Nurul kalb

Page 5

by @khadijaharuna389


馃挒馃挒馃挒馃挒
bismillahir rahamanirrahim 


Tun daga ranar da mahaifinta ya dawo daga Dubai, rayuwar Sarah ta sauya gaba 蓷aya. Gidan da a da take jin da蓷in zama a cikinsa ya zama kamar gidan yari a gare ta. Duk inda ta juya, umarni da dokoki ne kawai take tarar wa.
Mahaifinta, Mr Williams, ya 茩ara tsananta mata fiye da da. Ya hana ta fita ko'ina,  Ya kuma umarci ma'aikatan gidan da su ri茩a sanar da shi duk lokacin da Sarah ta yi 茩o茩arin yin wani abu ba tare da izininsa ba.
Babban abin da yake tsoro shi ne kada ta sake Samun damar haduwa da Rahman. 
Sarah kuwa ba ta ta蓳a tunanin cewa za ta iya rayuwa cikin irin wannan takura ba. Duk da cewa tana cikin gida mai kyau, tana da komai na jin da蓷in rayuwa, amma zuciyarta ba ta samun kwanciyar hankali.
A wasu lokutan takan zauna kusa da tagar 蓷akinta, tana kallon lambun gidan ba tare da ta ga komai ba. Tunani ne kawai yake yawo a kanta.
Ina Rahman yake yanzu? Shin yana cikin koshin lafiya? Ko shi ma yana shan irin wannan azabar da nake sha? Shin zai iya mantawa da ni?
Tambayoyin da ba ta da amsarsu ne suke 茩ara mata ciwo.
A hankali ta fara 茩in cin abinci. Idan aka kawo mata abinci, sai ta 蓷an 蓷an蓷ana ka蓷an ta ture.  Ba wai ba ta jin yunwa ba ce, amma damuwar da ke zuciyarta ta fi 茩arfin duk wani sha'awar cin abinci.
Wata rana Emily ta shigo 蓷akinta da farantin abinci a hannu.
"Sarah, don Allah ki tashi ki ci wani abu. Tun safe ba ki ci komai ba."
Sarah ta 蓷aga kai daga kan gadonta. Fuskarta ta nuna gajiya, idanunta sun yi ja saboda yawan kuka.
"Ba na jin yunwa, Emily."
Emily ta ajiye farantin a kan teburin da ke gefen gadon, sannan ta zauna kusa da ita.
"Sarah, wannan ba wasa ba ne. Kin san yadda kika fara ramewa? Ko da yake dad ya hana ki fita, amma ba yana nufin za ki daina kula da kanki ba."
Sarah ta yi murmushi mai rauni.
"Emily, kina ganin zan iya ci kamar babu abin da yake faruwa? Kullum ina kwana da tunaninsa, ina tashi da tunaninsa. Ko na rufe idanuwana, shi nake gani. Na rasa ko da damar jin muryarsa."
Emily ta numfasa.
"Na san kina son shi, amma ki taimaki kanki. Kada ki bari wannan lamarin ya kai ki ga halaka."
Sarah ta juya fuskarta gefe.
"Ni kuma me zan yi? An hana ni ganinsa, an hana ni magana da shi. Kamar an yanke min wani 蓳angare na rayuwata ne."
Hawaye suka gangaro mata a hankali.
Emily ta rungume ta, amma ita ma ba ta san irin shawarar da za ta ba ta ba.
A wannan lokacin Sarah ba ta san cewa abin da ya fi tsoronta yana dab da faruwa ba.
Wato rasa hanyar jin muryar Rahman gaba 蓷aya.
---
Wata rana da yamma, Sarah tana 蓷akinta lokacin da wayarta ta fara 茩ara. Da ta duba, sai ta ga sunan Rahman a kan allon wayar.
Zuciyarta ta buga da sauri.
Da sauri ta 蓷auki wayar ta amsa.
"Hello..."
"Sarah, ya kike?"
