FreeArewaPen original
AN YA BAIWA CE?
- 1views
- 20chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · SHAFI NA ƊAYA
*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️*ANYA BAIWA CE?* Na*AMEERA ADAM* _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR ***,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ FREE PAGE 1 Tafe take tana ɗan waige dan gudun kar wani ya ganta ko taci karo da wani a hanya, saboda abin da ta gano take san zuwa ta isar da shi ko ta samu ɗan alheri, aikuwa batayi aune ba tana shiga soron tsakiya suka yi gware da mutum a zabure ta ja da baya tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce tayi tseren gudu, kallan tsaf yayi mata yana karantar yanayinta yasan tabbas akwai abinda ke ƙunshe cikin bakin ta, aɗan diriri ce ta kalle shi ta ce. "Yautai mugun tsuntsu masha miyarka sai yayi dare" Kallanta yayi sai da yayi murmushin gefen baki yana ƙara karantar yanayin ta sannan ya ce, " Tauraruwa mai wutsiya..., Kura kike ga tsoro ga ban tsoro. Ina zaki kike sauri kina ta juye-juye haka? " Sai da ta juya hagu da dama ta kuma leƙa soron ƙarshe tana mai miƙa wuya cikin ƙasa da murya ta ce, " Gobara daga teku maganin ta sai Allah, wata ƙura ce take ƙoƙarin kunno kai a cikin gidan nan amma karka ce kaji daga baki na " ta ƙarasa magana tana kuma duba gabanta da bayanta. "Jakadiya Kubura kenan, ay harbi ga ɗan jaki gado ne, kuma iya ruwa fidda kai gayamun ina sauraron ki kowa ya biya allon sa ya wanke " ya faɗa cikin son jin labarin. Sunkuyowa tayi dabda shi sannan ta ce, " Kasan koda girgiza kurna tafi magarya, mai tsoron a mutu shi yake maho " Ƙara gyara tsayuwarta tayi sannan ta ce, " Ƙaramar kyauta tafi babbar rowa " ta ƙarasa faɗa tana miƙa masa hannu alamar ya bata wani abu. Ya gano abinda Jakadiya ta ke nufi, dan haka ya sa hannu cikin aljihu ya ɗebo mata silallah ya zuba mata akan hannun ta yana faɗin, " Ke dai ciki kike mai manta kyautar jiya, kuma Kura kike mai manta alherin baya" Juya su tayi cikin jindaɗi ta kunto bakin zaninta ta ɗauresu tana faɗin, " Domin rana ɗaya ba'a ƙin zuguri, kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan langa, buɗe kunnen ka yanzu zaka sha labari, ashe Fulani Zaliha ciki gareta har ya girma, kasanta da shegen nunkufurci ba ta cika bada fuska a shiga sashenta ba " zaro idanu yayi waje shima yana waigen bayansa sannan ya ce, " Lallai tsugunne bata ƙare ba ansai da kare an sayi Mage, naji daɗin wannan albishir naki jeki anjima zan neme ki " ya faɗa yana yin gaba abinsa. &nbs...
App exclusive
Continue “AN YA BAIWA CE?” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.