Resignation and Reinvention
9:00am
Zara ce ta shigo bedroom ɗinta riƙe da Jasmine a hannunta, freshly bathed and dressed, ta gama ma ta wanka kenan ta shirya ta tsaf, curly hair ɗinta is as neat as it can be and her little outfit soft against the morning light. Ta shigo bedroom ɗinne ta ga ko Zafar ya farka. Jiya bayan sun dawo daga manor har gurin ƙarfe sha ɗaya na dare tana zaune tana kuka, her eyes heavy and her chest still aching from the night's fallout, amma Zafar bai ce ma ta uffan ba; daga ƙarshe ma ɓangaren sa ya tafi ya shige office ɗinsa, leaving her alone with the cold silence between them. Bayan ta gaji da kukan, tashi tayi ta sauka downstairs ta ci abinci; bayan ta gama ta dawo ta maida kayan baccin ta sannan ta kwanta, exhausted down to the bone. Ganin ya bar wayarsa a ɓangaren ya sa ta ɗauka, her fingers hesitating only a second before unlocking it; message ta shiga ta shara apology message ta tura wa Daddy a zuwan Zafar ɗin ne, dan tana lure da ko gaisuwarsa Daddy bai amsa ba har kuma suka tafi bai kula sa ba wanda hakan sam bai wa Zara dadi ba. Tana gama tura message ɗin ta goge, wiping every trace from his screen, sai gashi ya shigo da laptop ɗinsa ya zauna kan gadon ya ci gaba da danne-dannensa, his jaw set in a quiet, unreadable line. Ba su ce wa juna uffan ba yayin da Zara ta faki idonsa ta tura ma sa wayarsa inda ta gan ta sannan ta juya ta kwanta; in five minutes bacci ya ɗauke ta, pulled under by sheer fatigue. Sai dai gurin ƙarfe ɗayan dare ya tada ita, she was on her period, ya sani—so sai ya sa ta ta yi ma sa wasu abubuwan daban; sanin he’s in a bad mood ya sa ba ta ma sa musu ba, tayi iya ƙoƙarinta gurin faranta mai and it worked, bayan ta gama gamsar dashi kuma ta koma bacci. Amma ko minti goma ba ta yi da kwanciya ba kuma Jasmine ta tashi; wasanta ta riƙa yi kamar rana ta hana Zara bacci, kicking and fussing softly. Lokacin yana zaune kan sofa ɗin ɗakin yana ta aiki a kan laptop ɗinsa, the faint glow of the screen catching his tired, sharp features; can ya miƙe ya fita, bayan few minutes ya dawo da bottle ɗin Jasmine a hannu. Tana kwance kusa da Zara tana ta surutunta ya zo ya ɗauke ta sannan ya fice daga ɗakin, taking the weight off Zara without speaking a single word. Sai a lokacin ne Zara ta samu bacci ya ɗauke ta, finally sinking into deep sleep, yayin da shi kuma ya koma lounge da Jasmine ɗin ya yi ta raino har ta yi bacci gurin biyu da rabi na dare. Bayan ya kwantar da ita ya ci gaba da aikinsa; sam bai runtsa ba daren ranar har asuba yayin da Zara ke ta sharar baccin ta, his eyes wide awake despite the long hours. Bayan yaje masallaci ya ya dawo kenan Jasmine ta tashi; Zara ya tada ta ba ta abincinta sannan ta miƙa ma sa ita ta koma ta yi kwanciyarta, letting the early morning quiet pull her back to sleep. Ita ma Jasmine ɗin ba ta wani daɗe ba ta koma bacci, bayan Zafar ya kwantar da ita sannan shima ya samu ya kwanta, finally letting his guard drop. To shine ya samu ya runtsa cike da gajiya, deep asleep as the morning light climbed higher. Yanzun da Zara ta shigo still bacci yake, his breathing slow and steady against the pillows. Juyawa tayi ta koma lounge ɗinta ta buɗe mini fridge ɗin ɗake gurin ta ɗauki robar ruwa ɗaya, sannan ta juya ta nufi ɗakin tana kallon Jasmine tace, “Let’s wake daddy, yeah?” A soft, tentative warmth breaking through the hushed room. Yarinyar dai sai kallon ta take tana ta ƙoƙarin kama gashin kanta ɗake a baje, tiny fingers reaching up with clumsy curiosity. Zara na shiga bedroom ɗinta ta nufi kan gadon yayin da take buɗe murfin ruwan, the faint twist of the cap sounding clear in the quiet morning air. Tana