KINYI BAJINTAFree

ArewaPen original

ThrillersFreeOngoing

KINYI BAJINTA

  • 1views
  • 21chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

Sample · CHAPTER 1 YAR KWALISA

KIN YI BAJINTANa'ima, matashiyar mace ce 'yar shekara ashirin da biyar, gogaggiyar 'yar boko ce, a wasu lokutan, tana sirka hausarta da turanci, kuma tana da ilmin addini daidai gwargwado. Ta mallaki matsakaicin kyau da tsawo. Duk da yake 'yar zamani ce ita, wayewar kanta bai gurɓata mata tarbiya ba, ma'abociyar son girke girke ne, musamman na zamani, haka kuma ta iya ko wane irin girkin gargajiya. Malama ce a makarantar gaba da primary inda take koyar da food and nutrition.  Yanzu haka Zaune take a gaban mahaifiyarta tana shirga kuka, kamar wance aka naɗa wa kafirin duka, duk tayi wujiga-wujiga. Mahaifiyarta Hajiya Hauwa ta daka mata tsawa, "Shin dukanki na yi? Ko kuwa faɗan ne ba ki so ayi maki?"Na'ima ta gintse kukan haɗi da fara magana cikin shassheka, "To Hajiya, Mutumin nan fa, he doesn't love me at all, amma ku ka matsa sai da aka ɗaura auren nan, ga shi yau wata biyu kenan bai zo ba, apart from that, an faɗa  mini aurensa biyu, matan suna mutuwa, kuma duk shi ne sila. Honestly speaking, ba na sonsa Hajiya, gara a..."Hajiya Hauwa ta katse mata hanzar,"Waye ya faɗa maki shi ne silar mutuwar matansa? Wannan duk ƙaryar jama'a ne 'yan gaza gani, ni dai na san matarsa ɗaya ce ta rasu, to wai ma ba a mutuwa mahaifinki ya rasu? Ashe sai ace ni ce silar mutuwarsa. lta kuwa ɗaya matar ta sa fita tayi.Na'ima na san ke gwana ce a fannin girki, shi fa kika karanta, kuma fannin girke-girke ki ke koyarwa a makaranta, shi yasa na ke so ki kwantar da hankalinki waje guda, ki zage damtse a gidan mijinki, ki dunga yi masa girke-girke masu ƙayatarwa, kuma na samu labari a wurin mahaifiyarsa, shi Mannir mutum ne mai son abincin gargajiya, bai faye son cimar turawa ba kuma ya tsani cin abinci a waje, don Allah idan bar na isa dake, to ki yi min biyayya, ki zauna lafiya da mijinki, ki dubi irin yadda yaransa ke sonki da zumuɗi a kanki. Kwata-kwata shekarunsa bakwai. Amma sun san su kiraki a waya su gaidake, kullum suna ɗoki da zumuɗin zuwanki gidansu."Na'ima ta share fuska, "Hajiya, if he really loves me, me yasa baya zuwa wajena? Me yasa baya kirana a waya, sai dai yaransa su kirani? Ni na san ba sona yake ba, ku ka ɗaura mini aure da shi."Ta sake ɓarkewa da wani sabon kukan. Hajiya Hauwa ta dafa ta, ji ta yi kamar a fasa auren, don ta daɗe da sanin halin Mamnir na miskilanci da rashin Son aure, to amma kuma tana da yaƙini idan har sun zauna gidan ɗaya, to za a wayi gari wata rana diyarta zata ɗaga tuta a wajensa.Shi yasa take ji Sam! Ba za ta iya warware wannan aure ba, saboda nauyin mahaifiyarsa, tana ganin ƙimarta da girmanta, tunda har ta karya 'yancinta ta zo har gida akan matsalar. Hajiya Hauwa, ta ci gaba da lallashin ɗiyarta, "Ki yi haƙuri da maganar rashin kiranki a waya da baya yi, mahaifiyarsa ta sh...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “KINYI BAJINTA” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play