WA GARI Ya WAYAFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

WA GARI Ya WAYA

  • 1views
  • 1chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1

ME GARI YA WAYARubutawaMARYAM IBRAHIM LITEE(labarin zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta.)Chapter OneSai ƙarfe ɗaya muka shiga kaduna,kayan kwalliyata na ciro na kuma gyara fuskata,Na goggoga turaruka a jikina.Ina nuna ma direba hanya muka isa har gidan,Horn direba yayi,ina niyyar sanar ma shi ba megadi ya saurara,aka wangale get ɗin,wani wanda ban taɓa gani ba sai a yau,shi ya buɗe,ya kuma iso wurin yana tanbayar wurin wa muka zo.Ni na yi ma shi bayani,haƙuri ya shiga bani kafin ya soma gaishe ni.Motar ta kunna kai cikin gidan,Megadin ya biyo mu da sauri,na fito ina kallon yanda aka ƙara gyara gidan,taɓe baki nayiƙila sanda zai yi amarya ya yi gyaran.Direba ya shiga fito min da kayana,megadi ya kira Garba me wanki wanda shi na bari kafin tafiyata Lagos.Kuɗi na ciro wanda babansu laila ya bani da naje yi ma shi sallama,ya ce ba lallai ina da kudin nan ba in riƙe za su yi min amfani.Nayi ma direba alheri na sallame shi,Megadi da Garba suka biyo ni da kayana,Knocking nayi a ƙofar main falon, daga ciki aka bada izinin shigowa,Takun ƙwas ƙwas da takalmina ke yi yasa mazauna falon maido hankalinsu inda nake,Zaune suke a kujerin da suka yi wa falon ƙawanya dukkansu har megidan.Megadi da ke bayanaya tanbayi inda za a ajiye min kayan,Ƙofar ɗakina na nuna masa,Zama nayi ɗaya daga cikin kujerun,kowace da irin kallon da take min,kafin suka soma min sannu da zuwa,nayi mamakin canzawar su,mun gaisa na gaida megidan,suka bi ni da kallon ita ɗin ce koko wata aka canzo bayan na miƙe zuwa ɗakina.Key na fiddo cikin hand bag ɗina,na buɗe dakinina cusa kai mamaki ya rufe ni dan ko ina a gyare yake tsaf yana tashin ƙamshi,  Ba alamar an daɗe ba a yi amfani da shi ba.Jakata na ajiye na cire takalmi,na koma kofar daki na shigo da jakunkuna naBasma ce ta shigo abinci ta miƙo min,na ƙarba tare da godiya cikin wani bala'in mamaki da ya kara rufe ni game da matan na TahirNa dai ajiye nayi alwala nayi sallah,da na idar na ji cikina yana bukatar abinci,amma zuciyata bata nutsu in ci wanda aka kawo min ba dan ni dai ina ta mamakin canjin nasu.Wani danbun nama da laila ta sanyo min cikin kayana na ci sai na sha ruwa,canza rigar jikina nayi zuwa wasu riga da wando masu santsina koma bisa kujera na miƙe ina latsa wayata.Tahir ya shigo,Zaune na tashi ina ƙara gaishe shi ban samu amsawar shi ba illa faɗan da ya lullube ni da shi,Mutum shi da iyalin sa an nuna masa iyakar shi,ana ma shi iko da matarsa.Shiru nayi ina sauraren shi,zuciya na kawo min wuya,kamar in ba shi amsa sai na kasa,har ya ƙarewai kuma sai yana faɗa min ni zan yi girki yau,komawa nayi na kwanta Na ce "Gaskiya a gajiye nake ka bar me girki ta kare girkinta in ya zagayo kaina sai in yi".Wani kallon mamaki ya kafe ni da shi,"Saboda me?&...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters1
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play