KAYAR RUWA

7

by @halimahz

Ni dai tun da na yi komawata ɗaki ban ƙara fitowa ba, ina jin duk wani kai komo na su da su ke yi. Ba yawa gare su ba, amma yadda ka san masu jeran kayan amarya, duk sun cika gidan da hayaniya. Lallai ala dole sai an nuna min gidan Ɗan uwa aka zo.

Hmmm. Allah sarki rayuwa, ni fa ina cikin ƙungiyar kare mutuncin dangij miji. In har ina wuri bana yarda a taɓa su, wallahi ban yarda da sukar dangijin miji ba sam. Duk rashin bakina, akan kare dangin miji dai, to bakina har tsini yake yi, haka zan ta kumfar baki ina kare musu girmansu da mutuncinsu. Amma inaaa yanzu kam zan fita fit a wannan ƙungiyar, zaman cikinta ba da ni ba, na ga nima karatun da bai biyo ta kaina ba, yanzu ya zo, na fara ɗaukar darasin cikinsa babi babi.

Ai ni duk yadda za ace, gani nake kawai masu kokawa akan dangin miji, laifin daga garesu ne, su ne basu iya zama da su ba. Saboda ban yarda akwai marasa kirki ba, kawai ɗauka na ke dukkansu masu kirki ne. Baƙin halin Mace ke janyowa ta rasa kirkinsu. Na san halinmu Mata. Ashe dai da gaske ana rashin dacen su. 

Duk da dai har yanzu ina ganin kamar ni na yi musu wani laifin, bisa kuskure wanda ban sani ba, shi yasa suka canja min, suka juya min baya, suka ce bari su barni da baƙin halina. 

To kuma dai duk iyakar zurfin nazari da tunani, banga wani mugun hali da na ke da shi ba, wanda har zai sa in dinga fuskantar cin zarafi da wulaƙanci daga garesu. Kawai dai suna da na su dalilin ne. Tsana ce ta babu gaira babu dalili, ko gani su ke kamar zan iya shiga tsakaninsu da Ɗan uwansu ne, ko kuma duk saboda rashin haihuwar ne, kamar yadda na lura yanzu duk wata magana mara daɗi da za a gasa min sai an goranta min rashin haihuwa.

Irin yadda na yi amanna da dangin mijina, sai da ta kai ta kawo ina daidaita matsayinsu ɗaya da nawa Ƴan uwan. Saboda har ga Allah a yadda suka ƙaunace ni lokacin da aka auro ni, sai da aka dinga tayani murna, ana cewa Allah yasa su ɗore, ashe ashe su kam sa ce, jira lokaci Matar Nazifi.

Na sauke numfashi, juyawar al'amarin nan yana bani mamaki, yana ɗaure min ka. Duk saboda ban haihu ba wai? Ko kuwa dai akwai wani dalilin? Kaiii.
Alqur'ani na ɗauka ina karantawa don shi zai mantar da ni babinsu, har sai bayan sallar la'asar na dai na jin motsi, a sannan ne na fito, lokacin na tarar ashe sun tafi, tafiyar da ko arziƙin sallama ban samu ba.

Na furta "Allah ya kyauta." 
Ɗakin yaran na buɗe na leƙa, zaune na gansu kan gado ɗaya suna kallo. 

Atika ta yi murmushi da gani na, ita kuwa ɗayar ta haɗe rai tana juyar da fuska gefe. Na ƙarasa wajen su, ɗakin na su ya yi kyau, gadon yara ne guda biyu aka saka kowacce da nata. Sai durowar kayansu ma kowacce da nata, arziƙi mai daɗi, da babu kuɗi fa ba za a musu duk wannan hidimar ba.
Kaya har kaya masu mugun tsada, a duniya wa kuwa zai so talauci, ai wanda ya ce kuɗi ba su yi ba, to bai samesu ba ne kawai. 