kuwa ƙarasawa tsaya kansa, ba ta yi wata-wata ba ta watsa ma sa chilled bottle water ɗin nan a fuskarsa da jikinsa; ɗigon sanyi ya fara sauka a kan gashinsa da fuskar da take kwance a pillow, icy drops trickling down his neck. A gigice ya farka yana miƙewa zaune, his chest rising fast, eyes snapping open in shock; sai dai ya tashi ya zauna ba ta fasa zuba ma sa ruwan ba sai da ta juye ruwan tass a kansa, tipping the bottle till the last drop soaked him and the sheets. Cike da gigicewa yake share fuskarsa da tafin hannunsa, water dripping from his lashes and jaw, yana ƙoƙarin miƙewa tsaye, still dizzy from sleep and shock. Sai dai muryar Zara ta dakatar da shi cikin masifa, sharp and unbothered in the quiet room:
“Who lied to you that poor, jobless men have the luxury of sleeping in? Abeg oga, up and at ’em! Don't tell me you forgot Baffa’s 8:00 AM appointment at the Nexus—you wouldn't want to be late to your own firing!” Daga haka ta juya, turning toward the door in a rush, tana cewa, “Rise and shiiine! Hop up and hit the shower sharp-sharp—and just so we’re clear, broke men don't get morning privileges, so don't even think about coming near me.” Daga haka ta fice daga ɗakin, her flip flops soft against the tiles; ƙasa ta sauka ta shiga dining room dan ganin ko breakfast is ready, dan yanzu gaba ɗaya ya daina shiga dining hall—a gida suke breakfast ɗinsu har da Zwar, settling into the morning routine. Yau ɗin Sam ta sa ya sauke Zwar school saboda ya yi complain a kan yana zuwa late kullum; da ta ga Zafar na bacci sai ta tada Sam tace ya kai sa bayan ta haɗa ma sa a bowl of cereal ya sha, dan ba da wuri ake breakfast ɗinsu ba sai an daidaita lokacin tashinsu sannan ake ɗaurawa—yau dai take so ta yi wa Jummai magana a kan ta sa kitchen staffa su riƙa yi ma sa na sa breakfast ɗin da wuri tun da yace yana late kullum. Ɗakin Sam ta shige tana ɗan knocking bayan ta buɗe ƙofar, her knuckles tapping lightly against the wood. Tsaye ta gan sa bakin mirror yana taje kansa da brush, ɗaure da towel a waist ɗinsa, da alama daga wanka ya fito, steam still clinging to the air. Juyawa ya yi yana kallon ta, fuskarsa a haɗe, his brow knitted tight, yana cewa, “Seriously? I’ve told you a million times to knock before coming in.” Taɓe baki tayi tana ma sa kallo sama da ƙasa, kafin tace, “What time are your classes this morning?” Maida idonsa ya yi kan mirror ɗin yana ci gaba da taje kansa yace, “Why? What’s up?” Zara ta ƙaraso ciki, walking closer with Jasmine resting against her hip, tana cewa, “I need you to hand something to Roman before you leave for school.” Ba tare da ya juyo ba ya gyaɗa ma ta kai yana cewa, “Sure, just make sure it’s nothing that’ll drag me into drama—I know Daddy was here yesterday.” A calm edge in his voice. Zara ɗake yi wa ƴarta wasa tana ma ta kisses, nuzzling the soft curve of her cheek, ta ɗan kalle sa tana cewa, “It’s not—just a small apology. Daddy instructed me to apologize to him.” Sam ya gyaɗa kai yana nufar cikin closet tare da faɗin, “Oh, fair enough. Go bring it, then.” Daga haka ya shige closet ɗin, the door clicking softly; ita kuma ta juya ta fice da sauri ta hau sama, her steps quick as she headed back upstairs. Sama ta koma tana hawa matakalar benen da sauri, ko da ta shiga ɗakin, Zafar na cikin bathroom. Shiga tayi ta isa gurin walk-in shower ɗin, tana buɗe ƙofar gilashin a hankali, ya juyo da sauri yana kallon ta, ruwa na bin fuskarsa da jikinsa. Ganin ta na tare da Jasmine ya haɗe rai yana ata kallon kanki daya? Dan tara hannunsa a ƙarƙashin shower sannan ya watsa mata ruwa with a serious face, yana cewa, “Out. Now, creep.” Da sauri Zara ta matsa