Muryar Rahman ta fito cikin sanyin murya. Da jin muryarsa kawai sai hawayen da ta yi ta dannewa suka fara zuba.
"Rahman..."
"Me ya faru, sweetheart? Kina kuka ne?"
Sarah ta kasa magana na 蓷an lokaci. Sai da ta share hawayenta kafin ta ce, "Na yi kewarka sosai. Ban san ya zan yi ba. Kullum ina cikin 蓷aki, babu inda nake zuwa."
Rahman ya lumshe idanunsa.
"Ni ma ina cikin irin wannan halin, Sarah. Amma ki yi ha茩uri. Zan nemi mafita."
Kafin Sarah ta sake cewa wani abu, sai aka turo 茩ofar 蓷akin da 茩arfi.
Ta firgita ta juya.
Mahaifinta ne!
"Me kike yi?"
Sarah ta kasa amsawa. Hannunta ya fara rawa, amma kafin ta samu damar kashe wayar, Mr Williams ya 茩araso ya 茩wace ta.
"dawa kike waya?"
Sarah ta sunkuyar da kai.
"dad..."
"Na tambaye ki dawa kike waya
Ya 蓷aga wayar zuwa kunnensa.
"Hello! Wane ne?"
A 蓷aya gefen wayar, Rahman ya yi shiru na 蓷an lokaci.
"Ni ne Rahman."
Mr Williams ya 茩ara fusata.
"Ka saurare ni da kyau, Rahman. Ina so ka fita daga rayuwar 'yata. Kada ka sake kiranta, kada ka sake neman ta, kuma kada ka kuskura ka sake kusantarta. Ka fahimci abin da nake gaya maka?"
Rahman ya yi 茩o茩arin magana, amma Mr Williams bai ba shi damar yin hakan ba.
"Ba na son jin wani uzurinka. Ka rabu da ita!"
Ya katse wayar, sannan ya saka wayar a aljihu  Sarah
"Na yi miki garga蓷i sau da yawa, amma kin 茩i ji. Daga yau ba za ki sake samun damar magana da wannan mutumin ba."
Sarah ta kalle shi da idanu cike da hawaye.
"dad, don Allah..."
"Ki yi shiru!"
Ya nuna mata yatsa.
"Ba zan bari wani mutum ya lalata rayuwarki ba. Kuma ki sani, ba zan ta蓳a amincewa da wannan auren ba."
Ya fita ya buga 茩ofar da 茩arfi.
A wannan karon ba kawai an hana ta ganin Rahman ba ne, an kuma hana ta jin muryarsa.
---
Kwanaki suka fara ja, sannan suka koma makonni.
Sarah ta 茩ara ramewa. Fuskarta ta rasa haskenta, idanunta sun yi zurfi, jikinta kuma ya fara nuna alamun rashin 茩arfi. Abinci kusan ba ya shiga cikinta, ruwan sha ma sai an matsa mata sosai kafin ta sha ka蓷an.
Mahaifiyarta ta fara damuwa matu茩a. Sau da yawa tana shiga 蓷akin Sarah ta zauna kusa da ita, tana 茩o茩arin lallashinta.
"Sarah, 'yata, ki taimaki kanki. Ba zan iya jure ganin ki cikin wannan hali ba."
Sarah kan yi 茩o茩arin murmushi, amma murmushin ba ya kai wa zuciyarta.
Wata rana ciwon ya tsananta sosai. Sarah ta fara jin jiri, jikinta ya yi rauni, har ta kasa tashi daga kan gadonta.
Da farko aka kira likita zuwa gida. Ya duba ta, ya yi mata tambayoyi, sannan ya ba ta magunguna. Amma duk da haka, babu wani sau茩i mai ma'ana.
A 茩arshe aka yanke shawarar kai ta asibiti domin a yi mata cikakken bincike.
Mr Williams kuwa, duk da taurin kansa, wannan karon tsoro ya kama shi. Cikin 'ya'yansa, Sarah ce ya fi so. Ba ya son ganin wani abu ya same ta.
