FreeArewaPen original
RANAR BIRTHDAY
- 1views
- 4chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Broadcast Journalist/Writer/Blogger/Social Rights Activist
Sample · BABI NA 1
A shekarun baya can ba kasafai za ka ji ana maganar wani ko wata na shirya bukin zagayowar ranar haihuwa ba, musamman a nan ƙasar Hausa, saboda al'adu da yanayin fahimtar da aka yi wa koyarwar addini a lokacin. Ba wai babu masu shirya bukin zagayowar ranar haihuwa ba ne, amma ko da akwai ba su da yawa, kuma ana yi musu kallon 'yan boko ne masu iƙirarin wayewa, ko kuma ma dai ba Musulmai ba ne.Amma a hankali a hankali wannan al'ada ta shirya bukin zagayowar ranar haihuwa da aka fi sani da Birthday Party tana ƙara samun karɓuwa a tsakanin Hausawa Musulmi, maza da mata, musamman 'yan mata da jaruman shirya finafinai, mawaƙa da wasu fitattun mutane ko masu ganin gabansu da kyau, wato masu hannu da shuni!Rukayya Mohammed da ake yi wa laƙabi da Rukky na ɗaya daga cikin rukunin waɗannan mutane, kasancewar ta marubuciya kuma 'yar makaranta, wacce ke da ilimi da wayewa daidai gwargwado a ɓangaren addini da boko. Ƙawayen ta na unguwa da wasu 'yan makarantar su Musulmi suna kiranta da Ustaziyya, saboda yadda take da kamun kai, natsuwa da son addini. Duk da kasancewarta budurwa matashiya, hakan bai hana ta suturce jikinta da kaya na mutunci, wanda ke ɓoye surar jikinta da ƙara mata kwarjini a idon mutane ba. Idan ba wanda ya santa ba, duk wanda ya ganta a waje tana tafiya zai yi mata zaton ko matar aure ce, saboda yadda take rufe fuskarta da wani bakin kyalle da aka fi sani da Niqab, wato ƙyallen da ake ɗaura shi a kan hijabin da aka sa domin ya ƙara suturce fuskar mace, sai dai ƙwayar idanunta kawai za a gani.Idan tana tafiya, takun ta gwanin ban sha'awa, cikin natsuwa da wani yanayi na rausaya ba tare da ya ja hankalin maza da ke waje ba. Amma duk da haka idan har mutum bai kai zuciyarsa nesa ba, da ƙyar ya kiyaye da kallo ɗayan da Sunnah ta amince ya yi wa macen da ba muharramar sa ba. Kai, ko da mace ce 'yar uwarta sai ta waiga ta sake kallonta.Sau da yawa za ka ji mata na gulmar yadda take tafiya, kamar mai tausayin kasa ko kuma a rika ce mata Rukayya Yanga, duk kuwa da cewar ita har ga Allah a zuciyarta ba da niyyar yanga take yi ba. Haka dai tafiyar ta take, tun ma tana ƙarama. Abin da wasu da suka yi mata farin sani ke ganin yana da nasaba da gado, saboda an ce kakarta ta wajen uba, Hajiya Zuwaira wata kyakkyawar bafulatana ta yi tashen kyau kuma ta yi wasa da zuciyar maza. Sakamakon yadda aka ce take tafiya da rangwaɗa da nuna isa da ƙasaita na cikar 'ya mace.Ko da yake ita Ruƙayya ba ta biyo ta a cikar kyawun da ake kururutawa ba, amma fa ita ma ba baya ba ce. Tana da kyan diri da sura mai ɗaukar hankalin duk wani ɗa namiji da tsautsayi ya sa ya ƙyallara ido ya ganta lokacin da ba ta sanye da burmemen hijabin da ta saba sanyawa, wato idan tana cikin gida kenan. Don hatta 'yan uwanta mata suna yaba kyan halittar ta, duk da yake ba jin daɗin hakan t...
App exclusive
Continue “RANAR BIRTHDAY” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.