FARATAN ZAKIFree

ArewaPen original

AdventureFreeOngoing

FARATAN ZAKI

  • 1views
  • 21chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1

FARATAN ZAKILittafi na daya 1 completena Shuraihu Usman© Shuraih 99% - 2020Chapter 1Na hada chapters guda hudu a wuri guda ku karanta domin kuwa insha Allahu gobe zan cigaba muku da wannan kasaitaccen labarin dana fara kawo muku kwanaki..Saurayine kyakkyawa tafe bisa kan ingarman doki, yana shara masifaffen gudu tamkar zai kure duniya, wannan saurayin ya wanzu yana keta dazuzzuka, kwazazzabai gami da koramu.matashin saurayin mai suna Muzaffar yaci alwashin koda zai gamu da ajalinsa bisa ga batun mutane akan wurin daya nufa sai ya isa wannan wuri ya isar da bukatansa, shi dai muzaffar ya fito ne daga wata alkarya mai suna DUMBAZUR SAHIR, cikin birnin MARHABUR SIHIR,birnin marhabur sihir birni ne da aka sana'anta shi da alkaluman tsafi hadi da sihiri, Birnin na karkashin wani azzalumin sarki ne mai suna basdur, duk da mutanen birnin marhabur sihir suna rayuwa cikin kunci gamida takurar rayuwa da suke fuskanta daga sarki Basdur, hakan bai sanya sun canja birni ba, domin kuwa gaba dayan biranen dake Alkaryan dumbazur sahir suma suna fuskantar kwatankwacin wannan ukuba da mutanen birnin marhabur sihir ke fuskanta.Muzaffar ya cigaba da keta dazuzzuka yana tsala masifaffen gudu bisa kan dokinsa, babu abunda ke tsaida shi dare ko rana, komai duhuwar dare baya tsagaitawa da tafiya, burin muzaffar guda daya ne a duniya shine ya isa KOGON SARKIN ZAKUNA ya ciro FARATAN SARKIN ZAKUNA dun yiwa babban abokinsa kuma amininsa maganin cutar data kama shi.lallai muzaffar yaci alwashi gamida alkawari bazai koma birnin Marhabur sihir ba batare da FARATAN ZAKI ba koda kuwa zai riski ajalinsa.wata rana cikin ranaku muzaffar na tsala azababben gudu cikin daji kamar kullum, kwatsam babu zato babu tsammani sai dokin nasa yaja ya turje yaki gaba yaki baya, muzaffar ya zaburi dokin don yayi gaba amma dokin ya ki, maimakon ma dokin yayi gaba sai ya fara rimi yana kokarin kayar da muzaffar dake bayansa, cikin sauri muzaffar ya daka tsalle ya dirgo kasa, sannan ya fara karema hanyar kallo, ko shakka baya yi wani abun cutarwa dokin nasa ya hango masa, cikin yadda dakai ya zare takobinsa ya nufi hanyar.ai yana kara gaba kunnuwansa suka fara dauko masa wani irin sauti mara dadin sauraro sautin yafi kama da a kirashi da sautin gurnanin wata mugunyar dabba, ai babu zato babu tsammani wani jibgegen mutum ya dirgo daga saman wata jibgegiyar bishiya dake kusa da muzaffar da niyyar ya dirgo a saman kan muzaffar, hucin zuwan mutumin ne ya sanya muzaffar saurin kallon saman kansa inda yai arba da katon yana kusantoshi, cikin azama ya kauce katon ya fado bisa kan kasa, muzaffar ya juyo ya dubi katon takobinsa a zare, katon da babu komai a hannunsa ya cigaba da gurnani yana kallon muzaffar yana dalalar da yawu daga bakinsa.bayan dakiku biyu sai katon nan yayi kukan kura ya fada...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters21
premium11
11

Chapter 11

Premium
Updated 9 months agoAvailable now
12

Chapter 12

Premium
Updated 9 months agoAvailable now
13

Chapter 13

Premium
Updated 9 months agoAvailable now
14

Chapter 14

Premium
Updated 9 months agoAvailable now
15

Chapter 15

Premium
Updated 9 months agoAvailable now
16

Chapter 16

Premium
Updated 9 months agoAvailable now
17

Chapter 17

Premium
Updated 9 months agoAvailable now
18

Chapter 18

Premium
Updated 9 months agoAvailable now
19

Book 5 chapter 19

Premium
Updated 9 months agoAvailable now
20

Book 6 Chapter 20

Premium
Updated 9 months agoAvailable now
21

Book 6 Chapter 21

Premium
Updated 9 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play