Da suka isa asibiti, aka kar蓳e ta aka fara gwaje-gwaje. Mahaifiyarta da mahaifinta suna zaune a wajen 蓷akin jinya, yayin da Emily da Daniel suke ta fargaba.
Bayan wani lokaci likita ya fito da sakamakon gwaje-gwajen.
"Mr Williams, ina so mu tattauna."
Mahaifin Sarah ya mi茩e da sauri.
"Yaya take, Doctor? Akwai matsala ne?"
Likitan ya yi shiru na 蓷an lokaci kafin ya amsa.
"Yanayin jikinta ya nuna cewa akwai babbar matsala da ta shafi damuwa da halin da take ciki. Ba wai rashin cin abinci da shan ruwa ka蓷ai ba ne. Akwai matsananciyar damuwa da ta da蓷e tana tattarewa a zuciyarta."
Ya 蓷an dakata, sannan ya ci gaba.
"Idan aka ci gaba da barin ta cikin wannan hali, akwai yiwuwar matsalar ta shafi lafiyar zuciyarta sosai. A yanzu muna bu茩atar ta sami kwanciyar hankali, ta fara cin abinci, ta sha ruwa, kuma a kula da yanayin tunaninta. Ina ganin abin da take bu茩ata ba magani ka蓷ai ba ne."
Mahaifiyarta ta dafe 茩irji.
Emily kuwa ta fara kuka.
Mr Williams ya tsaya cak. Maganar likitan ta yi masa nauyi fiye da yadda ya zata.
"Doctor, me kake nufi da abin da take bu茩ata?"
Likitan ya kalle shi cikin nutsuwa.
"Ina nufin akwai wani abu da yake damunta 茩warai. Dole ne ku fahimci abin da yake faruwa da ita, ku taimaka mata ta samu sau茩i. Kada ku 茩ara mata wani nauyin da zai tsananta mata."
Mr Williams bai sake cewa komai ba.
A karon farko, ya fara tunanin cewa wata茩ila tsananin da yake yi wa Sarah bai kawo mafita ba. Maimakon haka, yana iya zama sanadin abin da ya kai ta wannan hali.
Ya kalli 茩ofar 蓷akin da aka kwantar da 'yarsa.
Ya sauke ajiyar zuciya.
A cikin zuciyarsa, tunanin wata mafita ya fara tasowa.
RAHMAN 
A Dubai kuwa, Rahman yana cikin irin wannan hali.
Tun daga ranar da ya ji muryar mahaifin Sarah yana masa barazana, ya kasa samun nutsuwa. Kullum yana kallon wayarsa, yana jiran ko wata rana Sarah za ta kira shi. Amma babu kira, babu sa茩o.
Ya san ba laifinta ba ne. Ya san mahaifinta ne ya toshe musu duk wata hanya ta sadarwa.
Duk da haka, kewarta tana cin sa.
Ya daina zama da abokansa kamar da. Ko yana tare da su, tunaninsa yana can nesa. A wasu lokutan yana zama shi ka蓷ai, yana kallon hoton Sarah a wayarsa.
Umminsa ta fara lura da canjin da ya samu.
Da farko ta 蓷auka wata matsala ce ta aiki ko kasuwanci. Amma da ta lura yana 茩in cin abinci, sai ta fara damuwa.
"Rahman, zo ka ci abinci."
"Na 茩oshi, Ummi."
"Yaya za ka 茩oshi alhali tun safe ba ka ci komai ba?"
Rahman ya yi 茩o茩arin murmushi.
"Ba na jin yunwa ne kawai."
Ummi ta kalle shi da tausayi.
"茒ana, tun yaushe ne ba ka jin yunwa? Ko da kuwa kana da wata damuwa, ba za ka warware ta da yunwa ba."
Rahman bai amsa ba.
A hankali ya fara ramewa. Fuskar da a da take cike da fara'a ta koma ta damuwa. Ko da yake yana 茩o茩arin 蓳oye wa iyayensa abin da yake ciki, amma ba zai iya 蓳oye shi har abada ba.
