KAYAR RUWA

8

by @halimahz

Wucewar wasu kwanaki lamari ya ƙara taɓarɓarewa tsakanina da Mijina.
Abun ya koma tamkar sa hannu, bai bar ni da yunwa ba, zan ci in sha, amma babu zaman lafiya sam, na rasa kwanciyar hankali da jin daɗi daga gare shi, komai na yi ba daidai ba ne, abinci idan na yi ba ko da yaushe zai ci ba, magana idan na yi, sai ya ga dama zai amsa min.

Makarantar tahfeez ɗin da na ke zuwa ya soke, ya ce in har da aurensa akaina na gama zuwa makarantar, to ya fini ilimin balle in ce baƙin ciki yake in fi shi, mugunta dai kawai.
Idan na zo masa da buƙatar wani abu ranar sai ya yi tamkar ya tashi gidan da wuta, ya dinƙa masifa ban da aiki sai shegen bani bani, kamar don ni kaɗai ya ke neman kuɗinsa.

Ahh lamarin fa idan da kishiya tsab sai zuciyata ta yarda ita ta mun asiri ta raba ni da shi.
Kullum a nurƙufanci ya ke, fuska ba wata walwala, ya dinƙa ƙunci da ɗacin rai, ba zan san fitarsa ba, haka ba zan san dawowarsa ba.

Maimakon na tattara shi na watsa gefe, amma inaa, na zama mayyarsa, ina sonsa da yawa ba zan iya ba.
To zaman hakan ne na ga ba zai kai min ba, na tambaye shi jari. Kun san sai da na yi danasanin tambayarsa. Saboda buɗar bakinsa cewa ya yi,"Wai ke neman kuɗin da na ke yi, ce maki na yi saboda ke kaɗai ne? Sa'ida kin sakawa dukiyata ido, sam ba ki da godiyar Allah, menene ba na yi miki? Ko so kike na sakar miki duniyar mu cinye lokaci ɗaya, idan na talauce ki ce ba za ki zauna da ni ba ko?."

Maganganunsa sun mun min ciwo. Amma wallahi ko kusa ban iya tanka masa ba. Wani lokacin na kan yi tunanin ina iliminsa ke tafiya.
Sai da ta kai ta kawo idan zan mutu ina ciwo, wallahi sannu ba zai ce min ba, haka zan ƙara ci ciwona in warke, babu ganin likita balle magani. Anan na ga ranar ace mace na sana'a.

Sai ranar ma da ya ɗan ji tausayina ina matsanancin ciwon kai, ya siyo paracetamol kwali guda ya bani, wai in ajiye saboda gaba, kar ciwo ya kama ni in zo masa da zancen magani ko asibiti, wannan ya ishe ni ko da ciwon ajali na ke.

A yadda muka saba rayuwa, duk abin da zai siyo na amfanin gida, ni na ke yi masa list, akwai abinda kuma shawarata yake nema, sai ya ce,"Kin ga abu kaza na gani Bashir yana siyawa gidansa, kina ganin ya yi muma mu dinga saya?".

Amma yanzu sai dai ya kira Yaya, duk abin da tace shi zai yi.
A haka tace da shi nama da kayan marmari da ya ke ajiyewa ya daina, don ta lura ina masa almubazzaranci da kayan abinci, kuma ɗiba na ke ina kaiwa gida ba tare da saninsa ba.

Abubuwan baƙin ciki su ka taru su ka min yawa. Yadda ku ka kasan mara gata haka na ke rayuwa a cikin gidan nan. Har kwanan yau ban san babban laifin da na yi ba, da hakar yake hukunta ni ta hanyar ƙuntata min haka. 
To an zo gaɓar da fita ma kwata kwata ya hana ni. Rasuwar da aka yi ta wata Kakarmu, mutumin nan haka ya rufe ido babu kunya babu tsoron Allah yace ba zan je ba.

Sai da ƙyar ya bar ni, na sha kuka wajen magiya da roƙo. Kuma a hakan sai da ya gasa min babu daɗi kafin ya bar ni, ya gama ci min mutunci da cewa,"Ai idan kin fita gulma da munafurci ke fitar da ke. Da koyo fitsarar wulaƙanta aure da dangin Miji."

