Chapter 7
馃挮BA TSANA BACE 馃挮
..........007
Tsaye yake hannuwansa duka biyu cikin ajihun farar jallabiyar jikinsa,yayi kyau matuka duk da fuskarsa tana Nan kadaran---kadahan Bai saka hula ba Amma bakin lallausar sumar kansa da sajensa sai kyalli suke
fatarsa kadai ta Isa ta bayyana halin Hutu da nustuwa dayake ciki ,skin dinsa yayi hasken sosai Yana fitar da khamshinsa Mai Sanyi da Dadi....Baqaramar bugawa zuciyarta yayi ba,rabon da zuciyarta Tayi wnn bugawar tun lokacin Daya kirata lokacin tafiyarsa Qatar....ganin ta sandare Bata da niyyar basa Hanya yasa ya wuce ta gafenta haryana gogarta, jiki a mace tarufe kofar....da sallama ya karasa shigowa cikin dakin ummee tana xaune kan sallaya da sauri ya isa wajenta tare da hugging dinta ya lumshe ido shafa sumar kansa Tayi tana cewa Musawweer "baka Girma" sai yamaida kansa kan kafarta "ummee Nayi kewar kine dayawa" ya tashi xaune yadan rusuna Daga zaunen dayake"ummee Ina wuni,mun sameku lfy" "Alhamdulillah Aboon ya aeki"aeki ba "sauki Ummee yasu Abba?"sunanan lfy...dama ae aekin can da namu ba dayaba "wlh ummee aekin su akwai takura sosai" Allah dai ya taimaka...Amma Babu takura a cikin hidimtawa LITTAFIN Allah " haka neh ummee" Yaushe zaku wuce? Visern mu dai bayan Sallar da kwana 4 ne yadanyi shiru alamar tunani snn yace may be mu tafi tare nima na Samu hutun 3 weeks
sai yanxu tasamu damar karasowa ta xauna kusa da ummee snn a hankali tace"Aboon Ina wuni" lfy ya amsa a takaice batayi mamaki ba Dan dama ta xaci Hakan,ita kanta ummee Bata ji dadin yadda ya amsaba Amma sai Bata nuna Masa ba.....gefe ta koma ta cigaba da latse-latsen wayar ta su Kuma suna hirar su kasa虏 da Ummee"musawweer Sai naga kamar ka rame" yayi murmushin sa Mai kyau snn yace" ummee ae doleh na rame kodan rashin ku kusa Dani,da Kuma missing gikin ki" ae shiyasa naso kayi aure musawweer" shiru Yayi ummee ta kalleshi" bakason xancen auren koh?.... Haryanxu baka Samu wacce ta kwanta Maka bane? Kamar baxai Yi mgn ba sai Kuma yace " nasamu ummee Amma ban Kai ga sanar mata ba" cikin kulawa ummee tace saboda meh toh?...ko tsoro kakeh karta qi amincewa ta karashe mgnr tana dariya shima murmushi yayi snn a hankali yace"ummee tana da Wanda takeso neh....Kuma bana tunanin zata Soni? Sosai ummee ta Maida hankalinta kanshi"Ummee Banason Tayi rejecting Dina..zai fi kyau idan ban sanar mata ba...ta katseshi da sauri" Musawweer ba'asan Namiji da ragonta koh fargababa mata akafi sani da wnn halayyar,idan har ka tabbatar kana Santa toh ka sanar mata Koda Tayi rejecting dinka don't give up,ka yaki soyayyarh ka,kayaki xuciyarta har sai ka tabbatar ka Samu soyayyarh ta sai da tagama ya dago ya kalleta" Ummee tafah Yi nisah ason wnn Kuma har mgr aure an kullah tadanyi shiru " Toh Amma Mai yasa baka sanar mata da wuri ba? Ni kainah ban fahimci sonta nake ba ummee sai kwanan Nan" Musawweer zaifi kyau kacigaba da Addu'ah tunda har mgr aure ya shiga,kasan Kuma ba'a NEMA cikin NEMA nima xan tayaka da Addu'ah insha Allah idai Kaine mijinta toh Babu makawa sai ka aureta" toh ummee ngd.
