FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Book 1 (Farko)
Bisimillahir Rahmanir RaheemDAN WAYE???Ko ina cikin gidan a hargitse yake. Wasu kayan cikin akwatuna, wasu cikin kwalaye, wasu kuma an tara su gefe an lullube su da manyan mayafi farare, ko ba’a tambaya ba alamu sun nuna mutanen da ke gidan suna shirin barin gidan ne. darfe bakwai na yamma agogon dasar London ya nuna a halin yanzu. Gaba daya mutan gidan suna zaune bisa datuwar darduma suna cin abincin dare. A cikin su babu mai Magana, kowa dibar abinci yake yana kaiwa bakin sa rai bace tamkar masu cin magani. daya tak a cinkinsu ya yake cin abinci hankali kwance. Abban sun a laura da kowa, dan murmushi yayi kafin yayi gyran murya yace, “Amma dai yaran nan ku nab a ni mamaki, yanzu, saboda za ku bar kasar nan shine kuke wani cin magani kamar wadanda aka yi wa mutuwa? “Yayi dan guntun tsaki sannan ya ci gaba, “Ko kun so, ko kun di, Najeriya itace kasar ku!”matashin dake kusa da shi ya dago...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.