Tun daga wannan furucin na sa kuwa na cirewa raina son fita, dama ni ba wani fitar na ke yi ba, ko gida sai na jima ban je ba. Kuma yanzu ya zamana ko zuwa gida bana son tambayarsa, gani na ke kamar kallon duk sadda zan je gida ina ɗeba masa abinci ina kaiwa yake min.

A ɓangaren Rumana da Atika kuwa, zuwansu gidan bai haifar da Ɗa mai ido ba. Don zuwan nasu ne ma ya ƙara nesanta tsakanina da Hubbi.
Yara su ka zamar min annoba, ta silar su ne hargitsi ya girmama a cikin gidan aurena, har akansu ina neman na kamu da ciwon zuciya. Idan ɓacin rai ya yi ɓaci, haka zan dinga jin zuciyata na yi min zafi sosai. In ta haki, ƙarshe dai paracetamol zan afa na sha, ina jin ciwo sosai a zuciyata amma na kasa zuwa asibiti, saboda ko na tambayi zuwa ba barina zai yi ba. Sai dai duk idan ciwon ya motsa min, in tofa bismillah da fatiha a ruwa na sha, ina sha ɗin kuma zan ji na samu salama na nemi ciwon na rasa.

Duk abin da ke faruwa, wani ɓari na zuciyata na gaya min in ɗauki mataki, idan ba haka ba baƙin cikin Nazifi da Ƴan uwansa sai ya zama ajalina. Amma sai ɗaya ɓarin zuciyar tawa ya zo ya kore wannan huɗubar, ya bar ni da cewa komai zai wuce. In ci gaba da haƙuri kawai, addu'a na maganin komai.

Da ace ina da wanda na ke amayar wa da damuwata, atleast zan na samun sauƙi. To ni haka Allah ya yi ni, komai ya faru da ni tun yarinta ni ɗaya na ke shanyewa. Ko Babata sai tayi ta fama in faɗa mata abin da yake damuna, amma bana faɗa sai dai na ce babu komai. Ita kuma sai ta min nasiha ta ce barin kashi a ciki baya maganin yunwa.

A halin da ake ciki kwata kwata ba ya min magana. Tattara ni ya yi ya watsar kamar shara. Idan magana tsakaninsa da ni ta zama ta dole, zai faɗawa ɗaya daga cikin Yaran ne su faɗa min.
Shi yasa ma yaran suka raina ni. Cikinsu ba wadda na isa na yi mata magana, sai ta min rashin kunya da fitsara, dama na faɗa muku a baya, yaran ba su da mutunci, ko Family kuka ake da halinsu.

Haka su ke kallon tsabar idona su faɗa min ai Abbansu ba ya sona, don haka suma ba sa sona. Idan na ba su abinci sai su ce ban iya girki ba, ba za su ci ba. Shi kuma idan ya dawo sai ya hau kan ƙaryar da suka gilla masa ya zauna, haka zai kira ni ɗakinsa ya ci mutuncina, ya dinga faɗa yana maimaita idan ina son zaman gidansa to wallahi kar na ƙara hana yaransa abinci.

Yaran nan tsabar ba su da tarbiyya, ba su iya su ga na yi baƙo su gaishe shi ba. 
Wata rana Ya Imam ya zo, suna zaune a parlon amma ƙirmisisi suka ƙi gaida shi. Yana musu magana irin na Babba yaga yara zai ja su a jiki, amma suka yi masa banza. Raina kuwa ya ɓaci na tsawatar musu, na ci mutuncinsu, ai wallahi sai su ka ƙara bayar da ni, don miƙewa su ka yi suna turo baki gaba suka wuce suka barni a tsaye cike da kunyar Ya Imam, kuma ba su gaishe shi ɗin ba.

Ranar dai har dare ban ƙara jin motsinsu ba, suka ƙule a ɗaki. Da yake basa cin abincina, su kan sakko su ɗauki cake da lemu a fridge, shi su ke ci da rana. Da daddare kuma dama kullum ne zai shigo da kaza to ita suke ci abincin dare.
Amma ranar saboda na musu faɗa sai suka yi zuciya ba su ci na rana ba, haka suka wuni da yunwa.