Ɗakin ya burgeni sosai kam, dama ta ɓangaren gyaran gayu, Anty Aisha ba daga nan ba. 
Na zauna cikin yarana ina masu hira, na zama kamar ƙawarsu, har sai da Rumana ta saki ranta. Dama ita ce mai bakin magana, nan kuwa aka shiga bani labarin ƙawayen makaranta da Malamarsu mai sa kamun kunne, tana faɗa min tun da sun dawo nan, ga makarantar da zan ce Baba Ƙarami ya saka su.

A haka Hubbi ya dawo ya same mu, annurin fuskarsa kaɗai ya shaida min yana cike da tsananin farin ciki, sai na ji tausayinsa duk ya kama ni.
Ya kenan yau in ace Yaransa ne na cikinsa? Na kai hannu saman cikina, ina rufe idanuwana tare da roƙon Allah ya azurtamu da haihuwa kafin mutuwa.

Farin cikinsa ya kasa ɓoyuwa fa, abin da ya siyo musu ya basu, su ma ɗin sai murna su ke yi. Wayarsa ya ɗauko ya kira Yaya yana ƙara yi mata godiya da alkhairinta gare shi, Anty Aisha ma ya kirata daga baya.

Tambayar yaran ya yi ko sun ci abinci, suka ce masa ehh, ya ce,"To ku ta so mu je ɗakina."

Tare muka fita gaba ɗaya muka bi shi, yau dai haka na ci albarkacin yaran, walwalarsa gare ni ta dawo, mu ka yi ta hira kamar ba shi ba ne ya canja min ba, canjin da babu magana babu kyakykyawar mu'amala.
Amma yau bini bini ya tambaye ni me ya kamata a siyawa yaran. Ni dai abin da na fara cewa masa. "Ni na fi ganin akai su makaranta da wuri, kar ayi musu nisa a karatunsu ko."

Bayan ƴan kwanaki da safe na fito a wanka, turus na yi ganin Hubbi ya shigo ɗakin, wanda rabonsa da ɗakina har na manta. Kallonsa na tsaya yi, shi ma bina yake da kallon, to da yake dai tun zuwan su Atika ya ɗan sakko, tsoronsa ya ragu a raina, muryata a hankali nace,"Ina kwana".

Ya ƙaraso ciki yana zama bakin gado. "Kin tashi lafiya".

"Lafiya lau, mun je ɗakin ai na tarar baka tashi ba. Sai na ɗauki ɗari biyu a wallet na bawa su Rumana kuɗin makaranta".

Na ƙarasa gaban madubi na ɗauko takarda ƙarama, na miƙa masa ina daɗa cewa,"Jiya aka ba su a makaranta, wai sun manta ba su baka ba".

Ya kalli takarda yana cewa,"Ta me cece?".

"Ban duba ba".

Karɓa ya yi ya duba ya ajiyeta. Sai kuma ya kishingiɗa da gadon yana danna wayarsa. Ni dai tun fitowata daga wankan na ke jin tasirin kallonsa na shiga jikina. 
Tun da aka bamu yaran nan ya dawo hayyacinsa, kuma alamunsa sun nuna ya gaji da ƙauracewa junanmu, so ya ke ya kasance da ni, sai dai ni ɗin na ƙi basa dama da fuska. Ko jiya da na ga a gwiwa ya ke, tuni na gudo ɗaki, don nima sai na rama. 

Mutumin da zan je masa, ya buɗe baki ya ce min ai ya san banda matsala zan iya riƙe kaina, to shima ya riƙe kan nasa yanzu, kamar yadda yake yawan faɗa min bai da matsala.

Yi na yi tamkar na mance da shi a ɗakin, na buɗe wadrobe na ɗebo kayan da zan saka, sannan na ƙarasa na zauna kan kujerar madubi.
Ta cikin madubi na hasko shi idanuwansa sun kafe a kaina. 

Na yi guntun murmushi da ni ɗaya na ji sautinsa. Zai yi bayani ne, da ni yake zancen.
Cikin natsuwa, da yadda na ke yin komai nawa a hankali, na ɗauko man shafawa ina shafawa, cikin wani irin salo na ɗaukar hankali, da kunna lafiyar Oga.

