FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
I’m a bilingual writer of over 20 complete books and over 200 books in my drafts. I’ve been writing since 2017 and enjoy what I do! Reading my books is one of the things you’d thank yourself for doing!
Sample · Daya
Da hanzari ta tsallaka titin dake gabanta, gudu take kar ace ta makara, kar wani abu ya samu tilon y'arta. Yanzu idan wani abu ya faru da Hanan ina zata saka rayuwarta? Hawayen dake zubowa saman kuncinta tayi kokarin sharewa a hankali. Zata daure, Insha Allahu duk ynda zatayi dole ne ta sama ma kanta yanda zata sama ma Hanan lafiya. Tsayawa tayi bakin kofar asibitin tana kallon shige da fice na mutane. Wasu suna fita da ihu da kururuwa alamar wani nasu ya rasu, wasu kuma suna dariya alamar lafiya ta samu. Wasu kuma suna shiga cikin rudu, firgici da tunanin yananin da dan'uwa ko yar uwarsu take ciki. Duniya kenan, nan ita yanda take a hakan tana ji duniya ta mata kunci, wani nacan yau yake farin cikin da bai taba irinshi ba. Share hawayenta ta karayi tana mai kokarin fitar da murmushi saman kyakyawar fuskarta, wacce a yanzu idan ba mutum ya kura mata ido ba bazai taba cewa tana da kyau ba. Takawa tayi har dakin da aka kwantar da Hanan. Ko yanzu taga likitar data kawosu dakin nan sai ta kara gode mata, dan baccin ita da batasan abunda zatayi da ranta ba. Dan kila ko ciwon Hanan bai dauki rayuwarta ba, to allergy din da take fama dashi sai ya dauki rayuwarta. Hanan bata san mutane ko kodan, idan a waje mutum ya wuce biyar to tabbas yanzu zata fara numfashi kuraje su fara fito mata, musamman yanzu lokacin zafi, gashi indai maganar zafi ake akazo Katsina an gama magana. Saboda Hanan ko fita batayi...kukan dataji tanayi ne ta window yasa ta katse duk wani tunani da take ta ruga ta shiga dakin. Da hanzarinta ta karasa gadon Hanan tana me rungumo ta a jikinta, "Hanan, har kin tashi baccin? Sannu, ya jikin?" Tambayar da take mata kenan tana tallabota a hankali kamar wacce tsoron ta fashe. "Akwai zafi Ummi, ban iya numfashi sosai," fadin Hanan kenan hawayen na fita tana wani kuka a hankali wanda dagaji kasan ba karamin jin jiki take ba. Saurin maida hawayenta tayi tana murmushin karfin hali, "Karki damu kinji, Hanan? Insha Allah zaki samu lafiya, ai yau da sauki kadan ko?" Duk yanda taso ta daure ta nuna ma Hanan cewar babu wani abu, duk tazo magana sai ta kasa. Sauran kashe da tsokar daya rage a jikin yar shekara biyar shine take girgizawa a hankali tana juya kanta, "Ummi ance idan aka mutu ba'a jin zafi ko? Bacci kawai zanyi kafin a kaini makarantar Annabi Ibrahim."Hawayen da take kokarin maidawa ne suka zubo, duk idan Hanan tayi maganar nan sai taji zuciyarta ta kare. Hannayenta ta riko a hankali tana mai sumbutarsu a hankali, hawayenta na diga a sama, "Kinaso ki tafi kibar Ummin ki ne, Hanan? Ni in kika tafi ya kikeso inyi?" Kawo yanzu kuka yaci karfinta, ta rasa duk fadin duniya inda zata saka rayuwarta. "Ummi ki daina kuka, kinji? Idan ina nan nike saki kuka, amma idan na tafi ai zasu barni inje inga Abba na ko?" Wani i...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.