FreeArewaPen original
RAYUWAR MACE
- 1views
- 45chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Page 1
*RAYUWAR MACE* _Hafsat Rano_ Free Page (1)******* Sanye take da hijabi ruwan toka dogo har kafarta, kanta a k'asa sanda zata wuce ta daidai majalisar mazan wadda kullum sai ta bi ta wajen idan zata je islamiyya tana kuma jin yadda suke maganar ta a kullum idan tazo wucewa, tun abin na damun ta har ta iiik ya dake makale a kafadarta ta jingine ta a wajen ta nufi dakin nasa kirjin ta n I'm aw dukan uku-uku. Shi kadai ne a dakin daga gani ya gama shiryawa fita zai kasuwa, tun bayan da manyan yayanta maza suka taso sai ya zama ba kasafai Abban yake fita ba sai ya dau kwanaki yana gida yana hutawa. "Sannu da hutawa Abba.". Tace tana neman waje ta rabe dan ta riga ta san kwanan zancen, ya kwana biyu be mata maganar ba shiyasa ta dan samu nutsuwa a kwanakin"Yawwa Asma'u, an dawo!?""Eh Abba.""Toh Madallah, sannu da dawowa.""Yawwa." Ta amsa a ciki tana sake lankwasa kafarta"Kina jina ko,akwai wani da yazo ko kuwa har yanzu dai?""Babu kowa Abba." Tace a sanyaye dan tuni har yar karamar kwalla ta soma taruwa a idon ta. Shiru Abban yayi be tanka ba, tamkar me tunanin abinda zai ce, bayan wasu yan dakiku ya kalle ta sannan yace"Ko dai kina korar su ne Ma'u?"Da sauri ta girgiza kai hawayen da take kokarin rikewa suka sakko. Kura mata ido yayi sosai sannan ya soma magana a nutse cikin son kwantar mata da hankali Kanta a kasa tana jin Abban har ya kai karshe, cikin nutsuwa tayi masa godiya sannan ta mike ta baro dakin zuciyar ta na sake tsinkewa. Idan tace bata damuwa da rashin aure tayi karya. Tafi kowa son ganin tayi auren kamar yadda yake burin duk wasu iyaye da zarar yar su ta kai munzalin aure! Tabbas tasan duk wasu iyaye da yar su ke gaban su basu da kwanciyar hankali har sai sun ga sun aurar da ita gudun magana da abinda ka iya zuwa ya dawo. Amma kuma abu guda da mutane suka kasa ganewa shine, aure, haihuwa da mutuwa duk lokaci ne mutum be isa ya bawa kansa ba idan ba har lokacin ne yayi ba. Da yan yatsun hannun ta, take kokarin kirga adadin kannenta da akayi wa aure kamar yadda ta saba a kowanne lokaci, ta riga ta san adadin su sai dai kirgawar na sake tabbatar mata da dole ne mahaifin ta ya dinga tunasar da ita a kowanne lokaci. Duk da shekarun ta ba wai sun ja sosai bane dududu a yanzu ne ta cika shekara ashirin da biyar sai dai yanayin yadda ake musu aure da kananun shekaru ya saka ake ganin ta tsofe a gida. Kannenta biyu da akayi wa aure karshe ,shekarar su sha bakwai dan haka idan zaa hada su da me shekara ashirin da biyar toh fa tabbas dole a dinga yi mata kallon taki aure. Bata san kalar matsalar ta ba, dan ba zata iya tuna lokacin da wani ya tare ta ko a hanya bane. Ta kan zauna tayi ta tunanin ko dai ba za...
App exclusive
Continue “RAYUWAR MACE” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.