Baby Bata Jin abun da suke fada Amma tabbas taji yace "nima bansan Ina Santa ba sai kwananan" Kalmar ta daki xuciyata dukda Tayi mamakin Hakan to wacece wnn da Aboon yake so...kodai Zunnirah ce Kai Allah yasa ba ita bace domin Bata kaunar wnn matar kwata虏 mgr da Ummee Tayi ya dawo da ita hayyacinta.....sai lokacin ta kula matar da suke xuwa sallah taxo Kuma shima Aboon Baya dakin ta gaida matar snn suka fita da Ummee ta rufe kofar snn ta xauna bakin gadon kasancewar tana off.....ana idar da Sallar Isha'e yayi knocking ta Bude Masa batare da tace uffan ba...dama video call suke da Hafeez Dan haka ta dauki wayarta suka cigaba shikuwa ya zauna Nan gefen gado ya mike kafafuwa tare da lumshe idanu.....kallo Daya yayi mata ya dauke Kai ya Kuma fahimci da Hafeez take waya Amma Bai cemata Komai ba ya cigaba da sabgar gabansa... Sun dauki lokaci sosae a haka kafin ta mike ta dakko abincinta ta fara ci...."keh" yafada kamar Wanda yake gabar mutuwa sai Tayi kamar Bata jisa ba tacigaba da cin abincin ta tana danna waya....a matukar zuciye yataso tare ta karbe wayar itama ta dago a zafafe da niyyar yimasa fitsara....Amma Daga lokacin da idanunta suka sauka cikin nasa sai ta kasa jure Koda kallon kwayar idanun nasa yayi mata wata iriyar kwarjini ba kadan ba... Shima a nasa bangare ba karamar Dakar xuciyarsa idanun nata sukayi ba ganin na canxa Masa sosoe ta dadayin kyau Mai daukar hankali ta xama babbar budurwa...Amma dake Namijin Duniya ne Bai nuna koh a fuska ba....Sai kawai ya koma da wayar a hannun sa ya xauna yashiga dubawa game teke Dan haka ya aje wayar a gefe...ta taso da niyyar daukar wayar duk Yana kallonta ta kasan idanu, sai da yabari tana gab da dauka ya cafki hannunta da mugunta ta kuwa saki Yar karamar Kara....a hankali ya fara mgn Cikin deep sharp voice dinsa"wato kin Raina ni yanxu koh?...Ina Miki mgn kina jina "ni ka sakar mun hannun Dan Allah" an qiya...koh kina da abun dazakiyi neh? Kokarin kwacewa tashiga Yi Amma takasa Dan haka sai tasaka Masa Kuka tabe Baki yayi snn yace" na Maida kina da karfi "bani dashi Amma ae Ina da Allah nah Kuma xai Saka mun duk abun da kake mun cikata yayi batare da yace komai ba ta dauki wayarta ta wuce ta xauna tana goge hawaye tana Kuma Kun kunai kasa虏 duk Yana kallonta ta kasan ido....Daga karshe ma lumshe idon yayi Dan ya Dunga kallonta da kyau....
NIGERIA
Bestie nifah gsky na fara kokonto akan aekin wnn bokan naki, almost 1 month kenan Babu Wani Labari Daga musawweer "calm down bestie tunda kikaga aekin bulu bulu Bai yiba may be Babu Alkhari a Lamarin neh...u have to forget about himm plss "no baxan iya ba "baxan iyaba bestie inason musawweer sosoe baxan iya hakura dashi ba Yamata ki Nemo mun Wata Hanya "shikenan mu'aje mgrn for now xanyi tunani.....
MADINAH
Yau ummee ta tashi da ciwon Kai tun safe baby Ke kula da ita, siyayyar dazasu karasa ma Basu Samu damar zuwa ba.
