FreeArewaPen original
DUHUN ZUCIYA
- 1views
- 14chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Army of BTS💜
Sample · Page 1-5
Bismillahi Rahman Rahim.DUHUN ZUCIYA 2021SHAFI NA ƊAYAPharty BBWattpad PhartyBB...'Ina ma ni ce a wannan yanayi da lokacin? Ina ma duniyata zai canza zuwa ga mafarkina? Duhun da yake kewaye ya gushe ya zamto haske. Koyaushe zan samu haske? Wa zai cire ni daga duhun da yake lulluɓe da zuciyata? Tsawon lokaci hasken cikin rayuwata ya gushe. Ko wacce rana ina tsumayin wanda zai haskaka duniyata.'"Radiyya! Radiyya!!"Sunan da ya shiga kunnuwanta cike da karaɗi da amo ya sa ta dawowa daga duniyar tunanin da ta tsunduma kanta.Firgigit Radiyya ta amsa tana duban wacce ta ƙirata tare da faɗin."Ki ka ce me?"Ba ta damu da yanayin da take ciki ba. Kullum uzurinta shi ne a gaba da rayuwar wani. Ba ta duba da rayuwar wani na kusa balle ta fahimci halin da ya ke ciki.Mugun kallo take watsa mata, duk da ta sunkuyar kanta ƙasa balle ta hango.Kalmar da ya fara fitowa daga bakinta shi ne."Ubanki na ce...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.