Wata rana Ummi ta zauna kusa da shi, ta kawo masa abinci da kanta.
"Rahman, ina so ka ci wannan abincin. Ko ka蓷an ne."
Ya kalli abincin, sannan ya girgiza kai.
"Ummi, don Allah ki bar ni. Ba na iya cin komai."
"Me ya same ka ne, 蓷ana? Ka san ba zan ji da蓷i ba idan na ga kana cikin wannan hali."
Rahman ya sunkuyar da kai.
"Ba komai, Ummi."
Ta da蓷e tana kallonsa kafin ta ce, "Kana tunanin Sarah ne ko?"
Ya 蓷ago kai da sauri. Bai yi tsammanin Umminsa za ta fa蓷i sunan ba.
Ya yi shiru.
Ummi ta sauke ajiyar zuciya. Ta san 蓷anta yana son Sarah, amma ita da mijinta ba su ta蓳a amincewa da wannan soyayyar ba. Ba wai don ba sa son ganin 蓷ansu cikin farin ciki ba, amma suna ganin auren da mace Kirista zai kawo musu matsaloli, musamman bayan irin rashin mutuncin da mahaifinta ya nuna musu.
Duk da haka, ganin yadda Rahman yake lalacewa a gabansu ya fara ta蓳a zukatansu.
Ba su nuna masa tausayin da suke ji ba, domin ba sa son ya 蓷auka sun sauya ra'ayinsu game da auren.
Amma ba za su iya ci gaba da kallonsa yana shan wahala haka ba.
---
Wata rana Rahman yana zaune a falo, yana kallon wani wuri ba tare da ya san abin da yake kallo ba. Abin da yake tunani kawai shi ne Sarah.
Abi ya shigo falon, ya same shi cikin wannan yanayin.
"Rahman."
Rahman ya 蓷aga kai.
"Na'am, Abi."
"Zo ka zauna kusa da ni."
Rahman ya matsa ya zauna kusa da mahaifinsa.
Abi ya kalle shi na 蓷an lokaci kafin ya fara magana.
"茒ana, na lura da abin da yake faruwa da kai. Tun bayan wannan maganar da muka yi, ka daina zama cikin walwala. Ba ka cin abinci, ba ka barci yadda ya kamata. Me kake so ka cimma da wannan halin?"
Rahman ya sauke kai.
"Abi, ba na jin da蓷in wannan rayuwar. Na san kun 茩i amincewa da Sarah, amma ni ina sonta. Ban ta蓳a tunanin zan iya rayuwa ba tare da ita ba."
Abi ya yi shiru.
Rahman ya ci gaba da magana cikin murya mai rauni.
"Na san mahaifinta ya yi muku rashin mutunci. Na san abin da ya faru ya 蓳ata muku rai. Amma Sarah fa ba ita ce ta yi muku hakan ba. Me ya sa za a hukunta ta saboda abin da mahaifinta ya yi?"
Abi ya kalle shi sosai.
"Rahman, ba wai abin da mahaifinta ya yi ka蓷ai ne matsalar ba. Ka san ita Kirista ce, kai kuma Musulmi ne. Wannan ba 茩aramin abu ba ne. Ba za mu amince da auren da muka san ba za mu samu nutsuwa a cikinsa ba."
Rahman ya ha蓷iye yawu.
"Amma Abi, ni ba na neman wani abu sai ita."
Abi ya yi ajiyar zuciya.
"茒ana, ka rabu da ita. Ka ba kanka lokaci. Wata茩ila  ka manta da ita."
A wannan lokacin Rahman ya ji kamar an zare masa numfashi.
Ya kalli mahaifinsa, sannan ya yi 茩o茩arin magana.
"Abi... kar ka ce min in rabu da ita."
Amma kafin ya 茩arasa maganar, sai ya dafe 茩irjinsa. Fuskarsa ta sauya, idanunsa suka fara juyawa, sannan jikinsa ya fa蓷i a kan kujera.