baya tana ɗan ihu tare da fashewa da dariya sosai, sautin dariyarta na cika banɗakin yayin da Zafar ya danne tasa dariyar yana haɗe rai tare da rolling idanun sa, wanda hakan da yayi ba ƙaramin kyau yayi mata ba. Jasmine kuwa da ɗigon ruwan ya sauka a jikinta, ta ɗan firgita at first, ta kalli mahaifinta da idanu a buɗe, kafin nan take ta saki wani kyakkyawan murmushi tana wuntsila ƙafafunta da hannayenta cikin jin daɗi, kamar ta gane wasa suke yi. Zara na dariya tana share splash ɗin ruwan a fuskar Jasmine da gefen hannunta a hankali, ta cewa Zafar, “Come on, Obim, wrap it up. You know, I’ve been thinking—maybe the two of us should go see Baffa together and apologize properly before he steps into the Nexus hopefully, or send little Jasmine over as our peace offering with a sweet note—there’s no way his heart won’t melt.” Ta ƙarasa maganar tana tickling ƴarta ɗake ta mata dariya tana enjoying wasar. Zafar da ya ci gaba da wankansa, ya girgiza ma ta kai a hankali yana cewa, “It’s already done, Mama. I drafted my resignation letter last night and submitted it first thing this morning.” Muryarsa na fitowa a nutse, ba tare da wani alamun damuwa ko nadama a fuskarsa ba. Cikin kiɗimewa Zara take kallonsa, murmushin dake fuskarta ya ɗauke gaba ɗaya, kafin ta daka wata uwar tsawa tana cewa, “You did what?! What the fuck is wrong with you, Zafar? Have you completely lost your mind? No, no! Look at me and tell me you didn't do that, Zafar! Tell me you didn't just throw everything away!” Ta fara matsawa baya tana kallon sa cikin tashin hankali, kirjinta na ɗagawa da sauri, yayin da Jasmine tuni ta fashe da kuka saboda tsawar da Zara ta yi, kukan na gauraye banɗakin nan take. Cikin sauri Zafar ya fara wanke jikinsa yana cewa, “Chill out, Zara. I didn't do it blindly. I have my reasons.” Tuni hawaye ya fara bin fuskar Zara tana kallon sa unbelievably tana girgiza kai, hawayen na zuba kan kumatunta ba ƙaƙƙautawa. Cikin kuka tace, “There is zero excuse for throwing your entire life away like that, Zafar! You bled for that position—everything you poured years of sweat into! How could you just hand it over without a fight? How could you even—Oh God, I can’t even look at you right now. You genuinely disgust me.” Daga haka ta juya ta fice tana wani kukan takaici, tana taka ƙafafunta da sauri zuwa wajen bathroom, baƙin ciki na danne mata ƙirji. Ta ma manta rabonta da ta ji wannan baƙin cikin a rayuwarta, kamar wani abu mai nauyi ya tokare mata maƙogwaro. Tunani kawai take me yake damun Zafar yanzu wai? Ta na bin kowane tunani na zuciyarta a nutse tana son gano a ina matsalar take. Ta wani ɓangaren kuma tana mamakin yadda abubuwa suka rikide cikin ɗan gajeren lokaci. Ba ta taɓa jin takaicin sa ba irin na ranar—shi har babansa yi wa zuciya yake? Wannan wane irin hali ne? Ta riƙa tambayar kanta tana jijjiga Jasmine a hankali a kafaɗarta, tana bubbuga bayanta da hannu ɗaya, yayin da hawayen idonta suka kasa tsayawa. Ita fa gani take duk ɓacin rai ne—in sun ba Baffa haƙuri ko kuma ta je ita da Jasmine da ɗan note a hannun Jasmine ta ba shi haƙuri da kanta kuma ta san zai haƙura, domin a ganinta dattijon ba zai jure ganin ƴar princess ɗin nan na lallabarsa ba; amma shine Zafar zai yanke hukunci cikin fushi ba tare da tunanin gobe ba? Wani kukan baƙin ciki ta sake fashewa da shi tana doka wani uban tsaki mai ƙarfi, wanda ya ratsa ɗakin, jin ya buɗe ƙofar bathroom ɗin ya fito. Inda take zaune gurin sofa Zafar ya ƙaraso, yana bin fuskarta da kallo cikin yanayin damuwa, kafin ya zauna kusa da ita, muryarsa a sanyaye kamar ba shi ba ɗan lokaci kaɗan da ya wuce, yana cewa, “Princess, please stop crying for