Hubbi na dawowa suka ce masa na zazzagesu, na ce zan kore su daga gidan. Suka ta rantse masa akan sai da suka gaishe da Yayan nawa, yaƙi amsawa.
Ranar na yi kuka na gode Allah, zagi na cin mutunci da ƙare dangi ya yi min a gaban yaran.
Wannan dalilin na cin zarafina da ya ke a gabansu, sai ya ƙara ba su lasisin yi min duk abin da suka ga dama, kun ga dai yara shekara takwas amma ya nuna musu ni wulaƙantacciya ce.

Ni ji na ke har gwara sharrin kishiya akan na su. Abin da suke yi min gwara na san kishiya ce ke min. Saboda idan su ka kunna wata wutar bala'in, zaka rantse da Allah ba ƙananan Yara ne suka kunnata ba. Ga shi sun ƙware a kirsa, kirsar da duk mai hankali yana gani ya san ba tunanin yaro ba ne, dole saka shi aka yi.

So tuni na tsinke da lamarin su, don na gane karanta musu komai aka yi kafin dawowarsu gidan.  A gabansa ladabin da su ke yi min kamar Uwarsu, amma da zarar an ce bai gidan, duk wadda ta ganni ma sai dai ta yi min tsaki. 
Na kuwa faffalawa Atika mari ranar da ta min tsakin, ina ga tsoro ta ji da yadda na fusata, na ga dai ba su faɗa masa ba har kwanan yau.

Akwai ranar da na ke musu faɗa akan ƙin zuwa makarantar da suka tsira, hakan sai ya zama tashin hankali. Ya ishe min a ɗakin yana ɗaga min murya. Faɗi yake. 

"Saboda ba Ƴaƴanki ba ne, ba kuma Ƴaƴan ƴan uwanki ba, saboda nawa Ƴan uwan sun bani, zaki nemi ki takurawa yara, ki ce za ki hanasu sakewa a gidana da na gina da kuɗina. To ki cire idonki daga sha'aninsu, tunda ba akan ki su ke zaune ba, kuma ba ke kike ɗaukar nauyinsu ba. Haba! Duk kin mayar da ƙananan yara kamar kishiyoyinki, me suka tare miki?"

A lokacin kuwa na masa daurewa innyi shiru nace masa.
"Yanzu Hubbi kai daɗin cin zarafina kake yi a gidan nan? Har rawar jiki ka ke yi ka ga ka ci min mutunci akan Yaran nan. Sai su kitsa maka abu ba zaka iya zuwa ka ji ta bakina ba, haba don Allah, abinda kake yi baka kyautawa."

Buɗar bakinsa sai ce min ya yi.
"Ni kike mayarwa da magana saboda ba ki da mutunci? Shikenan ki ƙara maimaitawa ki gani. Kuma na faɗa miki, ki fita a sha'anin Yarana, bana so kike takura musu, idan ba haka kuwa zamu samu mugun saɓani da ke."

A hankali nace masa. "Allah ya baka haƙuri. Gata na yi musu dai tunda akan zuwa makaranta na takura musu. Amma tunda an nuna ba a so su yi karatun, na fita sha'anin makarantarsu in sha Allahu. A ba su gata yadda ya kamata."

"Magana za ki faɗa min kenan?"

"Ka ga don Allah, don Annabi ka yi haƙuri Hubbi. Ni bana son rigima da tashin hankali."

Ina faɗar haka na buɗe alƙur'anin da yake hannuna. Shi kuma ya fita a ɗakin ransa a matuƙar ɓace.

Ta ɓangaren ƴan uwansa kuwa sun taso ni gaba da gorin haihuwa. Ba su tsaya iyaka nan ba, har faɗi su ke wai me ake da auren ƴan talakawa.
Sam ba su ga abin da aurena ya tsinanawa Ɗan uwansu ba, banda tawaya da yaja masa, da sun san haka aurena zai zamar wa ahalinsu masifa, da ba su bari ya aure ni ba. Ni kuwa kullum cikin tunanin masifar da na zame musu nake yi.

