FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Barka da zuwa shafin littattafan SUMAYYAH ABDULQADIR TAKORI
Sample · Book 1 (Farko)
YAR NAJERIYA FARKON FARI (HASNA 'YAR INNAR TA)N a taso cike da dokin ranar zuwan ziyarar ‘yan makaranta, ba don komai ba sai don na san Inna zata kawo min kanzo, kuli da kwaki, wadanda su ne abinda nake samu a kowanne visiting, sabanin sauran dalibai masu uba a raye, idan aljihun Inna da dan nauyi (in ta samu surfe mai yawa) kafin zuwan ranar ziyarar mu to tana hadomin da mankuli wani lokacin har da busashishiyar yakuwa (rama) wadda zan dade ina jikawa ina kwadantawa.Makarantar mu makaranta ce ta hadakar ‘yan Najeriya (UNITY COLLEGE) wadda nayi nasarar samu sabida hazakata ba don ina da gatan zuwan ta ba. Duk fadin kauyen mu na fi kowa kwazo a karatun boko da na muhammadiyya har wani suna ake kira na da shi (Huda-Huda ‘yar Inna) wasu su ce (Mungu Park ‘yar Inna) sabida tsabar son karatu na da son Inna ta.Bayan son karatu Allah yayi ni da tsafta, wadda aka ce it ace cikon addini, duk da irin halittar da yayi min wadda ta banbanta data sauran al’umma, kai bazaka ce girman kauye bace kuma tashin kauye sabida yadda nake kula da tsaftar jiki na. Tsaftar da Inna ke kan ce aljanu ke sani yin ta, domin ta wuce misali. Na taso ban san kowa ba sai Inna ta ban kuma shaqu da kowa ba sai ita, mahaifi na tun ina ciki ya rasu, kuma nice kadai diya ga iyaye na. Sannan ba kowa ke son mu’amala da iri na ba (da mutum mai irin halitta ta).Mahaifi na Mal. Dabo dan asalin karamar hukumar Kabo ne ta jihar Kano, wanda sana’ar sa ta iyaye da kakanni itace ‘jimar fatu’. Da wannan sana’a yayi aure ya kuma rike Inna ta da mahaifiyar sa Kaka A’I. kakata A’I bata tare da mu yanzu haka tana can garin Kabo.Mahaifiya ta ‘yar asalin garin Kachako ce inda ci-rani ya kai mahaifi na ya auro ta, bayan auren su ya taho da ita garin su wato Kabo suka zauna gida daya da mahaifiyar sa A’I. duka-duka auren bai rufa shekara biyu ba ciwon ajali ya kama mahaifi na Malam Dabo, kuma bai dade yana jinya ba ya amsa kiran mahaliccin sa.Mahaifiya ta Inna Zulai ta cigaba da rainon ciki na a gidan mahaifi na har ta haife ni. Na zo da halittar data barranta data kowa a gidan mu, ga dai kyau har kyau amma zabiya ce, don haka ni ban gado fatar jiki na ba a wajen iyaye na kudurar Ubangiji kadai ta sa aka haife ni haka.A lokacin ne manema suka fara kawo mata caffa, don haka A’I tace ta yaye ni ta bata ni ta samu ta yi aure, amma Inna ta kafe kan cewa ita ba auren da zata yi raino na kawai zata yi har karshen rayuwar ta, sabida irin halittar da Allah yai min, da ba kowa ke son raba ta ba, sannan bata son tayi wani aure da zai sa a kira ni AGOLA.Zaman mahaifiya ta da kakata A’I sai ya canza salo bayan rasuwar mahaifi na, sabida A’I ta dage sai ta yi aure shine mutuncin ta kuma ta gaji da dawainiya da mu, ta kan ce da wannan zabiyar ‘yar taki wadda ba miji zata samu ba. A karshe ba tare da shawara da ita ba ta...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.