me, yeah? You’ve shed more than enough tears yesterday—ya isa haka. Everything is going to be fine, I promise. Just calm down and let me explain myself first.” Ya faɗi hakan cikin wani irin lallashi mai ɗauke da kwantar da murya, yana ƙoƙarin kwantar mata da hankali bayan tashin hankalin da ya girgiza su duka. Ɗauke idonta tayi daga kansa, ta juya fuskarta gefe ɗaya tana ci gaba da kukan ta a hankali, hawaye na bin kumatunta ɗaya bayan ɗaya ba tare da ta share ba. Cikin sauri ya miƙe ya juya ya koma bathroom, ya ɗauko cream ɗinsa ya shafa wa jikinsa a nutse sannan ya fito. Closet ɗinsa ya shiga ya saka shorts ɗinsa da T-shirt, bayan ya fito daga closet ɗin ya isa inda Zara ke zaune, zuwa lokacin ta daina kuka amma ta cika tayi fam, fuskarta a ɗaure kamar hadari, tana ganin sa ta ɗauke kai ta maida kallon ta wani gefe daban. Hannu ya sa ya karɓi Jasmine daga hannunta a hankali, ya kwantar da ita a jikinsa cikin kulawa, sannan ya zauna kusa da Zara ɗin; hannun ta ya kama cikin nasa, yana riƙe da yatsunta a nutse yana kallon ta, yayin da ita kuma take kallon wani gefe daban, wasu sabbin hawayen takaici na zubo ma ta a hankali, tana cije leɓenta domin kar sautin kukanta ya fito. A sanyaye ya fara magana cikin lallashi, ya ɗan matsa kusa da ita yana bin yanayin fuskarta da idanu, “Ba ki san halin Baffa ba ne princess. He never acts on impulse—when he issues a threat, he’s already weighed every angle and locked in his decision, and nobody on earth can talk him out of it. The second he said he’d strip my title, I knew the exact script for this morning if I walked into the Nexus: public humiliation in front of the entire staff, forcing me to sign off on my own demotion, and handing me over to HR like some entry-level hire. I will never let myself be reduced like that, Zara. I’d rather walk away completely. We both know he still needs my brain, and I’ll gladly help him from home—but I will never be a subordinate in a building where I once called every shot.” Ya ƙarasa maganar a nutse, yana gyaɗa kai a hankali kamar mai tabbatar wa kansa da ita cewa wannan ne kaɗai mafita mai daraja a gare su. Tuni Zara ta sauko, fushin da ke ranta ya fara raguwa a hankali, jikinta ya yi sanyi sosai tana kallon sa cike da tausayin sa; ranta wani irin suya yake tana jin haushin abin da Baffa ya masa a kan wani da mai ma sani ba, wanda a ganinta bai cancanci haka ba ko me yayi kuwa. Tana kuka a hankali, muryarta na ɗan rawa da rauni, tace, “Still, Obim, we owed it to ourselves to try. How can we surrender everything without even putting up a fight?” Ɗan murmushi ya yi yana girgiza kansa a nutse, fuskarsa na ɗauke da wani irin yanayi na wanda ya riga ya hango nesa, yace, “Zara, ba ki san halin Baffa ba ne—you really don't know how unbending he is once his mind is made up. No amount of pleading was going to reverse his decision this morning. Let it go, princess; it’s all for the best, inshaAllah. Just be grateful I spared myself—and our family's name—the humiliation of watching my demotion splash across the media and become gossip for everyone in this city. Truthfully, I already see the silver lining in all of this: I have the experience, the network, and the drive, and now I finally have the push I needed. We’re going to build our own firm from the ground up, inshaAllah—something that belongs solely to us, where nobody can ever threaten to strip away what we worked for.” Shuru Zara tayi tana nazarin maganarsa daki-daki, tana jujjuya kowace kalma a zuciyarta; kallon sa take a nutse kuma tana mamakin yadda kamar ma daɗin abin yake ji, kamar ba wanda aka ce ya ajiye muƙami ba. Wani tunani ya zo ma ta a