FreeArewaPen original
DABI'AR ZUCIYA
- 1views
- 37chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Am a writer,i dream while awake.
Sample · Shafi na biyu
Duk wannan aikin da yake baisan tari ko adani ba,burinsa daya samu kudin ya siya abu mai dadi yaci,ya kuma kawowa mahaifiyarsa a boye,baya taba bari mahaifinsa ya gani,don yana da tabbacin indai ya gani ba rabonsa bane kudi ko abinci,koda na nawa ne kuwa,zai karba ya kalmashe a aljihunsa,rashin kawo musu baisa yaji kunya yaqi amsar nasu idan sun samu. Sosai abun ke cima kaltum tuwo a qwarya,tana qaunar bilal sosai,yana da sauqin kai,bashi da rashin ji ko hayaniya irin ta yara,wahalar da yakeyi tana ganin tayi yawa,saidai kusan ta zame masa jiki ma,ya zama tamkar bawa,don baya iya zama wuni guda a gida ba tare da yayi aikin komai ba,saidai idan bashi da lafiya. Shi dinma da kaltum taso yayi karatu koda su din basuyi ba,tunda shine da namiji guda daya tilo da mahaifiyarsu keda shi,amma sam yaqi,ya nuna aikin neman kudinsa ya fiye masa,kod...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.