Suna xaune a dakin har musawweer ummee ta Kalli baby "baby tunda nadan ji sauki kuje ku karasa siyayyar keda musawweer"ah a'a ummee ki barshi kawai" yazaki ceh haka Maza tashi ki Shirya kutafi,Badan taso ba tashirya cikin Bakar abaya Mai stones red Tayi rolling din round face dinta da mayafin abayar sai flat shoe as usual suka fita....Babu Wanda yace da Wani qala duk da dukkansu na cikin gdn baya a taxin dasuka shiga,ita window side take kallo yayinda shi ya lumshe idanuwansa.....Wani babban shago suka shiga kasancewar dama sun fara siyayyar da ummee sai Basu karasa ba....
turaruka da Abaya xasu Kara sai hijabs da sallaya na tsaraba da na EId dinta ita da Ummee haka Tayi ta dauka shikuma Yana binta a Baya ba tare da yace komai ba duk da Yana ganin abun da take dauka wata Arsh jallabiya takai hannu zata dauka Wani ya rigata dauka suka juyo suna kallo juna....Kananun kaya ne jikinsa Riga da wando na Polo duk farare yayi murmushi tare da cewa ita kadai ta rage Kuma na rigaki dauka cikin slanz English dinsa irin na Yan America yayi mgn sai bace komai ba ya miqo mata ta karba snn tace "Tanx" da mamaki ya kalleta sai yayi dariya"kice Yan garinmu ne suka Badda kama" Gwana Ummu-khursum Ashe zamu hadu" da mamaki take kallonsa Jin yadda ya juya harshe zuwa Hausa"Kai Amma naji Dadi Barka kina lfy? Alhamdulillah "Masha Allahu suna Sayyeed Hamad Dan Nigeria ne Amma garin Kano nasanki sosai Amma fah ta waya da TV ya kare Yana dariya,Bata iyatace dashi komai ba ya cigaba gsky naji Dadi haduwa Dake "ngd ta fada kan lebbanta nooo yamakata ki bani numberki koh? kodan sadaukar Miki da wnn hadaddiyar rigar daniyi? Malam Daga Ina? Sukaji deep sharp voice dinsa fuskarnar amurtuke hannu ya mika Masa Amma yayi kamar Bai Gani ba sai ya Maida kallonsa gareta" Gwana kodai anyi auren neh? Ta fuskanci Yana da suturu Kuma baya kama bakinsa....dubi Daga haduwarsu Yakama mata xuba kamar ya Santa....kafin ta bashi amsa taji an fusgi hannuta pay point yawuce yabiya kudin...Kuma har lokacin Bai saki hannuntaba har sai da suka shiga MOTA yasaki, takuwa banka Masa harara ita bakin cikinta biyu Bai Bata damar daukar jallabiyar bama ya Wani janyota wai shi Mai karfi da wnn tunanin suka karaso ta dauki abun da zata iya ta bar Masa sauran duk Kuma Yana kule da ita......Koda suka shiga dakin Ummee kawai tayiwa sannu tana hade Rai ta amsa da cewa "an dawo" eh kawai tace a takaice shikuma ya shigo fuskasa kamar Koda Yaushe ya aje kayayyakin tare da musu sai da safe ya fice xuwa nasa masaukin.....Yana tafe Yana tunanin Mai yake damunsa shikam ya kasa gane kansa Mai yasa idan yaga baby ta Wani Namiji yake shiga bakin ciki har Baya iya controlling din kansa....toh kodai kishinta yake neh? Ya tambayi kansa toh Amma Mai xaisa yayi kishinta Wani bangaren na xuciyatar "ko dai kana Santa tane? da sauri ya ce a'a bana San.....sai Kuma ya kasa karasawa
******** ********. ******. *****
Yau haka kawai ta tashi Bata Jin Dadi jikinta bawai Dan Kuma batada lfy ba, a'a lfyrta lau kawai dai batajin Dadin komai gobe neh sallah....Kuma bayan sallah da kwanaki 4 zasu tafi.....
