FreeArewaPen original
Ƙarshen Zalunci
- 1views
- 11chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Karshen Zalunci
ƘARSHEN ZALUNCIRubuta LabariMANSUR USMAN SUFIWthapp Number***Littattafan MarubucinTAFARKIN TSIRAKOGON ANNOBAJARUMAN DUNIYAKANGIN BAUTAFATAUCIN BAYITAKOBIN ƊAUKAKASARAUTAR MUTUWASARKIN SADAUKAIGOGA SHA FAMAKARYA DA GASKIYAKARSHEN ZALUNCIKUNDIN AL'AJABIBABI NA ƊAYA Wata mata ce mai shekaru talatin sanye da kayan fata riga da wando, ɗauke da juna biyu a jikinta ke ta faman tafiya babu sassauci, A wasu lokutan har tuntuɓe take yi ta faɗi ƙasa, amma sai ka ga ta miƙe tsaye da ƙyar ta ci gaba da tafiya a cikin kasaitaccen birnin ma'abocin dogayen gine-gine. Sa'adda ya zamana ta shafe rabin rabin sa'a tana wannan tafiya sai kishi ya addabeta sakamakon tsananin zafin rana. Duba ɗaya za ka yi mata ka fahimci cewa tana cikin matuƙar buƙata, domin ƙafarta ko takalmi babu. Lokacin da ya zaman ta shafe sa'a ɗaya cur tana wannan tafiya sai kawai ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a dai-dai wannan lokaci ne wani saurayi ma'abocin kwarjini da haiba ya durfafo inda take, yayin da ya iso daf da ita sai ya durƙusa bisa gwiwoyinshi. domin ya ga mene ne ya same ta cikin alamun tashin hankali. Nan take ya lura cewa tsananin kishi ne ya addabe ta har ta yanke jiki ta faɗi, cikin matuƙar kaɗuwa ya ciro wata salka dake maƙale a kwiɓin cinyarshi ta dama ya buɗe murfin. sannan ya sanya hannunshi ɗaya ya tallafo wuyan matar ya kafa mata salkar ruwan a baki, take ta shiga kwankwaɗar ruwan har sai da ta sha ya ishe ta, tana kammalawa sai ta ja gwauron numfashi sannan ta yi ajiyar zuciya ta miƙe zaune tana mai ƙurawa saurayin idanu hawaye na zuba. Al'amarin da ya bawa saurayin mamaki kenan kuma ya ji ya kamu da matuƙar tausayin, ya dubata cikin damuwa ya ce “Ya ke wannan mata shin ina dalilin wannan zubar da hawaye naki? Koda jin wannan tambaya sai hawaye suka sake kwaranyowa daga idanuwanta kuma ta yi shiru ba tare da ta ce uffan ba. Daga bisa ne ta buɗi baki muryarta na rawa ta ce. "Ya kai wannan saurayi ma'abocin tausayi da jin ƙai ka yi sani cewa a halin yanzu ba zan iya baka amsar watdannan da ka yi mini ba. Kuma bani da abin da zan saka maka bisa wannan taimako da ka yi min sai dai kafin mu rabu ina neman wata alfarma guda daya a wajen ka.” Cike da mamaki saurayin ya ce, "Ke kuwa wace irin alfarma ki ke nema a gare ni?" matar ta yi murmushin karfin hali, sannan ta ce "Alfarmar ta farko da nake nema a wajenka ita ce, ina so ka taimake ni da abin hawa haɗe da guzuri, sannan ina so kar ka bayyana labari na ga wani domin matsawar wani ya sani tamkar ka rushe taimakon da kayi mini ne.” Da jin wannan batu daga bakin matar sai saurayin ya sake cika da tsananin mamaki, kuma hankalinshi ya dugunzuma ainun ya faɗa kogin tunani, abu...
App exclusive
Continue “Ƙarshen Zalunci” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.