FreeArewaPen original
RAYUWAR RAYHANAH
- 1views
- 8chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Barka da zuwa shafin littattafan SUMAYYAH ABDULQADIR TAKORI
Sample · Book 1 (Farko)
RAYUWAR RAYHANAH! 1Garin TAKAI, karamar hukuma ce dake cikin birnin Kano, galibin jama’ar Takai Fulani ne da Hausawa farare da bakake, duk inda bahaushe da bafillace suke babbar sana’arsu Noma da Kiwo, manoma da makiyaya sune kashi tamanin cikin dari na jama’ar garin. Kowa ya san jama’ar Takai ya san su da hadin kai da taimakon junan su, rashin son zaman banza, sana’o’in dogaro da kai musamman saye da sayarwa na abinda suka noma da karfin su ko suka kiwata. Kowa a garin Takai kokarin neman na kansa yake babu wanda ya dogara da wani ba ga mazan kadai ba har matan manya da yara, tsofaffi, ‘yammata, da samari da wuya kasamu wanda baida sana’a, domin neman rufin asirinsa da iyayen sa ko iyalinsa.Kasuwar Takai tana ci ne ranar Talata. Don haka kamar kowacce Talatar, Malam Rashidu, yana nan bakin kasuwa ya baza hajarsa kwano-kwano cike da dankalin Hausa (Sweet Potatoe). Tun karfe goma na ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.