FreeArewaPen original
RAYUWAR MA'AURATA
- 1views
- 7chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1/2
[4/10, 00:09] Kyauta Daga Allah: 🌎 *RAYUWAR MA'AURATA*🌎Writings By IKILIMA ADAM and Maman NusaibaTsaraban Ramadan ne..Tsokaci bamu yarda wani Ko wata ya juya mana wannan labarin ba '' munyi shi ne akan masoyan mu.Dakuma jawo hankalun mata akan zamantakewar auren su..Idan kinga halin da yayi daidai da naki kiyi hakuri 'ki gyara halin ki, inkuma irin halin ne me kyau kika gani tokici gaba Allah yabaki lada...Babu cin Fuska Ko wulakanta wani a wannan novel din' munyi shi ne dan Allah..Allah kasa kamar yanda muka fara lafiya 'mukare lafiya.Takaitaccen labari ne dan nishadin ku masoya......Daga Marubuciyar *KANWATA* DA Marubuciyar *TANI DA MANU'*Muna muku Barka da babban bako Allah yasa mu fara azumi lafiya mukare lafiya yasa muna cikin yantattun bayi awannan watan....ALLAHU Ameen..0️⃣1️⃣ Sallamar da aketa kwada mata yasa cikin hanzari tafito' 'tabude gate... Tsaki ya buga cikin fad'a yace" Ke Wallahi Hauwa anyi sakarya Wallahi tun dazun sai buga Gida nake Saboda Allah jibi shinkafar n'an d'ana auno har ledan ta tadan soma fashewa...Hauwa cike da ban hak'uri tace" Yi hakuri Maigida dan Allah Wallahi banji bane ina cikin d'aki ne '' ina gyare-gyare kasan Ramadan ya gabato saida gyara...Tsaki yayi cike dajin haushin ta yace" Dan Allah Malama ki amshi shinkafar nan dakyau dan bakusan wahalar nema ba..Kudai à kawo kuci kuka sani jibi yanda rigana ya baci da kurar shinkafar nan....Hannu bibbiyu tasa takarba cike da nutsuwa ta koma cikin gidan...Take mata baya yayi shikadai sai fada yake zubawa...Koda ta ajiye shinkafar adan robarta hamdala tayi tace" Oh yaushe rabon in samu shinkafar aune kullum sainaje nasiyo..Cikin dan hanzari da kuzarinta '' tajuye shinkafar.....Jok dîn ta sabuwa data shiga adashi 'aka bata shine tayi maza tacika da ruwan randa'' kai masa ruwan tayi cikin kasa da murya tace" Abban Aliyu yau me ruwa be kawo ba gashi n'a randa yakusa karewa....Kambuhu ya furta cike da ruwan bala'i yace" Amma ke Hauwa Albazarranci yayi miki yawa 'ruwa ma saikin banzartar inace shekaran jiya aka kawo ruwan nan amma yau kin ce yakare, gayamin Aliyu da khadija ne suka shanye ruwan ne koko makota kike rabawa.Hauwa tagumi ta zuba tana kallon yanda yake shiga yana fita cikin cool voice din ta' tace" Yi hak'uri yau ankai sati ba'a kawo ruwan pampo ba n'a rijiya ake debo mana kuma kai bakashan n'a rijiya....Innalillahi Hauwa daman ke masharanciya ce bansaniba da rai da lafiya ta ake min karya.'ruwa ne Ko bazan bada kud'in ba, inma kinayi dan canji n'a naira hamsin dake hannun ki maza kije ki dauko mun marasa godiyar Allah.....Sake da baki take kallonshi tana Girgiza kai haka ta tashi jiki babu kwari taje tadauko masa naira hamsin d'insa.Tana isowa inda ta barshi tace" Abban Aliyu ga hamsin d'in taka.Wa...
App exclusive
Continue “RAYUWAR MA'AURATA” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.