DAREN AURENAFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

DAREN AURENA

  • 1views
  • 2chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Allah first☝ Prophet muhammad (s.a.w)💔 Proudly muslima❤ Daddy's queen👑 Mommah's princess💓 Writing novels is my hobby❤💙 Author queen❤ C.e.o royal star writers association✍🏽

More from @shaabandaughter01

Sample · Chapter 1

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸     *😢DAREN AURENA💔*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸*Daga alk'alamin 'yar mutanan zazzau Naanah M Sha'aban💖*_Labari mai tab'a zuciya😭__Wannan littafin sadaukarwa ne ga k'ungiyata da kuma jaruman cikinta💖_*Wannan labarin k'irk'irarran labari ne ban yarda a juya min littafi na ta kowacce hanya ba😇*Shafi na 1.............📖Kuka take tamkar ranta zai fita kwance take a kan d'an k'aramin gadon d'akin ta duk'unkune a cikin bargo ta rintse idonta zuciyarta nayi mata wani irin zafi da k'una cikin da sasshiyar muryarta ta fara magana "tabbas nayi dana sanin, sanin Jabir a rayuwata, ka cuceni, ka yaudareni bazan tab'a yafe maka ba har duniya ta nad'e, Insha...insha Allahu, Allah sai ya saka min abin da kayi min Kuma....." Sai Kuma ta kasa k'arasawa saboda irin kukan da ya shak'eta.Aunty Murja ce ta shigo d'akin da sallama d'auke a bakinta zuciyarta cike take da tausayin k'anwarta ta saboda Jabir yabar mata mugun tab'o Wanda bazan tab'a gogewa a cikin zuciyarta da ma rayuwarta gaba d'aya, yayi mata abinda ba za ta tab'a mantawa ba a daren aurensu.Zuwa tayi kusa da ita ta zauna tare da jawota jikinta suka k'ank'ame juna suna kuka, sun d'auki kusan mintuna biyar suna kukan Aunty Murja ta had'iye nata kukan domin ta samu ta rarrashi k'anwarta ta, Cikin muryar rarrashi ta fara magana "Khadijatullah nasan akwai zafi sosai a cikin zuciyarki, abin da Jabir yayi miki sai dai muce Allah ya saka miki domin kinsan mu ba wani arzik'i ne damu ba, barantana muce zamu kai shii k'ara kotu abi miki hakk'inki, Kuma ko min kai Jabir k'ara a zamanin nan na yanzu babu abinda za'ayi Masa saboda Yana da kud'i, Dan Allah Khadijatullah kiyi hakuri kinsan yawan kukan nan zai iya haifar miki da wata matsalar Ina tsoron kar in rasa ki kamar yadda muka rasa iyayanmu ke kad'ai nake kallo nake jin dad'i a cikin zuciyata" ta k'arasa maganar hawaye na zuba daga cikin idanuwanta.Khadijatullah ta d'auki kusan mintuna goma tana kok'arin tayi magana Amman kukan da take ya hanata tayi dakyar ta samu ta sassaita kanta ta fara magana cikin sark'ewar muryar "Aunty Murja nasan bakya son kina ganina a cikin irin wannan yanayin, Amman Aunty Murja Ina ga ba zan tab'a daina kuka ba, zuciyata ba zata tab'a daina min zafi ba, saboda yanzu mun d'aura k'awance da tashin hankali, Aunty Murja wallahi ina ga bak'in cikin Jabir ne zai kasheni" wani sabon kukan ne ya kwace Mata Aunty Murja ta k'ara rumgumeta sosai a jikinta, Khadijatullah ta d'auki kusan mintuna biyar tana kukan kafin ta cigaba da magana "Aunty Murja wallahi na tsani Aure kuma na tsani maza, wallahi da za'a bani dama da sai na kashe duk wani namijin da yake duniyar nan tabbas na yarda da maganar hausawa da suke cewa namiji ba d'an goyo bane duk yadda ka Kai ga goya shi wata rana sai yayi maka abin da ba kayi ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters2
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play