RUMFAR KARAFree

ArewaPen original

RandomFreeOngoing

RUMFAR KARA

  • 1views
  • 3chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

Sample · Farko

Tana gaba, Alheri na biye da ita a baya, suka kutsa kai cikin wani tafkeken falo na alfarma, wanda aka ƙawatashi da kayan alatu na more rayuwar duniya , masu masifar kyau da tsada. Madina ta kalli Alheri ta ce " Zauna ki jirani, bari na karɓo na zo mu tafi.” Tana faɗin hakan bata jira abin da zata ce ba, tabi wata matakalar benen da aka ƙera ta da wani kalar ƙarfen silba, ta haye sama. Tsayawa Alheri ta yi tana ƙarewa falon kallo, tare da tunanin maƙudan kuɗaɗen da aka kashe wajan ƙawata wannan lafiyayyan falo, ta yi imani da Allah da ranar lahira, duk wanda ke kwana ya tashi a wannan gida, zai yi wuya ya yarda in aka ce masa akwai waɗanda ke kwana su yuni ba su samu na kaiwa bakin salati ba. Sai da ta zaɓi wata luntsumemiyar kujera daga cikin kujerun sannan ta zauna, ta ci gaba da tufka da warwarar rayuwa "Alheri bulus.” Kamar daga sama ta ji wata kakkausar murya cikin amsa amo na ambatar sunanta. Fargaba gami da mamaki suka taru suka mamaye kirjinta, da sauri ta juyo tana kallon inda sautin muryar ke daɗa fitowa, kanta ne ya fara juyawa yayin da falon ya fara girgiza tamkar zai ruso mata, tana miƙewa ta ga falon ya rikiɗe ya ko ma wata tafkekiyar maƙabarta. Cikin tashin hankalin ta miƙe da ga kan kujerar wadda ita ma ta rikiɗe ta koma wani ƙaton kabari. Sannu a hankali ta fara bin muhallin da kallo, wanda ya cika ya batse da manya da ƙananan ƙaburbura tamkar an jerasu ne domin ƙawata muhallin, wata tsohuwar mace ta hango sanye da jajayen kaya, tana tsallake ƙaburburan tana tunkaro inda take, bakinta a wangale ɗauke da wawakeken wawulo, sai wani ɗan ƙaramin haƙorin da bashi da maraba da na gafiya, sai faman ɓaɓɓaka dariya take. Kasa matsawa ta yi da ga inda take, sai ma ƙoƙarin kamo addu'ar da za ta ba ta kariya take yi, amma abin ya ci tura, haƙoran sama da ƙasa ta ji sun haɗu sun datse, kwata kwata ta ka sa furta koda kalma ɗaya. Har matar ta ƙaraso gabanta dariya take tana ƙare mata kallon sama da ƙasa, sai da ta yi mai isar ta, sannan ta dakata ta kalli Alheri ta ce, " Barka da zuwa Rumfar Kara Alheri Bulus, bai kamata ki yaudari kanki wajan mamakin ganinki a wannan muhallin ba, bayan kin san aikin dake gabanki, da tarin nauyin ƙungiyar da ke kanki wanda kika kasa saukewa shekara da shekaru.” Ta yi taku ɗaya zuwa biyu, sannan ta yi murmushi ta kalli Alheri ta ci ga ba da faɗin.” Me ya sa kike bawa ƙungiya da ahlinta wahala Alheri? Me kike so a duniya wanda ƙungiya baza ta iya miki ba? Idan so kike kifi kowa arziƙi, mulki, gami da kyau, babu wanda baza mu iya samar miki ba a duniyar nan.” Ta sake ɓarkewa da wata dariyar, wannan karon har da hawaye, sannan ta ci ga ba da faɗin, " Lokaci ya yi da ya kamata mu sanar dake ruhinki a tafin hannun rumfa ya ke, duk wani motsi da al'amuranki na rayuwa muna biye dake.” Tana gama faɗi...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “RUMFAR KARA” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play