena ya fashe da kuka, muka kwashe daren muna kuka har tsakar dare!

Yau kwananmu biyar cif muna zaman makoki a kanta muna kuka da tsananin baqin ciki domin an kashe ta ba tare da wani hakki ba, saboda qaryar wannan baqin bawa tsinanne! Wannan shi ne asalin dalilin da ya sa na kashe ta!

Saboda haka ina roqonka da darajar iyaye da kakanninka da suka gabata, da ka yi gaggawar zartar da hukuncin kisa a kaina domin a daukar mata fansa a kaina, domin wallahi ba ni da sauran wani amfani ko dadin rayuwa a bayan idanunta!'

Ko da Halifa Harunar Rasheed ya ji wannan labari mai taba zuciya daga bakin wannan saurayi, sai ya yi matuqar mamaki da tausaya masa, ya ce:

'Wallahi wannan saurayi yana da hujja da uzuri! Ba zan kashe kowa a cikinku ba face wannan baqin bawa tsinanne mai qarya da ya haddasa wannan kisa! Kuma zan yi wani babban aiki wanda zai sanyaya zukatan masu baqin ciki da radadi, kuma zai faranta wa Allah Mai Girma da Daukaka rai!'..."

A daidai wannan gaba, sai hasken alfijir ya fara ketowa a sararin samaniya, Shahrazad ta ga safiya ta yi, sai ta dakata da zancenta mai dadin sauraro ta yi shiru!

Dunyazad ta dube ta da matuqar sha'awa da shauqi ta ce: "Kai ya yayata! Lallai wannan labari ya cika da zaqin kunne, da dadi, da cikar nishadi da ban al'ajabi mara misali!"

Shahrazad ta yi murmushi ta dube ta ta ce: "Ai wannan ba komai ba ne idan aka kwatanta shi da labarin da zan fada muku a dare mai zuwa, idan har Allah Ya raya ni kuma wannan babban Sarki ya qyale ni?"

Ko da Sarki Shahriyar ya ji wannan batu, sai ya ce a ransa: "Wallahi ba zan kashe ta a yau ba, sai na ji sauran wannan kyakkyawan labari mai ban mamaki!"

Wayewar gari ke da wuya, Sarki ya fita fada ya gudanar da al'amuran mulki yana bayar da umarni da hani har dare ya sake rufowa, shi kuwa babban Waziri ya koma gida fuskarsa cike da farin ciki da godiyar Allah da ya ga 'yarsa tana ci gaba da rayuwa cikin aminci!

(A nan muka kawo qarshen DARE NA GOMA SHA TARA da kuma BABI NA ASHIRIN DA UKU cif!)

====================================================================