Tun da na shafa humra, na hango shi ya lumshe ido, yana sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske. 
Murmushi ya ƙwace a leɓena, yadda yake jin kansa kenan a yanzu, ba zai iya tasowa ya zo gareni ba, a fara al'amarin tun a gaban madubi. Lallai kuwa yana ruwa idan ni yake jira na miƙa kaina. Wato yana so yana basarwa, borin kunya ne fa duk, ba wani abun ba. Ai shima ya san abubuwan da yake min a zamantakewar mu na yanzu, ba ya kyautawa, kuma idan bai yi wasa ba sai Allah ya kama shi.

Na ƙarasa kimtsa jikina da turaruka masu shu'umin ƙamshi, irin humrorin nan ne, da ke kanki mace ƙamshinsu na taɓaki, balle kuma ga namiji.
In shafa wancan in mulka wancan duk na ƙamshi,  na ke tuna wata lecture da aka yi mana a Halima.hz Novel group. Sai na ji ba zan iya aiwatar da darasin da aka bamu ba, na san mijina ne, wanne dare ne jemage bai gani ba, amma dai ba zan iya kunce towel da gangan ba a gabansa in kamar zarya da sunan ina shiryawa, kunya na je ji, a bar ni a duhun kaina kamar yadda Coatch ɗin ta faɗa, masu irin wannan kunyar kansu a duhu ya ke. Ni fa ko mu'amala za a yi to kar na ga haske, ko da yake Coatch Aisha ta ce ƙaryar rashin kunya muke yi ai.

Na ɗebo kayana zan saka, sai na ji muryarsa a kasalance yana cewa.

"Zo".

Ɗago ido na yi na kallesa na ga yanayinsa duk ya sauya. Alamar ɗumina kawai ake jira a ji yana shiga jiki.
"Tom". Na faɗa.

Ina nuna kamar ban fahimci komai daga garesa ba. Na tsaya saka riga, sai dai kafin na kai ga sakawar, ya dakatar da ni,"Ki zo na ce fa".

A yadda sautin muryar nasa ya fito, ni dai shekaru goma da aure, ban taɓa jin muryarsa ta bayyana a cikin tsananin sha'awa irin haka ba.
Na kuwa ɓata fuska nace,"Hubbi bari na ƙarasa saka rigar...".

Sai da na saka ɗin kuwa, sannan na je wurin nasa. Ina ƙoƙarin zama a gefen kusa da shi, sai ji na yi ya janyo ni, na yi mazauni da cinyarsa.
Idanuwansa suka lumshe, yana ta faman jan numfashi da saukewa, humrar nan ta BestynnHalima.hz tana rikita bawan Allah nah.

Sai da ya zagaye ƙuguna da hannayensa, tukunna ya kwantar da kansa a ƙirjina. 
Murya a matuƙar kasalance ƙurewar lamba, yace,"Habibty fushi ki ke da ni?".

Na yi masa shiru. Kuma rashin ba shi amsar shi ya saka shi buɗe ido, ya ɗago kai ya jefa ƙwayar idonsa cikin tawa. Na ƴan sakanni yana kallon cikin ƙwayar idona, wadda ta cika taf da ruwan hawaye.
Shi kuwa idonsa kamar ba nasa ba, ya ƙanƙance saboda jarabar da yake tare da ita.

"Ki amsa min mana Habibty, fushi kike da ni?"

Ya sake tambaya yana kai hannu ya tallabi haɓata.
Kai tsaye na ɗaga masa kai, ba sai na yi magana ba, don bana so kukan da yake maƙale a maƙoshina ya ƙwace.

"Ki yi magana mana Ummm. Kin san bana son bayar da amsa da kai."

Kamar jira, sai kuwa hawaye ya sakko min. Yadda na ga ya nuna damuwarsa da zubar hawayen nawa, Wallahi sai na ga kamar a mafarki, yaushe rabo! 
Ai ban fita a wannan mamakin ba, ya ƙara danƙara ni cikin wani. Ahhh! To gani na yi ya shiga goge min hawayen yana faɗin,"Ki daina don Allah. Kin san bana son ganin hawayen Mace mai daraja."

