ASP ZARAHFree

ArewaPen original

RandomFreeOngoing

ASP ZARAH

  • 1views
  • 6chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

Sample · Ɗanɗano 1

ASP ZARAHHaƙƙin mallakin_ Asmau Bint Abubakar (Jasmine 🌸🌸)Da sunan Allah Mai Rahma Mai Jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin Sarki daya babni lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci da na samu daman rubuta wannan littafin. Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta Annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.Jan Hankali: Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya.BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIMƊanɗano..."Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Shine abinda matashiyar yarinya wacce ke sanye da kayan ƴan sanda take maimaitawa, alamu sun nuna cewa suma tayi aka watsa mata ruwa ta farfaɗo duba da yadda take a kwance a ƙasa idanu a rufe ga fuskarta data jiƙe da ruwan da aka watsa mata. Jin ana ƙoƙarin ɗagata a ƙasan ne yasata buɗe ido domin ganin mai taɓatan, Ammi ce wacce take matsayin ƙanwa ga mahaifinta. Kallon fuskar Ammin tayi wacce ta kumbura tayi jazir saboda kukan da tasha domin hatta idanunta sun koma can ciki ba'a ganinsu sosai saboda kumburin da fatar idon nata tayi. "Zarah kuka ba shine mafita ba a yanzu, kizo kiyi sallama dasu domin a samu damar kaisu makwancinsu da wuri." Ammin ta faɗa cikin dasasshiyar muryarta. Buɗe baki tayi domin magana amma kukan data kasayi tun farko ya riga maganartata fitowa, take kuwa ta fara rera kukan mai taɓa zuciyar duk wani mai sauraro. Hannunta Ammi ta kama ta ɗagota tare da nufar inda gawarwakin mutane takwas dake sanye da suturarsu ta ƙarshe a cikin makara, koda ta iso da ita wajen sake hannunta tayi tare dayin baya domin kukane yakeson ƙara kece mata. Cikin rawar hannu ta fara yaye mayafen daya lulluɓewa gawarwakin fuska tundaga kan gawa ta farko. "Mahaifina, Mahaifiyata, Kakannina uku, ƴan biyun ƙannena sannan ƙaramar ƙanwata. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." ta ƙara fashewa da wani sabon kukan mai taɓa zuciya, lokaci ɗaya kuma ta tsagaita tare da gyara rufuwar mayafan sannan ta ɗaga hannu sama ta fara addu'a. "Ya rabbi, Ya rabbi, Ya rabbi. Ya Hayyu ya Qayyum ya Allah ina gode maka a cikin kowani yanayi dana tsinci kaina. Ya Allah kaine shaidata ban shiga aikin ƴan sanda ba saidan na taimaka gurin gyara ƙasata, Ya Allah kasani ina tsare duk wasu dokokinka bana saɓawa da gangan saidai a rashin sani. Ya ubangijina nasan ka fini son waɗannan bayi naka shiyasa ka karɓesu daga aron daka bamu, na karɓi wannan jarabawa hannu biyu sannan ina ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters6
premium3
04

Wasa Farin Girki

Premium
Updated a year agoAvailable now
05

Tasku

Premium
Updated a year agoAvailable now
06

Komai Fararre Kararre

Premium
Updated a year agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play