BESTIEFree

ArewaPen original

Short StoryFreeOngoing

BESTIE

  • 1views
  • 1chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Rubutunka Tunaninka

More from @kyfagge

Sample · BESTIE

BESTIE(gajeren labari)Ban fi mintuna biyar da tsayawa a ƙofar gidan su Ziza ba ta fito, fuska fal da murmushin ƙauna."Amincin Allah ya tabbata a gare ka.""Tare da ke amaryata."Za mu tsunduma hirar soyayya Fesal ya iso wurin. Gabaɗaya hankalin Ziza ya koma kan shi. Sallama kawai ya yi yana kallona, na amsa masa, ya tattara hankalinsa kan Ziza. Sun yi tsayuwar gwamen jaki daf da daf har suna jin numfashin juna."Tawan." Cewar Fesal."Na'am nawan. Ya aka yi, daga ina?"Ziza ta amsa masa."Ai kin sani ba sai na faɗa ba. Kawai zan fita ne na zo ki ban na mota da katin waya."Ziza ta kalle ni."Habu ba shi dubu biyu."Kamar zan fashe saboda kumbura."Wai ke Ziza mene..."Ta katse ni."Ka ga Habu don Allah saurara. Na ga ɗanyen kishi a fuskarka kana neman zazzage mana shi. Sau nawa kake so in gaya maka.""Ki gayan me?""Au har ka manta?""Na manta ɗin tuna min.""Yanzu kuwa." Ta kalli Fesal. "Sorry Bestie, bari in yi masa tariyar baya.""Yi masa my b ko ya gane 'the D is c'."Ta kalle ni."Ranar farko da ka ce kana so na, me na gaya maka?"Na tuno. Gaskiya ne, a ranar sai da ta kira Fesal a waya, ya zo wurin da muke, a gabansa ta sa na maimaita abin da ya kawo ni gareta, na ce.“Ina son ki Ziza, na zo ki karɓi soyayyata."A lokacin ta kalli Fesal."Ka ji abin da ya ce, mene ne shawararka Bestie?"Fesal ya kalle ni sosai."Tawan gayen ya yi fa, ki karɓi soyayyarsa kawai.""Shikenan, na karɓa je ka."Fesal ɗin ya tsaya bai tafi ba."Ba ni wani abu."Ta kalle ni."Habu ba shi dubu biyu."Jikina na rawa na ba shi. Ya karɓa. Ya yi sumba a hannunsa ya hura mata a fuska suka yi lallausan murmushi, ni kuma saurayin ina bin su da kallo kamar kurege, sai da ya tafi na yi ajiyar zuciya."Shi kuma wannan wane ne shi a wurinki?"Dariya ta yi."Kishin ya motsa? To ba saurayina ba ne.""Wane ne?""He is my best friend, na gani na faɗa, ba ni da ƙawa ko aminiya da ta kai shi. He is my bestie.""Bestie?""Yes. Kar fa ka damu, shi ma yana ƙaunarka tun da ka ga ya amince in karɓi soyayyarka."Haka muka ci gaba da soyayya da Ziza, ina ganin abubuwa tsakaninta da Fesal, sai ka rantse mijinta ne, ni kam na ga tijara, so ya rufe min ido na rasa yin komai face zuciyata da ke jigata. Har aka sa mana ranar aure.Da bikin ya matso, kusan kashi tamanin na shirye-shiryen bikinmu da Ziza, Fesal ne ya tsara shi, shi ya raka ta wajen ƙunshi da kitso da sauran wuraren da ya kamata amarya ta je.Haka nan, takwas daga cikin hotunan 'free-wedding picture' da muka yi yana ciki, biyu ne kawai muka yi babu shi.A ranar dina (dinner) na ƙara tabbatarwa da kaina na zama surkududu.Na cancare cikin koriyar shadda mai ƙyalli a ɗakin dinar muna jiran ƙarasowar amarya da ƙawayenta, can sai ga ta ita da Fesal cikin shuɗin boyel sun yi anko. Gabaɗaya aka tashi ana yi musu tafi saboda sun yi kyau matuƙa."Riƙe fa suke da hannun juna!" Na ce da a...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters1
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play