FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Sunana Halima.hz, ni marubuciya ce, kuma ƴar kasuwa mai siyar da nau'ikan sutturun sawa da mayukan gyaran gashi. Ina rubutu don in rayar da abubuwan da mutane ke ji. Ba na rubutu don nishaɗi kawai, ina rubutu don motsa tunani. Kowanne labarina yana ɗauke da murya...
Sample · 1
SIRRIN ƁOYE©️Halima.hzHalimahz@arewabooksHalimahz@WattpadHalimahz@BakandamiyahikayaNa fara da sunan Allah mai Rahama mai jin ƙai. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga Fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.1)A komai nawa cikin kazar-kazar nake yinsa, ban cika yin abu da sanyin jiki ba ko yanƙwana, hakan yasa da yawan ƙawaye koma ƴan gidanmu, kai hattama da Gwaggona lokuta da dama su kance min mai jikin maza.A durƙushe nake ƙofar dakalin ɗakin Inna Amarya ina gyara tsinkakken silifas ɗina, wanda yasha jiki ya gaji da duniya, dan yanzu ma da baƙar leda nake ɗaure shi, ina gama gyara shi na zira a ƙafafuna masu ɗauke da zara zaren yatsu, na gyara zaman fuskar hijaɓ ɗina, na kuma ƙara tallafar allona da kyau, sannan na duƙa tare da ɗaga labule ina cewa Inna Amarya na tafi makarantar asuba.Bata amsa ba hakan ya bani tabbacin ko bata ɗakin ko kuma bata tashi a bacci ba, saboda haka na zare takalmina na faɗa ɗakin, na ƙaro hasken wutar aci bal-bal saboda ɗakin ya sami wadatuwa da haske kasancewar duku-dukun asubahi ne, ile kuwa sai naga Inna Amarya riƙe da carbi hannu tana lazimi ta ɓingilar da kai gefe tana bacci, nayi murmushi na ƙarasa gabanta, kallonta nake cike da so da ƙauna da kuma tausayawa, na sanya tafukan hannuna na tallabi fuskarta na haɗe goshinta da nawa, ananne kuma ta buɗe ido ta zuba su cikin nawa, tayi firgigit da son farkawa daga baccin da take tunanin gyangyaɗi ne take yi."oni Shatu, yanzu Allah kuwa Mairo baki wuce kin tafi makarantar nan ba, sai Malam ya fito ya ganki kija min magana, ko kuma kije a dakeki Kabiru ya tada jijiyoyin wuya yana hayagaga an taɓaki, shikenan yay ta sakawa ana sauya miki makaranta sai kace ke ɗaya ce ƴar gata".Duk wannan maganar da Inna Amarya keyi acikin faɗa take yinta, maimakon na yunƙura na miƙe kamar yanda take saka ran ganin nayi, saima na gyara zama tare da lafewa ajikinta, cije leɓe nayi ina ƙoƙarin danne dariyar dake neman suɓuce min saboda yanda naga ta saki baki galala tana kallona. Bata ce min uffan ba haka nima kuma ban kuma cewa komai ba, sai ƙara narkewa da nake ajikinta tamkar magen data sami katifar auduga.Tsawon mintunan da baza su wuce uku ba sai naji tayi ƙwafa kafin tace, "Allah ya shigo da Amadu nan kusa bada jimawa ba". Dariya na ƙyalƙyale da ita, na ɗago kai ina kallonta nace,"Inna idan ya shigo me zai yi miki?". Ba tare data dubeni ba ta ƙarasa tasbihin da take sannan tace, "ya shigo nace masa sauran ƴaƴa duk sun wuce makaranta ke kina nan a zaune". "idan yazo hukuntani kuma ki hana ba". Na faɗa ina ƙara ƙanƙameta ina murmushi, inata jiyo takun sauran yaran gidan na wucewa makaranta. Buɗar bakinta zatayi magana aka ɗaga labule, Gwaggona ce bakinta ɗauke da sallama, aciki na amsar sallamar sai Inna Amarya wadda ta amsa a fili suna gaisawa."ai zanbi bayanta sai Zulai take ce min ta shigo na...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.