Ai wallahi sai na yi sakk ina dubansa ta cikin ruwan hawayena, kai ni fa sabon mutum ya koma min. A zuciyata na ke jin kamar ba shi ba. To na manta rabon da ya kalle ni da mutunci ma, balle ya faɗa min kalamai tausasa. 
Abin da yasa na ke girmama lamarin, na faɗa muku a baya, ba mu saba faɗa da shi irin haka ba na dogon zango. Ace dai ya ɗauke min wuta gaba ɗaya ya daina shiga harkata. Sannan sai daga baya mu dawo mu shirya kamar ba ayi ba.

A'a! Iyakar faɗanmu mun daɗe kwana ɗaya, shima ɗin duk girman faɗan a naniƙe muke a makwanci, ba ma shiga da haƙƙin ba wa fatar juna ɗumin da ya kamata. Kun ga kuwa a yanzu dole in yi mamaki, tun da wata fin biyar ana ƙaurace maka ba wasa ba.

Ya kwanto da kaina a kafaɗarsa, yana shafa gashina mai laushi da ƙamshi, wanda ya sha gyara da man Sirrin Gashi. 
"Habibty ba kukan ba. Shin ba ki kewata ne?"

Ikon Allah, wai mutumin da kusan kullum sai na bisa ɗaki, shi ne zai faɗi haka. Gajiya na yi da cin kashin fa, shine na yi hankalin kama kaina na daina zuwa nemansa. Kai ko ba komai fa shiga groups ɗin Matan aure da ake wayar da kan juna, yana da matuƙar amfani. Bana magana a group, amma duk wata tattauna mai muhimmanci kwasheta na ke yi, ta boƙarewa miji ce dai Sa'idanku na kasa hawa kai.

Cikin muryar kuka na ce,"Idan ma na yi kewar taka ya zanyi Hubbi?"

"Ban gane ba. Me ki ke son faɗa?"

"To haka kawai ka mayarshe ni tamkar ba matarka ta so ba. Kuma ka ƙi faɗa min dalilinka na ƙaurace min, har ka ɗauki dogon fushi da ni. Na baka haƙuri time without number ka ƙi haƙura, ni kuma a iya sani na, ban san laifin da na yi maka ba, har ya kai ga ka daina sona".

Na yi shiru. Jimm kaɗan shiru ya ratsa ɗakin, kunnuwa na dai ba abin da suke ji, sai sautin saukar numfashinsa. 
Ƙuguna ya ɗan matsa a hankali. Tukunna yace,"To ki yi haƙuri, na san na miki ba daidai ba, afuwan kin ji".

Ya yi maganar ƙasa ƙasa, cikin muryar lallashi. 

Na narke murya nace,"To me yasa fushin Hubbi?".

Numfashi ya sauke. Kamar ba zai ce komai ba, sai kuma yace.

"Habibty ban san mai yake faruwa ba. Amma haka kawai na ji na canja miki ɗin."

"Dole akwai dalili Hubby. Ka faɗa min don Allah, ina so mu fahimci juna."

Sai da ya ɗan kalli cikin idona, kamar yana jin kunyar faɗa min abin da ke ransa. 
"Kin san ina so in ga na samu Ɗa, sai dai ke shiru, na ga kamar rashin haihuwar bai dame ki ba. Shi yasa na ke ta fushi. Har ma na ƙaurace miki a shimfiɗa, don ina ganin mu'amalar bata da wani amfani."

"Saboda a haihu kawai ake kusantar juna Hubbi? Kamar fa kana faɗa min abinda ba haka ba ne. Ba ina nufin kana min ƙarya ba, amma ba haka gaskiyar maganar take a ranka ba."

Shiru na ƴan sakanni. Tukunna ya ce. 
"To koma dai menene, fushin da na ke na rashin haihuwa ne. Amma yanzu da na samu yaran, na ji kaso saba'in ya yaye na damuwar rashin haihuwar da bamu yi ba. Kin sani dai ina sonki, matsayinki bai taɓa canjawa ba daga zuciyata, saboda haka kar ki ƙara cewa na daina sonki kin ji ko, ni ɗin na ki ne na har abada, ke ɗaya jallin jal Sa'idan Nazifi".

