๐‘ซ๐‘จ๐‘ต๐‘ฎ๐‘ฐ๐‘ต ๐‘ผ๐‘ฉ๐‘จ๐‘ต๐‘จFree

ArewaPen original

Short StoryFreeOngoing

๐‘ซ๐‘จ๐‘ต๐‘ฎ๐‘ฐ๐‘ต ๐‘ผ๐‘ฉ๐‘จ๐‘ต๐‘จ

  • 1views
  • 3chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

Sample ยท ๐‘ฌ๐’‘๐’Š๐’”๐’๐’…๐’† 1&2

*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*         Page           1 and 2Haisam shine kad'ai d'a a gun Mahaifiyar sa Wacce ta kasance talaka, Mahaifin sa ya rasu tun Haisam na 'dan shekara biyu a duniya.Mahaifin sa mai kud'i ne sosai shiyasa wasu daga cikin yan uwan sa suke bakin Ciki. Duk da ya kasance Mai taimakon mutane sosai ga duk Wanda yake neman taimako daga gareshi, hakan bai Hana Yan uwansa Shirin kashe shi ba sabida su mallaki dukiyar sa.Da sun so shi sabida shine kad'ai Wanda Allah Albarka ce shi da d'a na miji. A Haka, wani daga cikin su ya sa mishi guba a abinci.Mahaifin Haisam yayi duk abinda yaga zai iya don ya ceci ransa daga guban Amma ya Riga ya Masa illa a jikin sa.Bayan rashin lafiya na watanni biyu sai ya rasu, Amma Kan ya rasu ya bawa matar sa wasiya akan ta tabbar ta ilmantar da Haisam Boko da addini komin tsadan sa.Bayan wata d'aya da rasuwar sa, wannan d'an uwan sa da yasa Masa guba yazo ya kwace dukkanin dukiyar, ya bar su ba ko sisin da za su rike.Rayuwa duk ta lalace wa Haisam da mahaifiyar sa, da kyar suke samun abinda zasu sa a cikin su, Amma duk da wahalan da suke Sha Bai Hana ta sa shi a makaranta Mai kyau ba, sabida shine wasiyar Mahaifin sa.Haisam yaro ne Mai kokari a makaranta, ya kasance shine yake zuwa na d'aya a cikin shekaru uku da yayi a junior secondary School, tunda da ga Nan ya kafa record. Ya cigaba da kokarin da ya Saba har ya Shiga senior secondary School. A yanzu Yana aji SS3 babban matsalar sa shine inda zai sami kud'in registration na W. A. E. C.MAKARANTAA ko da yaushe Haisam na Zama shi kadai, baya kula kowa harkan gaban sa kawaii yake yi sannan bashi da abokai, Duk da ya kasance Yan ajinsu sukan Zo gun sa don ya ganar dasu darasussukan da ya shige musu duhu ko basu gane ba, Yana da kirki sosai ga ilimi sannnan a shirye yake da ya ga ya taimaka musu, wata Rana a aji, darasin English ake musu, Haisam na zaune kusa da Ma'isha wacce ta kasance sabuwar zuwa ce a makarantar tasu, Ma'isha yarinyar kirkice daga gidan masu kudi, Bai dad'e da aka zabi Mahaifin ta a matsayin chariman na karamar hukumar su ba. A Lokacin da ake darasi malamar su Tace "Who can define phrase?" Duk Wanda suka amsa ba dai dai ba aka sa su kneel down. Haisam ya San amsan Kuma ya lura da Ma'isha na tsoro sabida bata San amsar ba, yayi saurin rubuta amsar a paper ya Mika mata. Nan take Ma'isha ta karb'a, malamar ta juyo gareta Tace "Ma'isha Mus'ab Aminu, answer the question, what is a phrase?" Ma'isha mikewa tayi ta tsotsa keyan ta wasu daga cikin Yan ajin suka shiga yi mata dariya a ganin su baza ta iya bada amsar Amsar ba "A phrase is a group of words that does not contain a finite verb and cannot stand alone to make a ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters3
premium0
01

๐‘ฌ๐’‘๐’Š๐’”๐’๐’…๐’† 1&2

Free sample
Updated 4 months agoAvailable now
02

๐‘ฌ๐’‘๐’Š๐’”๐’๐’…๐’† 3&4

Free sample
Updated 4 months agoAvailable now
03

๐‘ฌ๐’‘๐’Š๐’”๐’๐’…๐’† 5&6

Free sample
Updated 10 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play