ALHERIFree

ArewaPen original

Non-fictionFreeOngoing

ALHERI

  • 1views
  • 6chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Barka da zuwa shafin littattafan SUMAYYAH ABDULQADIR TAKORI

More from @takori

Sample · Book 1 (Farko)

SHIMFIDALAGOS, 25 WATAN ZULKIDAHRanar Talata ce, cikin watan Zul’kidah, garin Lagos kamar koyaushe cike yake da cunkoson ababan hawa, babu masaka tsinke ; musamman da yake a daidai lokacin kowa na kokarin kai wa gida domin tsira daga duhun dare da samun hutu. Ma’aikata sun taso, suna son isa gida domin yada kafada, haka ‘yan kasuwa sun rurrufe shaguna an bar wa gobe cinikin in Allah ya kai mu. Da misalin karfe shida na yamma kenan.Daidai lokacin ne Rukayyah ta sauka a garin Legas cikin jirgin kasa, wanda ya dauko ta tun daga Yola. A kalla kwanan su biyu cur cikin jirgin don haka Rukayyah ta gaji likis, ta yi fiyat irin na kowanne matafiyin da wahalar zaman jirgin kasa ya koda. Doguwar Bafillatana, santaleliya, mai dauke da kayatacciyar doguwar fuska ma’abociyar zati da kamala. Wadda Allah ya wadata da kayatattun idanu farare kal. Babban sirrin kyawun RUKAYYAH USMAN JALINGO, shi ne gassun girarta masu kauri, bakake sidik wadanda ke zane zirit kamar shatar siririn watan da bai fi kwana biyu da bayyana ba.Rukayyah ma’abociyar kwalliya ce, don haka ne duk da gajiyar da ke tare da ita, da idanunta da suka fada, in ka dube ta sosai za ka hango bayyanannen kyawun fatar ta da jambaki ruwan hoda mai sulbi da ta mulke siraran lebbanta, wanda ya dace da launin shaddar Ghalilahdark pink da ke jikinta. Dinkin jikin ta babbar riga ce Senegalese har kasa da zane, tana yafe da dan kankanin gyale, launin kayan jikinta, amma mai haske wato light pink, wanda ya fi shaddar haske. Hannunta na dama sakale da babbar jakar mata ta hannu baka kirar Yue Jin ‘yar kasar China, mahadin bakin takalmi mara tsayin dunduniya da ke kafarta.Kasancewar ta yafa gyalen a kafadunta ne, yasa bakin gashin kanta mai santsi da sulbi ya bayyana ta kasan dankwalinta, wanda ke kunshe cikin tafkeken ribbon ruwan hoda. Kai da ganin Rukayyah ka san ba ta fito daga kankanin gida ba, abin nufi, kanta a waye yake, idanunta a bude farare sol. Kai tsaye ta fito daga (rail-station)wato tashar jirgin kasa cikin takun nutsuwa, tana tura ‘yar jakar kayanta troller mai matsakaicin girma zuwa inda ta hangi tadi-tadi masu jiran mai daukar su drop (shata).Tun kafin ta karasa gare su wani direba ya taso ya karbe ta, yana mai tambayarta inda za ta je, fuskarta babu walwala ta ce, "BGC, Road 2, G134."Cikin mintuna ashirin sun iso kofar tangameman gidan, mai dauke da irin girgijejen (gate) din nan na zallar farin karfe, da akewa lakabi da (Mahdi-ka-ture). Ta bude kofar motar ta fito, shi ma ya fito ya bude (boot) din motar ya fiddo mata jakarta, ta kirgo kudin da ta tabbatar sun fi karfin abin da zai tambaya, ta mika masa. Hannu bibbiyu cikin rawar jiki Bayaraben ya sanya ya amsa, yana ta zuba mata godiya kamar ba zai daina ba. Ba ta kara bi ta kan shi ba, ta karasa jikin (gate) ta kwa...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters6
premium5
02

Book 1 (Karshe)

Premium
Updated 6 days agoAvailable now
03

Book 2 (Farko)

Premium
Updated 6 days agoAvailable now
04

Book 2 (Karshe)

Premium
Updated 6 days agoAvailable now
05

Book 3 (Farko)

Premium
Updated 6 days agoAvailable now
06

Book 3 (Karshe)

Premium
Updated 3 days agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play