GOBE DA NISAFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

GOBE DA NISA

  • 1views
  • 63chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Army of BTS💜

More from @phartybb

Sample · Page 1

Ahlin gaba ɗaya idan ka dube su farin ciki suke da murna domin samun wannan karuwar abin da basu zata ba, wanda suke ganin abu ne mai wuya samun shi, duk da ya kasance murnar wasu a ciki suke hakan bai sa sun bayyana a fuskarsu ba suka bari a zuci. Ƙaramar walima aka haɗa a gidan, aka ci aka sha kowa na taya wacce abin farin cikin ya sameta murna.Idan ka dubeta kuwa yadda kyakkyawar fuskarta take annuri zai ba ka tabbacin tana farin ciki da wannan rana, burinta ya cika saura mafarkinta da kaso sittin shi ne abin da ya taimakawa rayuwarta tsawon rai. Jama'a da dama suna ganin hakan ba mai yiwuwa bane saboda kankantarta kuma mace ce.Sunanta ta ji an ƙira, ta juya tana amsawa wacce ta ƙirata cikin sanyin muryarta na marar son hayaniya. Kanwar mahaifiyarta ce Aunti Babie, cikin murmushi ta ce."Zamu wuce gida Mariya, Allah ya taimaka yasa a shiga a sa'a."Mariyatul Kibdiyya cikin muryarta mai daɗin sauraro ta ce."Amin Aunti na gode. Sai na zo muku.""Babu komai, ai ke yanzu babu zama."Aunti Babie ta faɗa tana saka yaranta a gaba suka fita a falon, Zakiyyah tabi bayan mahaifiyarta tana yiwa sauran ƴan matan sallama sai bayan kwana biyu.Suna fita Mariyatu, Haneefa da Ummi Aisha suka gyara falon ganin yadda aka mayar a hargitse. A haka kowa ya watse wanda suka zo tayata murna aka bar ƴan gidan. Suna gamawa ɗakinsu suka wuce, kai tsaye bathroom suka yi rige rigen shiga ganin magriba ta yi, alwala suka yi suka gabatar da sallah, kasancewar cikinsu a cike yake basu bi takan abincin dare ba kowace ta nemi guri ta zauna tana ɗaukar wayarta. Haka suka zauna suna chat suna hira jifa jifa wanda duk Haneefa da Ummi Aisha ne, Mariya daga umm sai a'a nata, haka har dare ya yi suka gabatar da sallar isha'i. Bayan sun idar suka fita suka yi wa Umma sai da safe suka dawo ɗaki suka kwanta.Washegarin ƙarfe bakwai da rabi cib Mariya da Haneefa suka gama shirinsu na tafiya aiki. Mariya yau ne ranar farkonta, wanda dalilin samuwar aikin yasa ahlin haɗa mata walima jiya a gida suka zo yi mata murna.Haneefa cikin uniform din nurses fari, ta yi kyau abinta.Mariya kuwa cikin bakin doguwar riga baki, sai baby hijab fari da ya rufe kirjinta, ya haska farin fatarta ya fito mata da tsantsan kyawunta, duk da bai kamata ba hakan baya hana mutum hango zubin halittarta. Fuskarta fiyau babu wani kwalliya sai hoda da man baki da ta sanya don girmama dokokin aikinta.Bayan sun gaishe da Umma a gurguje suka hau yin breakfast da mai aiki ta gabatar jera a dining. Haneefa ce ta fara gamawa ta miƙe, ta kalli Umma da take zaune ta ce."Umma wai Abba bai farka ba.""Yana falonsa."Umma ta faɗa daga inda take zaune tana duba wasu kayyaki da aka kawo mata.Haneefa ta juya kalli Mariya ta ce."Ki gama muje gaishesa sai mu wuce."Miƙewa Mariya ta yi don ta kammala kenan, ta ɗauki handbag ɗinta tabar gurin...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “GOBE DA NISA” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play