Mata da Miji sai Allah. Tuni na nemi jin haushin na rasa. Sai ma tausayinsa da na ji ya kama ni.
Ina murmushi na ke dubansa, kalamansa sun fi kama da daɗin baki, dole zai kalamance ni tun da yana so na kai shi duniyar sama. Kuma ba don ya ga ina bagarar da shi ba, bana zaton zai sauke kai ƙasa, ya biyo ta hanyar da ta da ce. 

Tabbas shi ɗin mai tsananin Sona ne, duniya kanta zata shaida hakan. Amma dai na faɗawa kaina gaskiya, in daina yaudarar kaina, soyayyar da na san ana min ada, ba bu ita a yanzu, kaso tamanin zan iya cewa ta mutu. Ni ɗin dai ya bari da tarin soyayyarsa da ƙaunarsa.

Don ko a yanzun haka, sabuwar soyayyarsa ta musamman na ji ta kama ni, amma na kasa amayar da duk wata magana da ke narke a cikina.
Take yanke duk tarin baƙin cikin da ya ƙunsa min na tsawon watanni na ji ya gushe, babu ko ɓurɓushinsa. Tabbas ina son Mijina, so mai tsanani ma kuwa, ban ƙara gasgata hakan ba sai  yau.

Ina ƙaunarsa matuƙa. Kuma Son na sa da ƙaunarsa ne yasa zan ci gaba da haƙurin rayuwa tare da shi. Duk da na ji wata a group na novel ɗin Halima.hz tana cewa, duk macen da take zaman haƙuri saboda soyayya ko tausayin miji, ba ya tarin wulaƙanci da nuna rashin darajar da yake yi mata, to bata san ciwon kanta ba sam. Kuma abar a kama a daka ce.

Ni dai to babu mai dukana, ai na ma rufawa zamantakewar tamu labulen sirri, ban ya ye labulen ba, balle aga a halin da na ke, har ace za a yi min dukan. Tausayin Miji kam da karɓar uzurinsa, na saka shi cikin ibadun aurena, kuma akan wannan ibadar zan mutu.

Duk da cewa dai, a ƴan kwanakin nan kaɗai na lura soyayya da komai nasa, ya tattare ya ɗora akan yaran can, kuma hakan zai iya haifar min da babban ƙalubale wallahi. Kun san fa akwai irin Mazan nan masu mugun son yara, da su ke iya ɓatawa da ke Uwa akan yaranki. 

Ya katse min tunani, ina jin shigar wani abu jikina, dalilin saƙon da ya fara aika min, ta hanyar kai hannu ƙirjina ya fara yawo da shi a wurin.

"Ya kamata mu sha soyayyar da zata mantar da mu komai da ya faru, komai ɗin ya zama tarihi".

Bai jira jin cewata ba. Ya miƙa wani saƙo da ya san zai tafi kai tsaye zuwa ƙwaƙwalwata. Take kuwa na karɓa. Don ni na taimaka masa wajen cire rigata. Lokaci guda ya shiga aiwatar da zazzafan salonsa ga jikina.
Tuni na bayar da kai bori ya hau, muka faɗa cikin duniyar sama. Lallai mun yi matuƙar kewar juna, don mun daɗe kafin mu samu natsuwar da muka rasa na tsawon watanni. 

Da mamakina muna gamawa ya tashi ya fita a ɗakin, ko wanka bai tsaya ya yi ba, saɓanin da anan yake tsayawa ya yi wankansa, wataran ma tare mu ke yi, amma yau ko mai yake nufi da hakan oho.

Ban ma kawo komai a raina ba. Na miƙe cikin gajiyar jiki na shiga wanka, bayan fitowata kasa komai na yi. Kawai kwanciya na yi, saboda ba ƙaramin gajiyar da ni ya yi ba, don sai da ya ƙosar da kansa da yunwar watanni da yawa da ya ɗiba ba ya tare da ni.