hankali, idanunta suka ɗan haska da wani sabon hope, kafin ta gyaɗa kai tana cewa, “It’s alright, Obim... you’re right, we can start our own firm from scratch. And look on the bright side—you’re Zafar Galado; your name alone carries serious weight across the industry, so doors are going to open for you regardless. And hey, you don't have to carry the financial weight alone either; don't stress for a second. I’ll back you with everything in my trust fund and my offshore accounts right on the table for us. We’ll merge everything we have and build an empire nobody can ever take from you.” Ta ƙarasa maganar tana zaro ido da ɗan zumuɗi, tana fatan hakan ya bashi ƙarfin gwiwan da zai dawo da farin cikinsa. Gyaɗa ma ta kai ya yi yana murmushi a nutse, murmushin da ke ɓoye da wani babban lissafi a ƙasan zuciyarsa, saboda hakan ne shima a ransa, sai dai manufarsu akan hakan da zasuyi yana da difference. Dabarar da ta zo ma sa daren jiya ita ce: zai karɓi dukiya sosai ta Zara sannan ya sa ka duk wani abu ɗa ya mallaka a duniya ya haɗa ya fara gina musu ta su rayuwar, tun jiya ya fara tsara komai a nutse kamar mai rubuta littafi; sai dai komai da sunan Zara da ƴarsa zai yi, komai! Zai kuma nuna wa duniya ba ko kobonsa a ciki—yanzu a ƙarƙashin dukiyar matarsa yake, he’s just a manager ko trustee da ke gudanar da kuɗi da kasuwancin matarsa. Duk wani abin ɗa ya mallaka zai maida shi sunan ta ɗa na ƴarsa, zaiyi asset transfer ya maida komai cikin trust fund ɗin matarsa da yarsa, kudi kuma yasa cikin kasuwancin matarsa. har share ɗinsa na Galado zai sa sunan Jasmine, jiyan tsab yabi kowane mataki da lissafi mai zurfi; ta haka ne zai yi maganin Rahama dama Yemma da ta ɗaure mata gindi a kan shegen cikin nan, in ma ta haifi cikin ɗan zai zo a zero, ga shi ita ma Yemma ɗin tuntuni komai na ta ya koma na Zwar, dan haka Rahama da uwarta sun yi aikin banza, dan ɗan da zata haifa ba zai samu ko asi dan lokacin da zai zo duniyar ya maida na Zara, kuma yawan dukiyar Zara da zai sa ciki shi zai sa babu wanda zai yi shakka, kowa zai yarda na ta ne kuma ita yake wa aiki. Gyaɗa ma Zara dake kallon sa kai ya yi a nutse yana cewa, “That’s my smart girl—I knew you’d see the bigger picture. Thank you for believing in me, baby. But your trust fund is off-limits; I refuse to touch your inheritance, I will never let you sacrifice your long-term security for my pride. However, I will accept what’s in your offshore accounts. I’m man enough to admit I need your backing right now, because on my own, I simply don’t have enough funds to pull off something this big.” Ya faɗi hakan ne cikin dabara dan har ita so yake ta yarda ba shi da komai, duk abinda ta gani yana so ta yarda dukiyar ta ce, ga shi ita daman Zara ba ta da zurfin fahimta a kan business ko wani kadara, ba za ta gane komai ba. Yana so ta kasance da cikakkiyar amincewar cewa komai nata ne, He wants her to have the confidence of she owns everything he’s running, ta haka ne mahaifiyarsa za ta fi yarda. Zara ɗake kallon sa cike da tausayi tace, “Hey, it’s totally fine—we have more than enough capital to launch properly. In no time, you’ll be back on your feet running your own empire.” Ta ƙarasa maganar tana kissing kumatunsa affectionately, pressing a warm kiss against his cheek, yayin da shi kuma ya narke ma ta yana kwantar da kansa kan ƙirjinta tare da miƙar da ƙafafun sa kan sofar, resting his head against her chest as Jasmine settled quietly between them, ransa fess dan yanzu ya samo maganin Rahama da iyayenta duk da still ba ya fatan ta haifi cikin nan ba ya yi komai a kai ba, wani calm, calculating satisfaction na settling beneath his quiet demeanor.