Idan na shiga cikinsu tamkar mushe, sun ta ja baya da ni suna habaici. Haka na ke zama saniyar ware a cikin facaloli.
Ranar da muka haɗu a gidansu ana taron Family, Anty Aisha ke min gori akan da aka auro ni, haka na zo babu kayan gara.

Ƙalilan cikinsu ne fa ma su tausaya min, sauran duk daga kyara sai hantara. Na rasa wannan bala'i. Shi yasa na kama kaina, na ja gefe don wulaƙancin na su ya fara min yawa.
Yanzu sam bana so ma abun shiga cikinsu ya ta so. Aka ce haƙuri idan ya yi yawa cuta ne. Na yarda da hakan wallahi. Amma duk ranar da na ce zan fanɗare, ba su isa su min kallon banza ba, to bana son tashin hankalin iyayena da damuwarsu, sannan kuma ina tsoron abin da zai jawa igiyar aurena samun matsala, Allah ya gani bana so aurena ya mutu.

Duk wannan matsaltsalun da ke faruwa surukata ta sani. Ina ta zuba ido in ga ta tsawatar akan abubuwan da ƴaƴanta su ke min, amma na ji shiru. Abun mamakin sai na ga tana goyon bayansu, itama ta hau kan layinsu, ta mayar da ni kamar kishiyarta.

Ƴaƴanta su yi min, Ɗanta ya yi min, itama ta yi min. Gaba ɗaya na rasa ta ina ƙiyayyar ta soma, na rasa me na musu a rayuwa.
Idan na basu haƙuri fa sai ya ƙara zama wani babban laifin. Amma abin da na lura da shi, ba akan rashin haihuwa kaɗai yasa su ka tsane ni, su ke tsangwamata ba, akwai wani dalili na su a gefe, wanda suka barwa kansu sani.

Tabbas babu babban tashin hankali a gidan aure irin ace uwar miji ta sanyo ka a gaba, ni da ban san wani matsalar uwar miji ba, tsagwaron soyayyarta na sani.
Idan na ji mutane suna ƙorafi akan uwar miji, sai in ce kune dai baku iya zama da ita ba.

Ita Uwar miji sonta ake tamkar mahaifiya, haka ma a yi mata biyayya kamar ita ta haife ki, kuma ta haifeki ɗin tun ta haifa miki Mijin da kike alfahari da aurensa. Da tarin soyayya gami da biyayya za ku mallake uwar miji a tafin hannu.
Ban mantawa duk sadda na faɗi haka, ƙawata Hassana Tijjani kanyi murmushi kawai, sai tace.

"Sa'ida ba za ki gane ba, in uwar miji na sonki, tana sonki kawai, in kuwa bata sonki, to wallahi duk Son da Ɗanta ke miki, zaman auren ba zai taɓa yi miki daɗi ba. Idan kuwa tana Sonki, to ko Ɗanta ba ya sonki kya samu salama, saboda zata na tilasta masa yi miki abinda bai niyya ba, kuma dole ya yi saboda ya rabu da ita lafiya. Idan mai tsananin son kyautatawa Uwa ne, sai ki rabauta ya so ki, albarkacin son da mahaifiyarsa ke miki."

Ta yi murmushi mai ciwo. Kamar tana da tabob ciwo akan hakan. Kana ta sake cewa.
"Idan kuwa uwar miji ta sako ki agaba, duk wani kalar biyayya da za ki yi mata a banza ne wallahi. Tana da power ɗin da umarni ɗaya zata bayar akan a baki farar takarda, kuma ba a isa aja da cewarta ba."

Ashe hakan da take faɗa gaskiya ne, domin kuwa ga shi ina ga ni. Kallon banzan da Iyam ke yi min ba ƙaramin tsorata ni yake yi ba. Idan na zauna sai na yi ta mamaki.
Duk wannan tashin hankalin da na ke ciki, iyayena da ƴan uwana babu wanda ya san me yake ke faruwa. Don ban taɓa faɗa ba, kuma ban taɓa nunawa ba.

Sai dai duk wanda ya yi min farin sani, yana ganina zai ce ina cin matsala, hankalina ba'a kwance yake ba, bana jin daɗin rayuwar da na ke.