FreeArewaPen original
๐บ๐บ K'ADDARA CE ๐บ๐บ BOOK 1
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample ยท Chapter 21/ 22
_*๐บ๐บK'ADDARA CE ๐บ๐บ*_Book 1STORY AND WRITING BY_Sarat Alk'asum ( Maman Nusaiba ce)__Wannan littafin na kud'i ne ki biya kisha karatu Hajiya ta__Nomal N300 ne__Vip N 500 ne post sau biyu kullin__*Domin k'arin bayani ku tintib'eni ta *** number na + 966599791573*_๐๐*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐*_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_*** ุงููู ุงูุฑุญู ู ุงูุฑุญูู _21/22_Hanan ji tayi kamar ta saki zawo saboda tsananin tsoro daya cika mata zuciya dama gangar jiki, jin ya kuma had'a ta da jikin shi sai ta saddakar yau ai kawai Yaya Faris Fad'e zai mata.. Shi kuma gogan yana kallon ta bako k'iftawa so yake yaga iya gudun ruwan ta da k'arfin ta, shi yasa ya matse ta kamar wata Y'ar shi, Hannun shi ya cire daga bakin ta daya rufe mata...Da sauri Hanan Ta matso hawaye Ta ce." Yaya Faris please ka cikani! Wallahi kila ka karya min kafad'a wannan matsa haka kamar ka samu soban wasan ka! To nidai ka sakeni ko kuma Anty na zuwa nace mata ka rumgume ni kamar wata Baby Jaririya. Ta k'arshe maganar tana turo mishi bakin ta.....Murmishi Yayi yana binta da namujiya , ji yake kamar ya maida ta ciki dan so da k'aunar da yake mata, sai dai ita tsoron shi ma takeyi, baisan yaushe zata dena jin tsoron shi ba a matsayin shi na Mijin da zata aura ba. Ajiyar zuciya ya sauke Ya ce." To shikenan naji zan sakeki amma sai kin min alk'awarin bazaki k'ara jin tsoro na ba! Idan kuma naga tsoron na nan to Wallahi gobe sai naje wajan Baba ya daura mana aure in ta tsoro kuma, wai ma meye ร jikina wanda in kika ganni kike tsoro na? Haba Hanny bana son kina jin tsorona nifa Mijin kine Insha Allah!Kara turo baki Tayi tana k'unk'unen magana Ta ce." Kaji wani sabon salo gemu a kafad'a! Tab ikon Allah ikon gaske wai kiran salla da usir kut! Wai hadda cewa nifa Mijin ki ne, kaji neman guri a wajan Yaya Faris hmm, to bazaa dena jin tsoron naka ba! Ni ai ba Matar ka bace da har kake rumgume ni saika bari inka aure ni kake tab'a ni ai ko! To saina dena zuwa Gidan naku ma ehee....Duk maganar da t...
App exclusive
Continue โ๐บ๐บ K'ADDARA CE ๐บ๐บ BOOK 1โ in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.