ummee suna daki ita da wnn matar Dan haka tace bari tafita tagano doll birds din madeenah plain black abaya tasaka Tayi rolling mayafinta sai Dan karamin pose dinta Wanda tasa wayarta a ciki sai Flat shoe Baki shima Tayi kyau tamkar balabiyar itama.....a hankali take tafiya kamar bataso batabi ta lifter ba sai tabi a bene ta xauna kan Wani kujera tana Jin daddadar iskar Dake wajen ta lumshe ido ta dauki lokaci a wajen kafin ta mike tafara tattaki....
Yaxo kenan zai shiga sai yaga kamar ita...at first ya dauka balarabiya ce Amma Daya kureta da kallo sai yaga ita ce Dan haka ya juya ya fara binta a Baya.....Farar jallabiya ce wacce Bata Kai kasa ba jikinsa sai takalmin sa da agogo suma duk farare Babu hula kansa sai dai yayi daurin mutanen Egypt akansa....yayi kyau tamkar Ethiopian...a hankali yake binta har yaga ta tsaya wajen birds din tana watsa musu Tsaba ba karamin kyau Tayi Masa ba Dan haka sai yafito ya wayarsa ya shiga Yi mata pics harda video...ganin Wani balarabe ya nufuta yasa ya tsaya da hotan kafin ya karasa wajen....balaraben ma tambayar ta Hanya yayi tace Masa Bata saniba Daidai ya karaso wajen ya tsaya daf da ita....ta Daga Kai ta kallesa sai ta ganga wata Yar karama a gabansa Dake musawweer dogo ne Masha Allahu itakuma tana cikin tsaka tsaki xata matsa kawai ya kama hannunta yayi Gaba da ita.....batayi kokarin kwacewa ba sai tafara hawaye sai da suka karaso Wani waje Wanda Babu jama'a sosai snn ya sake ta tare da xama kan wata kureja Dake wajen itakuma ta tsaya har yanxu Kuka take Mara sauti....ya dago da niyyar mata mgn ganin tana Kuka yasa yayi shiru Yana kallonta tun tana kukan Baya fita har ya fara fita sosae ya mike "meyafaru? Bata kulashi ba sai kukan dai ya Dan sassauta murya "Yi hkr,zauna" Bata zauna ba Kuma Bata Dena kukan ba ya kamata ya zaunar "Yi shiru ki fadamun Mai Nene? Sai ta Kara karfin kukanta bawai abun da ya mata bane yasata Kuka A'a dama Yau ta tashi Bata Jin Dadi so kukan na kusa,ya kureta da ido har tadena kukan tafara ajiyar zuciya ya Mika mata ruwa ta karba ta wanke fuskarta....idanuwanta sunyi jaa sosae "a hankali yace tell me mayasa kaki Kuka "Babu" tabashi amsa yaso ya sake mgn Amma yayi shiru....da sauri ya tashi ya riko tsohon Dake Shirin Fadi sakamakon ruwan Daya taka Wanda baby ta wanke fuskarta ita da shi duka suka sauke ajiyar zuciya "Shukran Shukran Likthir tsoron ya fada" sai Kuma yayi shiru Yana kallon musawweer yafara mgn lalle"akwai babban lamarin Dake tare dakai da wnn matar taka....inaso ku kara riko da addini kada kuyi sakaci ko kadan da azkar ya Kalli baby"Mafi yawan lokaci abun da muke so bashi bane Alkhari...Dan haka Babu yanda zamuyi da Alkawarin Ubangiji" Daga haka ya wuce sosae musawweer ya fahimci abun da tsohon yake nufin sai dai kansa yakasa breaking kalaman into Abu Mai ma'ana ita dai baby ayar Daya anbata ita kawai ta fahimta ya kalleta tashi mutafi Babu musu ta mike suka wuce.......Hernarn Muhammad鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