FreeArewaPen original
Fataucin Bayi
- 1views
- 9chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Fataucin Bayi chapter 1
Fataucin BayiLittafi na ɗayaRubuta labariMansur Usman SufiSarkin Marubutan yaƙi***Tafkeken jirgin ruwa ne da aka cikasa maƙil da fursunoni maza da mata,manya da yara ƙanana,gaba ɗaya fursunonin ɗaure hannayen su suke da waɗansu murtuka-murtukan sarƙoƙi kuma an haɗa da katakon jirgin an ɗaure tamau,Ta yadda babu mai iya guduwa daga cikin su, Duba ɗaya zaka yiwa fursunonin ka fahimci cewa sun kasance jama'ar ƙabila ɗaya,Abinda zai tabbatar maka da Hakan shi ne yanayin kirar jikin su da kamannin su gami da tufafin su iri ɗaya ne sak!A wannan lokaci jirgin ruwan na tafiya ne a saman wani makeken teku,A kowa ce kusurwa a jirgin an zuba dakaru masu tarin yawa, dukkanin su shirye suke cikin gagarumar shigar yaƙi hannayen su ɗauke da miyagun makamai, suna ta kai komo domin tabbatar da cikekken tsaro,Sai da jirgin ya shafe tsawon Sa'a biyu da dakika ɗari biyu yana tafiya a saman tekun batare da watsala ba,Tekun ana kiransa da suna Baharul-sawara.Ana cikin wannan tafiya ne Wani garjejen kato daga cikin dakarun ya dubi wani badakare wanda da alama shine shugaban su ya risina a garesa yace" Ya shigabana ina ganin Yakamata a kwance waɗannan fursunonin a basu abinci domin sun galabaitu ainun,Tabbas a koda yaushe zasu iya rasa rayuwar su,kuma kasan cewa mutuwar ɗaya daga cikin fursunonin tamkar rasa rayukan mu ne baki ɗaya, koda jin wannan batu daga bakin badakare sharkar sai shugaba Yasiran ya dube sa cikin kakkausar murya yace" sai Yakai sharkar tabbas kazo da shawara mai kyau,Amma fa wani hanzari ba gudu ba,shin baka tsoron kunce fursunonin zai bada matsala a tare damu?Koda jin wannan tambaya sai sharkar Ya bushe da dariya yace" Haba ya shugabana ka du ba fa kaga irin tsananin yawan mu, taya ya kake tsammanin cewa akwai wanda ya isa ya tsere mana.Yanzu shawara biyu ce ta rage mana kodai mu bawa waɗannan fursunonin abinci domin su rayu,Ko kuma mu kyale su yunwa da ƙishirwa su zamo ajalin su.Sa,adda shugaba Yasiran ya yi wannan batu daga bakin sharkar sai "Tabbas zancen ka dutse ne ya zama dole muyi amfani da wannan shawara,Yana gama faɗin hakan ya umarci waɗansu dakaru mutum arba'in suka kwance fursunonin mutum ɗari biyu, sannan suka rarraba musu wata bushasshiyar gurasa gami da wani ruwa mai yauƙi a matsayin abin kalacin su,Dakarun na cikin rarraba musu gurasar ne wani badakare ya miƙawa wata yarinya gurasar,Kafin hannun badakaren yakai inda na yarinyar yake, yarinyar tayi shammace sa ta ciri wata yar siriyar wuka a jikin sa ta caka masa a marainan sa, sannan ta sanya kafafun ta biyu tayi daki kafafun badakaren ya wuntsila izuwa Cikin tekun yana mai tsandara ihu,Al'amarin da ya janyo hankalin sauran dakarun kenan, suka zubar da abincin dake hannun sa suka zare makaman su suka ruga izuwa inda yarinyar take, koda ganin hakan sai yarinyar ta ɗauko wat...
App exclusive
Continue “Fataucin Bayi” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.