"Rahman!"
Abi ya mi茩e da sauri ya ri茩e shi.
"Rahman! 茒ana! Ka naji na?"
Ummi da ke kusa da su ta ji ihun Abi, ta shigo da gudu.
"Me ya faru?!"
"Ummi, kawo ruwa da sauri!"
Ummi ta 蓷auko ruwa ta zuba masa ka蓷an a fuska, amma Rahman bai motsa ba kuma jikinsa ya yi sanyi.
Tsoro ya kama su.
"Ya Allah! Rahman!"
Ba su 蓳ata lokaci ba. Aka kira ma'aikatan gidan, aka taimaka aka 蓷auke shi zuwa mota. Abi ne ya zauna kusa da shi yayin da direba ya yi gaggawar nufar asibiti.
Ummi kuwa tana ta addu'a, hawaye na zuba a fuskarta.
---
Da suka isa asibiti, ma'aikatan jinya suka kar蓳i Rahman da gaggawa. Aka kai shi 蓷akin kulawa ta musamman, aka fara duba yanayinsa.
Abi da Ummi sun zauna a wajen 蓷akin. Ummi ta kasa daina kuka.
"Ya Allah, ka bashi lafiya. Ka taimake shi."
Abi bai ce komai ba. Ya zauna yana kallon 茩ofar 蓷akin, zuciyarsa cike da fargaba.
Bayan wani lokaci likita ya fito.
Abi ya mi茩e da sauri.
"Doctor, ya 蓷ana?"
Likitan ya kalli su duka, sannan ya ce:
"Yanayinsa ba shi da kyau sosai a yanzu. Ya samu matsananciyar damuwa, kuma hakan ya fara shafar lafiyarsa. Muna 茩o茩arin daidaita yanayinsa."
Ummi ta share hawaye.
"Zai samu sau茩i kuwa?"
Likitan ya yi shiru na 蓷an lokaci.
"Ina fatan zai samu sau茩i. Amma akwai wani abu da nake so ku fahimta. Idan akwai wani abu da yake matu茩ar so, wanda rashin samunsa yake jefa shi cikin wannan hali, to ina ro茩onku ku yi 茩o茩arin taimaka masa. Kada ku 茩ara masa damuwa. A yanzu ciwon ya fara tsananta."
Abi ya yi shiru.
Likitan ya 茩ara da cewa:
"Yana bu茩atar kulawa, kwanciyar hankali, da goyon bayan iyalinsa. Kada ku 蓷auki wannan a matsayin 茩aramin abu."

Ummi ta zauna tana kuka, yayin da Abi ya tsaya a tsaye, hannayensa a ha蓷e a bayan jikinsa.
Ya tuna da maganar da ya yi wa Rahman a gida.
Ka rabu da ita.
Ya tuna yadda 蓷ansa ya kalle shi kafin ya fa蓷i.
A hankali ya zauna.
A wannan karon, ba wai kawai yana tunanin 茩in amincewa da auren ba ne. Yana tunanin yiwuwar rasa 蓷ansa idan ya ci gaba da tsayawa kan wannan matsayar.
Ya 蓷aga kansa ya kalli Ummi.
"Ummi..."
Ta kalle shi cikin hawaye.
"Me ya faru?"
Abi ya girgiza kai a hankali.
"Ban san abin da ya kamata mu yi ba."
Ya yi shiru na 蓷an lokaci, sannan ya 茩ara da cewa:
"Amma ba zan iya kallon 蓷ana a wanan yana yinba 
A zuciyarsa, tunanin wata mafita ya fara fado masa 
A 蓳angarori biyu na duniya, Sarah da Rahman suna kwance a asibiti, kowannensu yana fama da ciwon da ba magani ka蓷ai zai iya warkarwa ba. Kuma iyayen da suka tsaya a matsayin katangar tsakaninsu sun fara fahimtar cewa wata茩ila soyayyar yaran nasu ta fi 茩arfin abin da suka yi zato.